Sashe 33
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read
Dai dai lokacin ƙayataccen ƙamshinsa ya turnuke falon wanda ashi ya basu tabbacin cewa yana kusa, zubawa kofar shigowar ido aminatu ta yi tana jin wani irin sanyi da bugun zuciya wanda take kasancewa a cikinsa duk lokacin da yake kusa da inda take, ba tare da ta gama daidaita kanta ba ta tsinkayi dakakkiyar muryarsa yana sallama, bai shigo falon ba har sai da nana da Abby suka amsa masa, kana ya ƙaraso cikin falon a kamensa fuskar nan babu yabo babu fallasa, ya so wucewa upstairs bayan sun gaisa to amma sai Abby ya dakatar dashi da bashi umarnin zama,zaman yayi yana kallon aminatu ta kasa kasa yanda ko ita ba dan tana jin kallon har cikin ƙashinta ba to da bazata taba sanin yana kallonnata ba, Abby ya ce",gobe in Allah ya kaimu isma zai dawo ina tunanin ma yasanar da kai ko?"jinjina kai kawai mus ab yayi idanunsa a lumshe kansa a jikin bayan kujerar da yake kai,Abby bai damu da shurun nasa ba ya ci gaba da cewa sai abu na gaba zamu yi magana dakai kafin ka fita da safe maganar tana da muhimmanci kar ka fita bam tare da kazo mun yi ba", nan ma gyada kansa ya yi ba tare da ya motsa ba, Abby dinne ya fara miƙewa ya wuce zuwa bangarensa.
Khalid ne ya matsa jikin mus ab din Yana masa surutun school,aminatu kuwa tana zaune tana tura baki ta yi funfurus ta ƙi koda kallonsa ne bare a kai ga batun gaisuwa,juyawa Nana ta yi tana duban aminatun kafin ta ce."aminatu yaushe kika koyi ƙin gaida mutane ne ban sani ba?"ƙifi_ƙifi ta yi da idanunta tana kalmashe ƙaramin bakinta ta hanyar maidashi gefe kafin cikin sakalci ta ce." to nana ya za ayi na dinga asarar gaisuwata inda ba amsawa za a yi ba",to boddo da ki ƙi yin gaisuwar ai gara ki yi a ƙi amsawa", tura bakin ta tayi ba tare da ta ce komai ba kuma ta ƙi duban inda yake bare ta yi abinda Nana ke son ta yin,gashi har yanzu tana jin kaifin idanunsa a jikinta,a hankali ya zame khalid da tuni ya fara bacci ajikinsa ya kwantar dashi,kana ya miƙe yana dubanta ƙasa_ƙasa daga bisani kuma ya buɗe baki kamar ana masa dole cikin tsintsinka kalmomin ya ce "nana I need coffee",daga haka ya wuce cikin takunsa na cikakkun mazan da suka amsa sunansu maza,Nana ta ce "yanzu zan TURO aminatu ta kawo maka", da sauri aminatu ta zaro idanunta da suke wani irin maiƙo ba tare da ta ce ko mai ba ta ɗan bisa da hararar ƙasan ido kafin cikin ƙunkuni ta ce,"dama so yake a ce na kai masa ya kamani ya tsotse min ruwan jiki mutum ba abinda ya iya sai iskanc......kallon da ya watsa mata bayan ya taka step biyu ne yasa ta datse maganarta ba tare da ta ƙarasa ba kuma ta ankara da cewa a fili ta yi maganar,muryar nana ta ji tana cewa "Allah ya shiryamin ke boɗɗo",ba kunya kuma ta amsa da amin tana ci gaba da mitarta a ranta.
Har nana zata shiga kiching ɗin sai kuma ta dawo da baya tare da ya fito aminatu, tashi ta yi ta bi Nana kiching ɗin tana shiga ta sameta a tsaye gaban Caved din kiching ɗin, ƙarsowar Aminatun yasa nana bata waje tana cewa "maza haɗa ki kai masa"ta buɗe baki zata yi magana nana ta watsa mata hararar da yasa ba shiri ta ja bakinta ta tsuke,tana kallo nana ta bar kiching ɗin wanda hakan ke nuni da cewa lallaifa sai ta haɗa coffee ta kai masa, hada coffee ɗin tayi yadda ta gadama, ta zabga masa uban shuga da zuma bayan kuma tasan baya son zaki da yawa,tana gamawa ta fita tana dariyar mugunta tasan ko hanashi sha ta yi zata ji daɗi.
Da murmushi a fuskarta ta fara taka step ɗin ba tare da ta kalli me yake gabanta ba,karon da suka yi da zahida da ke ƙoƙarin saukowa yasa ta farga, wanda kuma kafin ta fargan har coffeen ya watse a jikin zahida, take zafinsa ya ratsa fata zuwa ƙashin zahidar wanda hakan yasa ta yi wata irin fusata tare da dagewa iya karfinta ta hankaɗa Aminatu baya,ƙara aminatu ta ƙwalla wanda hakan yayi sanadin fitowar gaba daya mutanen gidan dai-dai aminatu na gangarowa tun daga kan step na bakwai da suka ci karo da zahida har zuwa na ƙarshe wanda a take a gun hannunta ya yi wata yar bazawarar ƙarar da bayyana cewa ta karye ko ta samu gocewar ƙashi, da sauri innawuro da Nana suka yi kanta cikin ruɗewa da tashin hankali suke ƙoƙarin kamota amma ina aminatu azaba tuni tasa ta suma,mus ab kuwa ture su yayi ya dagota jikinsa yana dan marin fuskarta cikin yanayin dakiyarsa da ba kowa yake gane yanayin da yake ciki ba.
"Larai maza kawo ruwa a zuba mata",cewar Abby ke nan da yake kallon zahida cike da tuhuma,da sauri larai ta cika umarnin da aka bata,nana ce ta karɓi ruwan ta buɗe tare da zubawa mus ab a hannunsa da ya miƙa mata, a hankali ya shafawa aminatun a fuska yana kuma dan marin fuskarta a nutse, da azabar kuka ta buɗe idanunta tana mai kasa motsa hannunta ,"wayyo Nana ta karya ni wallahi ta karya ni muguwa azzaluma kalan tasa dan birni ya ce ba zai zauna da nakasasshiya ba, wallahi idan ya ce baya sona sai dai ki hakura da na ki ɗan birnin ki barmin zalumu kawai me zuwa wajen boka mashrikiya",duk abinda ake zahida na tsaye babu wani alamu da zai nuna maka cewa ta ji ciwon abinda ta aikata, a ranta ma fata ta yi aminatun ta samu gagarumar matsala ta yadda bazata kuma moruwa ba,Nana ta ce,"zahida me ya haɗa ki da aminatu kike neman kasheta?Aminatu fa har yanzu da kuruciya a tare da ita ko ma me ta yi miki bai kamata ki nemi makasarta ba",kuka zahida ta fashe da shi tana cewa amma ni baki duba cewa ta nemi kashe nin ba ruwan zafi ta fasasshe fa ta kwara min tana sane", aminatu da mus ab ya ke ƙoƙarin ɗagata cikin kuka ta bude baki duk da azabar da take ji ta ce."wallahi nana ƙarya take yi karo mu kayi shine ta tunkuɗe ni", Abby ya katse muhawarar da cewa"mus ab me ka tsaya yi maza ku tafi asibiti mana", da sauri aminatu ta kalli mus ab ta ce wane asibitin za a mu?"anne da haushi ya isheta ta ce to wane asibitin kika san muna dashi a gidan nan banda wanda kika ƙi jini na me gidan da yayi muku alfarmar zama a karkashin inuwarsa, in banda butulci da Rasha na hankali ma ya za ayi yarinya ta dinga juya mutane duk sanda za a kaita asibiti sai ta zaba wanda take so yarinya sai kace ta shanue ku",kiciniyar sauka daga jikin mus'ab aminatu ta fara yi tana cewa "wallahi ba zani asibitin nan ba in dai shi za a kaini to a barni na mutu",gaba daya zuba mata ido su kayi baran ma zahida da Abby da suke cike da zargin aminatu akan sanin wani abu na sirrin asibitinsu wanda suke tunanin shine makasudin tsanar asibitin da ta yi,a take dukkansu suka sha alwashin bincikar aminatun ta ko wane hali dan tabbatar da zargin su ko akasin hakan.
"Mus ab kuje Ka kaita ABM tun kafin hannun ya kumbura dan da alama dai gocewar ƙashi ta yi",cewar nana tana mai kawar da tunanin da suka tsunduma da kuma banbamin da Anne take ta faman yi akan sun sangarta aminatun bayan kuma babu dangin iya babu na baba,zahida ta yi caraf ta ce,"haba nana ya ga asibitin gida amma za a kaita na duniya bayan asibitin da ta raina shine best asibiti da muke da shi a jihar nan", aminatu da take kwance jikin mus ab tana faman raki ta kuma yin tsagal ta ce,"ina ruwanki da asibitin za a kaini naku ne dai ba zanje ba bare ku samu abinda kuke so me warin baki kawai",kut ni kike cewa me warin baki dan ubanki to in gaya miki tun kafin a haifi ubanki balbela take da farinta tsinanna sadakar yalla", suna gab da fita falon aminatu ta mayar mata da cewa hamma mus ab ashe tsohuwar guzuma ka aura bamu sani ba tunda a yadda take nuna mana ma ta haifeka",tun da ake fade faden bai ce ko mai ba sai yanzu da yayiwa aminati duban kai tdaye tare da cewa "idan baki rufe min baki ba zan sake ki anan ki ƙarasa dagargajewa",rufe bakinta ta yi tare da karyar da kanta akan kafaɗarsa tana cewa "zafi zafi wayyo zan mutu hannuna zai cire",Anne da ta bisu sa harara tana cewa, ai zafin ciwon bai hanaki yiwa mutane rashin kunya ba", zahida kuwa gaba ɗaya ji take kamar ta cire zuciyar aminatun tun yanzu kowa ya huta da bala'inta.
Nana ta dubi innawuro da gaba daya jikinta ya kuma gama yin sanyi saboda cin kashin da Anne da zagida suke musu wanda ita aminatu sam basa damunta,da fata nana tayi tare da cewa innawuro je ki kwanta ki huta aminatu zata kasance cikin kulawa in sha Allah", cikin gamsuwa innawuro ta jinjina mata kai tare da shigewa corridon da zai kaita zuwa dakinta.