← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 46

Sashe 30

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read

A yayin da waɗannan bayin Allah suke tsaye gaban Ubangijinsu suna raya daren da kyakkyawar dabi a, a daidai lokacinne kuma zahida take dakinta tana Safa da marwa, tunani iri da kala ta kasa samowa kanta mafitar rabuwa da ɗan ladi da kuma samun ƙaunar mus ab,a maimakon hakan ba sai damuwa da tashin hankali ne da suke nunnunkuwa a ranta duk ta tuna cewa ɗan ladi ya zamar mata maƙale mata kuma ƙarfan kafa,ƙarshe ma zama ta yi dirshen ta fasa kukan da bashi da magani ko nace bata san hanya me saukin da zata bi ta magance matsalarta ba.

Baccin awa daya suka kuma yi aka kira sallah,yanzun ma bai sha wahalar tashinta ba dan duk yanzu aminatun ta saba da wannan rayuwar.

Sai da gari ya ɗan yi haske kana ya shigo gidan kamar yadda ya saba,Nana ya samu a falo a tsaye da alama dai jiran wani abun take yi,ile kuwa hannunsa ta kama suka nufi ɓangarenta tana cewa "magana nake so mu yi da kai shi yasa na tsaya jiranka dan wannan lokacin shine ya dace da yin maganar sirri kuma me matukar Muhimmanci", bata tsaya iya falonta ba sai da suka dangana har uwar makeken lafiyayyan dakinta, zama ta yi tana nuna masa kujerar hutawa ta dakin dan ya zauna,a maimakon ya zauna sai ya zauna a kasa gaban ƙafafunta kana ya fara da gaisheta cikin wata irin biyayyar da ƙauna, itama amsawa ta yi cike da alfahari.

Kana ta ɗanyi gyaran murya kafin cikin taushin murya irin ta dattawan mutanen da suka san rayuwa ta ce," mus ba,me kake shiryawa a gaba? A halin yanzu dai ka sauke nauyin amanar da aka baka na abubuwa guda biyu masu muhimmanci,ka sauke wancan alkawarin da ka yi ya tabbata har gashi yana shirin haifar da abinda ake nema wato nasarar da al'amarin yake ta samu a daidai wannan lokaci,na biyu ka inganta rayuwar aminatu da ingantaccen ilmimmuka masu tarin yawa ta hanyoyi masu ban mamaki, acikin shekara biyun nan ka samarwa da aminatu ilimi wanda ita kanta idan aka ce ta faɗi iya abinda take karantawa bazata iya ba,ban taba ganin kwaƙwalwar da aka zubawa ilimin shekara bakwai acikin shekara biyu ba sai ƙwaƙwalwar aminatu tabbas wannan ba ƙaramin yaki ba ne kuma babbar nasara akan amana da alkawarin da ka ɗauka, su kansu malaman aminatu wanda suka koyar da ita cosess ɗin mamaki suke yi, dan dr helen cewa ta yi inama zaka iya bata aminatu ta koma da ita Istanbul da taji daɗi kuma kasarsu ta ci gaba", a nan ne ya dago rikitattun idanunsa ya kalli nana kafin ya ɗan fesar da numfashi kana ya ce,mu ce mata aka yi bama bukatar cigaban, batasan son ci gaban namu ne yasa ban tsallaka da aminatu can inda suke ba na daukosu gida?".jinjina kai Nana ta yi kana ta ci gaba da cewa.

Mus ab aminatu ta samu kyakkyawar rayuwar da kake buri domin a halin yanzu aminatu tasan rayuwa daidai irin wadda ka nuna min kana so aminatu ta kasance a cikinta,aminatu bata san mene girman kai ba,bata san raini ba bata san dizgi ba,abu daya ne ba zai canji a wajen aminatu ba shine gabunta na yar fari sai dai wasu abubun sun ragu tunda yanzu ta yi hankali,"duk da irin gidan da aminatu ta tsinci kanta a halin yanzu hakan baisa ta manta nasabarta ba, sam aminatu bata san meye rayuwar karya ba, duk da cewa ko mai mun wada tata dashi hatta suhaima kafin ta bar gidan nan sai da rayuwar aminatu ta canja ta, wannan halayyar ba mu muka koyar da aminatu ba da binta tazo duniya,kaf cikin anguwar nan babu da wnada aminagu take hulda sai talakawan cikinta har da na makwabtan anguwa, idan Khalid ya tambayeta me yasa bata yin kawaye masu kuɗi irin na mom ɗinsa takance masa,khalid ai nima talakace kuma dan duk ɗan halak baya manta mafari, sa misali ma nice Kai na tashi cikin daula rayuwar jin daɗi, bana hulda da masu ƙaramin ƙarfi, to dan Allah Khalid ta yaya zan yi na gane al'umma suna cikin wani hali ta yaya zan tausayawa na kasa dani? ta yaya idan Allah ya buɗa min zan taimaki talakawa,?khalid ba zan yi ba in dai har ban zauna dasu na san yaya rayuwarsu take ciki ba,Khalid idan kana so ka taimaki marashi to dole sai ka sauke girman kai ka manta da kai waye ka daidaita matsayinka da nasu ka shiga cikinsu kayi rayuwa matsakaiciya kuma ka yadda cewa da kai dasu duk ɗaya ne ta hanya ɗaya kuka zo duniya ta hanya daya kuma zaku koma ga Allah, kasa a ranka kuma ba dan Allah baya son su ba ne yasa suke shan wahalar rayuwa sai dan kawai ya gwada imaninsu yaga shin zasu yi hakuri su riƙe jarrabawarsu ba tare da sun faɗa wata mummunar hanya ba,kaima ba ya baka ba ne dan yafi sonka sai dan ya gwada imaninka ya ga ta ina zaka sarayar da arzikin da ya baka, dan haka kasa a ranka baka da wani arziki a duniya sai na kasancewarka musulmi wanda ya taso a tutar Muhammadur Rasulullah s.a.w).

Mus ab kaji fa wasu kalamai daga bakin ƴan baiwa wanda suke keɓabbu acikin al umma masu zuciyar zinare, wallahi mus ab Ni kaina na ƙaru ƙaruwa mafi girma a cikin rayuwata da su aminatu, na koyi abubuwa da yawa wanda tun kafin ƙwakwarwarta ta cika da ilmummuka na zamani da na addini na samesu,shi yasa na kiraka domin na shaida maka irin nasarar da muka samu a mataki na farko dana biyu na alkawari da amanar da aka bamu dan haka kai tsaye ka tafi kan mataki na gaba wanda yafi ko wanne hadari kuma me sauki idan an nemi taimakon Ubangiji,mus ab lokaci yayi da zaka fara bincike akan wadannan azzaluman mutane da suka kashe iyayen aminatu dan tabbas ina ji a jikina har yanzu suna nan a duniya suna ci gaba da yin ta adi da rashin imani dan irinsu basu cika mutuwa da wuri ba, Allah yana ara musu dama ko zasu yi hankali su koma gareshi, mus ab ka fara yakinka ni kuma zan ci gaba da taimaka maka da dukkan karfina da kuma na kasancewata uwa kuma musulma da zan iya yi maka addua a kan dukkan wani al'amari da naka", a hankali cike da samun kwarin gwiwa da wani irin alfahari ya bude baki zai yi magana,amma sai ta yi saurin taresa da cewa mus ab Allah yayiwa rayuwarku albarka Allah ya doraku akan makiya tashi kaje bana bukatar jin komai daga gareka, abinda zaka yake cikin zuciyarka na bayyana maka tunda nasan kai ba zaka iya baiyanashi ba, bayan kuma bayyanawar ita ce za ta zama silar shiryuwar wani, domin halayyar aminatu halayyar da ya kamata a bayyanawa duniya ce,ta shi kaje Allah ya fushshemu alkhairi ",cikin natsuwa da kamewarsa ya miƙe tare da bawa Nana sumba a saman goshinta dan karrama kalamanta da babu wanda ta yi kuskure ko son zuciya a cikinsa.

Yana fita ta daga hannunta sama ta yi addu'a me tsayi wadda babu wnada ya ji ko yasan me ta fadawa Ubangijinta daga ita sai shi.

A firgice zahida ta farka daga dan baccin da ya sace ta ba tare da ta sani ba,babu salati babu hailala haka ta miƙe a zabure ta faɗa bayi, duk dadewar da zahida ta saba yi a bayi ana kalkale kalkale yau bata samu dama ba dan bata son ta yi jinkirin barin gidan har ɗan ladi yazo ya sameta, a ranta babu wadda take tsinewa sama da anita da aminatu dan duk sune sila, a gurguje ta gama shirinta ta fito, kana kallonta zaka fahimci a firgice take saboda gayun da ta saba yi yau duk babushi,tana saukowa suka yi kicibus da mus ab ya fito daga sashen Nana,ɗan jim ta yi tana kallonsa bakinta na motsi kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta fita a sukwane kamar wadda ta samu kwancewar kai,girgiza kansa kawai yayi ya haye upstairs,bai samu aminatu ba dan tuni ta sulale ta koma ɗakin innawuro ta ci gaba da baccinta.

Zahida bata jima da fita ba sai ga ɗan ladi yazo ana rigima dashi wajen shiga,saboda kafin ta fita sai da ta bawa securitys din umarnin karsu sake su bar ɗan ladi ya shiga gidan duk haukan da zai yi musu kar su barsa,hakan yasa suka hanasa shiga, shi kuma ya dage sai ya shiga dan har ya fara tara musu jama a a kofar tangamemen gate ɗin, yanuyar da ake yi yasa gaba daya mutanen gidan suka fito, Abby ne ya fito ya sa aka bar dan ladi ya shigo, to da ya shigo din ma basu tsira ba dan ihu ya sa musu akan saiya shiga dakin zahida ko ta fito ya ganta,da suka kasa shawo kansa sai aminatu ce ta kawo dabarar bashi hoton zahida tare da kaisa wani daki daban,da wannan dabarar suka samu Salama akan tashin hankalin da zahida ta ballowa kanta.

Duk abinda ake mus ab naji kuma yana kallo amma da tanki bai tanka ba,har ya bar gidan babu wanda yaji ko tarinsa ne.

Shima Abby barin gidan yayi inda kai tsaye ya wuce gidan gonarsu inda suka saba haduwa da duk wani criminal Wanda yadanganci sirrinsu.
Chapter 30 · 0% Book details