Sashe 32
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read
Sai da Abby ya yiwa danial kallon sakonni sannan ya juya gare su yana cewa,"Garba duk abinda aka fada shine a raina bullowar wannan asibiti da kuma damuwar da zahida ta saka kanta a ciki shine duk ya jagula min lissafi,abinda yasa suka fi damuna kuwa shine wannan asibiti da ta ɓullo shahararta da ƙaruwarta wajen gwamnati da talakawa shine babban ƙalubalenmu dan kuwa ta dauko hanyar rushe gobenmu dan kuwa asibiti ita ce gobenmu ita ce gatanmu kusan fiye da rabin abinda muka samu da wanda muke samu duk ta hanyar wannan asibiti ce,to idan har ta rushe ta yaya zamu ci gaba da samun irin makudan kudaden da muke samu?abu na biyu kuma damuwar zahida, zahida ita ce ƙashin bayan asibiti, duk duniyar nan babu amintanccen likitar da zamu samu mu bata amanarmu ta riƙe mana sirri sama da zahida,to idan zahida bata cikin natsuwa ta yaya zata iya ci gaba da aiki ba tare da wata matsala ba?sanin kanku ne wannan kasuwancin namu yana bukatar jajirtacce kuma na gida me amana me irin zuciyarmu,shi yasa har muka yi dabarar gina rayuwar zahida da irin burinmu, to idan babu zahida wa muka sani ciki da bai me irin zuciyarmu da rikon amanarmu da rufe sirrin mu?"ya ƙare maganar yana kallonsu da dukkan zuciyarsa, fan zamowa Alhaji Kabir yayi kana shima ya fara magana cike da nuna gamsuwa akan maganganu da abinda Alhaji Jamil yake tunani,"babu kuskure a maganganunka gaba daya sai gaskiya dan haka Ni a ganina mu hada taura biyu a bakinmu duk zamu iya tunda muna da mataimaka ta ko wacce fuska,ma ana muji da lamarin zahida mu hadu mu samo mafitar damuwarta sannan mu ji da matsalar Mr alfa Romeo mu yi aikin da ya dace akan kakar aminatu, amma abu mafi muhimmanci dole mu fara da zahida tunda ita ce zata yi wannan aikin kaga dai-dai lokacin da zamu samar da zahida tuni mun gama tsare-tsaren hanyar kai kakar aminatu asibiti cikin dabarunmu da muka saba na kai duk wanda muke da bukata asibiti ba dan raɗin kansa ba", tafi suka saka gaba dayansu suna mai yin amanna da wannan shawarar dan haka daddyn zahida ya kuma gyara zama yana mai jin cewa shima wannan shawarar zata taimakesa wajen cimma manufarsa akan aminatu ko da kafin su cimma wancan babban burin ne tunda ba kasheta zai yi ma baiwar jikinta kawai yake so ya ɗanɗana,dan haka cikin farin cikin da ya fara bayyana saman fuskarsa ya ce,"to me zai hana aminatu ta dawo gidana na dan lokaci shi kuma yaron sai mu sa dantunkyi ya boye mana shi babu wanda zai kuma jin duriyarsa bare ya addabi rayuwar zahida ina ga wannan ce mafita kunga mun warware matsalar zahida cikin ƙanƙanin lokaci daga nan sai mu tafi kan wancan matakin",cike da farinciki suka amince da wannan shawarar farin cikinsu na mai bayyana suna ji kamar komai ya gama tafiya dai-dai,da wannan shawarar suka watse bayan sun sallami danial ya koma masaukinsa.
Da zafi zafi akan bugi karfe cewar Abby dan haka yana dawowa gida yamma liƙis yasa securityn da yake dan amanarsa ya buɗe ɗan ladi daga ɗakin da aka rufe sa aka hadashi da hoton zahida, Allah sarki bawan Allah duk ya rame a cikin kwana ɗaya da yini ɗaya,haka Abby yasa aka fitar dashi da yaudararsa kan zahida na can asibiti ya je ya sameta a can, duk gidan babu wanda yasan Abby yasa an fidda dan ladi sai aminatu da duk abinda ya faru akan idanunta ne, sai dai kuma bata kawo komai a ranta ba, bata san cewa Abby ya fitar da dan ladi ne dan su ɗantunƙyi su samu damar ɗaukesa ba,dan haka ta juya ta koma falo tana cewa haka kawai kin yi abinda zai cutar da bawan Allah wallahi Allah sai ya saka masa",
Sai da Abby ya haye bangarensa sannan ya kira wayar ɗantunƙyi ya sanar da shi ko mai tare da tura masa hoton dan ladi,an gama ya haj baka da damuwa shima wancan tsohon tuni mun cafke shi yana hannu",dariya Abby yasa tare da jinjinawa dantunkyi da yi masa kirarin da ya kuma tunzurashi da fasa masa kai.
Ɗan ladi yana kan hanyarsa ta zuwa asibitin a ƙafa ba tare da yayi tunanin abin hawa ba, dan gaba daya hankalinsa baya tare dashi burinsa kawai ya sanya zahida a cikin idanunsa dan haka tafiya kawai yake ba tare da jin wata gajiya ba,bai yi wani nisa sosai ba ya ga baƙar mota me baƙin galashi ta tsaya a gabansa kafin kuma wata matashiyar budurwa ta leƙo daga cikin motar tana kiran sunansa,bai ko yi alamar tsayawa ba har sai da yaji tana cewa zahida ce fa take maka magana", ai da gudu ɗan ladi ya juyo zuwa gaban motar yana fadin "masoyiya zahida kina ina?"budurwar ce ta kuma bude masa bayan mota tana cewa "ka shigo tana cikin mota", ba tare da hayyaci ba dan ladi ya shige mota, yana shiga suka fesa masa wata hoda shi kenan aikinsu ya kammala suka figi mota suka wuce inda Nima ban sani ba.
Ajiyar zuciya Abby ya sauke bayan da ya gama jin cewa an gama da batun ɗan ladi, waya ya daga ya kira zahida, sai da ya kira sau uku bata daga ba kafin ana hudun ta daga, ba ta yi magana ba sai sheshsheƙar kukanta da ya ji, cikin nutuswa da kamalar da suke yaudarar mutane da ita ya ce".calm down my zahida wai meye matsalarki ne?" Cikin kuka zahida ta ce haba Abby yanzu dama baka san damuwata baka san me yake samun zuciyata ba?"sorry zahida ki kwantar da hankalinki ai mun riga mun gama yi Miki maganin damuwarki karfa ki manta zahida ke ce rayuwarmu idan har muka barki da samuwar da zata rusa farinciki ki muma ta rusamu to meye amfanin so da muhimmancin da kike dashi a gunmu,ki dawo gida haka tuni mun yi maganin matsalarki da dan ladi bazaki sake ganinsa ba a rayuwarki bare ya tayar Miki da hankali ya hanaki nutsuwa itama aminatun ki cireta daga lissafin mutanen da zasu hanaki walwala gobe zuwa jibi zata koma gidanku bazata dawo gidan nan ba har abada bare ta raɓi mijinki mus ab naki ne ke kadai ɗiyar arziki", wani irin ihun murna zahida ta saki ji take kamar ta shiga ta cikin wayar ta rungume Abby saboda tsananin farinciki,dakatar da ita Abby yayi da cewa amma ina so ki yi min alkawari daya zaki nutsu ki kwnatar da hankalinki ki mana duk abind amuke so dan akwai aikin da zaki yi shi a cikin kwannakin nan kuma ba akan kowa ba ne sai innawuro kakar aminatu", good Abby aiki ya biyo ta kan mayu kenan in dai wannan ne KAR ku ji komai dan kuwa rayuta fansa ce akan duk abinda kuke so", cikin farinciki Abby ya sauke wayar bayan ya tabbatar mata gobe zasu haɗu a gidan gona dan shirye shiryen aikin.
Kowa yayi mamakin yadda zahida ta shigo gidan cikin farinciki da walwala wanda ko a baya da bata da wata damuwa bata kasancewa cikin wannan yanayin,sai dai babu wanda ya tanka mata akan hakan hatta da Khalid yau yaga canji a gun maminsa dan har fara'a ta yi masa wanda hakan ya yi masa wani banbarakwai ya kasa tanka mata sai kallo da ya bita dashi har ta haye upstairs,sai a lokacinne ma nana ta tuna da ɗan ladi dan haka ta dubi aminatu da take ta ɗurawa cikin ta wani hadin kankana da kabewa da madara da zuma da kwakwa da nana ta hada mata wanda kusan yanzu duk ire_iren kayan nan ne suka zama cimar aminatu, shi yasa kullum zaka ga kamar gana cnja maka kamar wata tarwada sabida sheki da kyau ciki da waje,ta ce."aminatu in kin gama je ki samar da faf security ya foto da dan ladi haka nan a lallɓashi ya tafi gida"aminatu da ta cika bakinta da wannan hadin ta ce ,"kai Nana wane dan ladin?ai tuni Abby yasa an fito dashi ya tafi gida abinsa", hamdala Nana ta yi tana mai ci gaba da kallon labaran da aka wuni yau ana haskowa na asibitin ABM.
Fyadam✍🏾
Amount 500
8064537048
Fatima yushau adam opay
[4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page24``*
Ɗif nana da ta maida hankalinta kacokam kan saurare da kallon haɗaɗɗen asibitin taji ankashe tvn,da sauri ta ɗago dan ganin waye me wannan wulaƙancin, haɗa ido su kayi da Abby wanda yayi saurin sauya yanayin ɓacin ran da yake ciki akan ganin asibitin ya waske da dage mata gira yana cewa "gaba ɗaya kin maida hankalinki kan TV yau bakya ta ni ba dole na kashe ba tunda yau na samu kishiya"dan murmushi nana tayi tana mai gyara zamanta da matsawa saboda kokarin zaman da Abby yake yi, kana ta ce,nima da ka dawo ai baka neme ni ba kaga kuwa dole na kama kaina",yar dariya yayi sannan ya ce,kuma fa kin fini gaskiya to kaina bisa wuya wani dan aiki na karasa shigarwa a computer shi yasa ban miki magana ba",juyawa yayi inda aminatu da Khalid suke zaune sun maida hankalinsu kan wasan yar tsun da suke yi,dariya Abby yayi yana kiram sunansu,tare da cewa aminatu ke sam bakya girma yanzu dan Allah ina ke ina wannan wasan wannan ai wasan yara ne", dan tura bakin ta yi kafin ta ce", Allah kuwa abby har yanzu ban girma ba gaba daya shekarata fa sha takwas dan haka sai sanda khalid ya girma nima zan girma", rike baki nana ta yi ta ce ah lallai ba girman za ki yi ba", khalid ya ce,to nima nana ai banaso adda aminatu ta girma ta barni dan kar na rasa dan wasa shi yasa na fido mu girma tare", dariya suka sa gaba daya suna jinjina shirmen Khalid da aminatu wamda har ma Gara Khalid din tunda akan kuruciyarsa yake.