← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 46

Sashe 31

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 6 min read

A nan ya samu Alhaji Kabir da Alhaji garba, sai kuma wani cusmer ɗinsu me suna danial,suna zaman jiran Abby ɗin, Abby Yana zuwa sai kuma ga ɗantunƙyi nan yana tafe yana layi sai kace tsinke kwakwa shaye shaye duk ya cinyesa, Abby Yana zama ki gaisawa basu yi ba ya fara tambayar dantunkyi sakamakon aikin da suka sashi na kashe Hajara,cikin maganar su ta cikakkun mashaya ya ce,"ya haj ai bamu samu kowa a gidan ba tun jiya bamu zauna ba saboda neman matar nan amma ɓat ta ɓata bamu sameta ba,sai dai na yi alƙawari da babata sai na kawo muku gawarta gabanku in dai hakan shine farin cikinku ya haj", da farko hankalinsu ya so ya tashi to amma da suka.tuna sun kwace duk wata sheda dake hannunta sai kuma hankalinsu ya kwanta,da ɗjn da ɗawa kusan kaf lauyoyin da zata iya tunkara sun sayesu dan haka basu da fargaba akan rashin mutuwar Hajara,kuma suna da tabbacin cewa in dai ta ji Br fele bai neme ba to ba shakka ita zata nemeshi tunda bata san komai akan abinda suke shirya mata wannan shine tunaninsu,dan haka Abby yagyara Zama tare da cewa "rabu da ita tunkyi muna zaune zata kawo mana kanta dan haka mu ci gaba da aikin binciken masu wancan asibitin ina ga shine abu mafi muhimmanci a halin yanzu".

Alhaji Garba zai yi magana kenan,Muryar wata yar jarida dake ta zango labarai a tashar tnn ta fara kawo kanun labaran da yayi matukar jan hankulansu da da sam baya kan tv.

Fyadam✍🏾

8064537048 opay Fatima yusha'u adam

Amount 500

Shaidar biya

08064537048
[4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page 23``*

A yau ne asibitin ABM suke gudanar da shagalin murnar cikarsa shekara biyu da fara aiki,wanda gashi nan dai kuna ganin yadda jama suke dafifi wajen zuwa dan taya wannan asibiti da ta samu nasarori masu tarin yawa a cikin shekara biyu murna, ga shi zaku ji kadan daga irin taimakon da wannan asibiti take yiwa talakawa a bakin daya daga cikin wanda suka samu tallafin aikin ido kyauta da suka saba yi duk watanni uku".

Daga nan ta aka.hasko wani bafulatanin dattijo yana feso bayanai na aikin warai da taimakawa matasa ƙarfi da tun kafa asibitin take yi,wanda ya zarta na asibitin GJK da suke yi wanda da yawan mutane suke zargin ba dan Allah suke yi ba akwai wata boyayyiyar manufa da yasa suke hakan dan janyo hankalin al umma,ya dora da cewa, "mun san cewa mutuwa dole ce da sanadi ko babu, amma mutuwar da ake yawan yi a asibitin GJK muna zargin bata Allah da Annabi ba ce,saboda a kullum idan ba a fidda gawa uku ba za a fidda ko da guda daya ko biyu ce,mun san cewa Allah ne me rayawa da kashewa kuma mun yadda da ingancin asibitin ABM,taimako kawai yake ba tare da ya bari munsan ko waye shi ba macece namiji ne Allahu a'alamu, muna samun magani kyauta, mjna samun kulawa ba tare da mun biya maƙudan kudade ba, kulawar da ko masu biyan maƙudan kudade basu sameta ba, babu kyara babu tsangwama, duk ƙankantar kudinka idan baka da lafiya kai tsaye zaka tafi wannan asibiti domin kasan ba za a koreka ba za a tsaya a duba lalurarka da kalilan din kuɗi cikin mutuntawa", yar jaridar ta watso masa tambaya da cewa, malam Bashir baka tsoron ace wannan mutanen kuɗi suka baka dan kawai kazo ka bayyana nasararsu ko ka tallata musu asibitinsu?"dariya yayi yana cewa wallahi ko kadan bana tsoro tunda nasan me gaskiya yana tare da Allah abinda na sani ne wallahi ban taba kebewa da ko nas din wannan asibiti da sunan makamanciyar wannan maganar ba bare masu asibitin da har yau babu wanda yasan ko da inuwarsu ne,Ni dai babu abinda zance sai Allah ya saka musu da alkhairi ya biya musu dukkan bukatunsu ya karesu daga sharrin magauta, Allah yasa masu tasowa su yi hali irin nasu", daga nan aka yanke magana dashi.

Babu abinda su Abby suke sai zufa suna mai kasa cewa komai,a haka aka ci gaba da nuno irin mutanen da asibitin ta taimaka da irin gudummawar da take bayarwa wajen marasa lafiya, Alhaji Garba ne ya kashe tv tare da kutuntuma wani uban ashar yana cewa,"tun farkon fara aikin asibitin nan na baku shawarar mu binciko me asibitin kuka ki acewarku babu wata asibiti ko me ikon da zai iya yin abinda asibitinmu ke iya yi,to yanzu ga irinta nan bamu yi maganin matsalar ba har sai da ta girmama", Abby ne ya sharce gumin da yake ta tsartuwa a goshinsa kana ya ce,tabbas ka fi mu gaskiya Garba mun yi sakaci da yawa,amma yanzu ba zamu kara barin kofar da hakan zata faru ba", juyawa yayi gun ɗan tunkyi da yake ta layi a zaunen ba faduwa yake neman yi,tsawa ya daka masa firgigit ya zabura yana cewa sorry ya haj na leka sama ta hamsinne na gano aljanna", Alhaji kabir ya ce,"a gidan uwarka zaka gano aljannar dalla ka bar shirme Ka nutsu kayi mana abinda ya dace",

"To ya haj ina saurare wa kuke so a sheƙe yanzu na sa ya shaƙi ƙamshin lahira?" Alhaji Kabir ya ce "wannan mutumin zaka nemo ka kawo mana shi nan", ya faɗa yana nuna masa hoton mutumin da ya gama magana yanzu a labarai akan asibitin ABM,wanda suka dauka a waya alokacin da yake ta zuba da zuzuta asibitin,kana ya ɗora da cewa, ba kashe shi zaka yi ba da ransa muke buƙatarsa dan dole sai mun fara bincikarsa ya gaya mana su waye masu wannan asibitin da kowa ya kasa ganosu"baka da matsala ya haj daga yanzu zuwa anjima ku zuba idon ganinmu dashi",daga nan suka sallami ɗantunƙyi da kudade masu yawa, sannan suka ci gaba da magana akan ainahin abinda ya tarasu.

Alhaji Garba daddyn zahida shi ya fara yin magana saboda duk ya fi su zakuwa da son ganin sun cimma manufarsu akan su aminatu dan kawai shima ya cimma tasa boyayyiyar manufar da su basu san yana da ita ba,numfashi yaja kafin cikin nuna muhimmancin maganar da zai yi ya ce,"ga danial nan shine yaron da Alfa Romeo ya aiko akan kasuwancin zuciyar kakar aminatu, saboda yanzu ne daidai lokacin da ya bamu akan samo masa irin zuciyar da tayi daidai da wadda yake nema, to kun san dai bature da rashin saba lokaci baran ma akan biyan buƙatarsa dan haka dole mu san abin yi akan ita kakar kafin mu cimma namu ƙudurin akan aminatu tunda ita dole sai mun samu wancan tsinannan da ubanta ya danƙawa ragamar komai nata sannan zamu samu yancin kasuwancinta",ya aje maganar yana binsu da kallo da sauraron abinda zasu ce,a hankali Abby ya janye tagumin da ya rafka hannu bibbiyu kana ya fesar da wani zazzafan huci ta bakinsa da hanci, sannan ya dubi danial da duk abinda suke fada ba ji yake ba dan da hausa suke maganar suna yi suna jefa fillanci shi yasa ya maida hankalinsa kan wayarsa tunda shi dan aike ne babu ruwansa da abinda suke fada abu daya ya sani shine su bashi amsar aikensa ya juyawa inda ya fito.
Chapter 31 · 0% Book details