← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 46

Sashe 43

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read

Zahida tana zuwa ta buƙaci ganin matar a office ɗinta,Mata me shekaru sittin da yan kai ta zauna ta zaiyanewa Zahida abinda yake damunta ta ɗora da cewa, "wannan yaron ne ya ga halin da nake ciki a titi da lalura Shi yasa ya ce zai kawo Ni inda za a taimaka min a bani magani kyauta ba tare da ko sisina ba,da na dauka ma wancan dayan asibitin da ake ce masa ko ABM Shi zai kai Ni sai kuma naga ashe nan ne,yar nan da tafiya zan yi wlh saboda na fi gamsuwa da wancan asibitin fiye ds nan ɗin,sai dai kuma yadda wanda ya barni tare da su suka dinga koɗa min irin tsaimakonku da tabbatar min da cewa duk abinda ake fada a kanku karya ne,yasa na hakura na zauna har kika zo kika sameni",da kyar zahida ta kai zuciyarta nesa ba ta sheƙe matar nan da mari ba, amma fuskarta babu wata fara a acunkushe take. kana kallonta kasan cewa dole take zaune da matar nan a gabanta,wani ruwan magani ta mikawa matar tare da cewa "karbi nan kisha taimakon farko ne da wannan asibitin ta fara baki",babu wani tunani matar nan ta karba maganin ta sha kamar yadda zahida ta umarce ta,tana sha ko minti daya ba a yi ba ta bingire da bacci, da sauri zahida ta mike tare da kiran Dr Samir a waya,cikin kankanin lokaci yazo a ka taitayi matar zuwa dakin tiyata.

Sosai mus ab yayi kokarin yiwa Nana bayani ta yadda zata fahimta,to dake ita ma a nutsen take ta fahimceshi sosai. sai dai kuma abin ya matukar bata mamaki ya kuma tsaya mata kamar yadda ya tsaya musu shida innawuro dan ba zai sa waccan shargallen a ciki ba dan ita baka taba gane damuwarta kullum cikin yanayinta na calikanci take aminatu kenan matar dan birni, jin shigowar Abby yasa shi mikewa ya baro dakin ya fice ta can baya ba tare da ya bari sun hadu da Abby din ba.

Hankalinsu ya kwanta saboda sun samu nasarar cire zuciyar wannan matar,sai dai kuma sun lulluɓe Mr alfa ba su sanar dashi an samu canji ba kuma basu gwada wannan zuciyar ba cireta kawai su kayi,ko gawar matar can suka jefar a juji kamar yadda suka saba duk sanda suka gabatar da irin wannan aikin.

Kwana biyu hankula sun kwanta a wajen su Abby suna daukar cewa duk acikin nasarar sune suka samu kan aminatu ta yi hakuri da rashin innawuro.mus ab kuwa bai ce komai ba bayan addu'ar Allah ya baiyanata cikin aminci. Anne Kam tunda ake wannan turka turkan cikanku ba ta ce ba,wanda hakan ya matukar harzuƙa aminatu, duk abinda za a yi da abinda za a ce tana daki idan ma tana kusa ko kallo baku isheta ba,bare ta tofa tata, shi yasa aminatu ta ci alwashin sai tasa ta tayi magana dan dole shegiyar tsohuwa me kan kwakwa da baƙin rai.

A can bangaren gidan Alhaji Garba kuwa Hajara ta kama aiki gadan gadan ,wanda hakan yake yiwa Hajiya zubaida dadi gashi ta samu abokiyar debe kewa,saboda ta fi azumi kwari da wayewa,shi ko Alhaji Garba gaba daya ya maida hankalinsa kanta saboda yasan tana dauke da kadarar da zasu iya samun manyan kudaɗe da ita,dan haka shima lallaɓata yake yana kyautata mata duk dan ta kara yarda da su ta yadda zata kawo ɗanta gidan ba tare da wata tantama ba.

Yau Litinin da wuri Abby ya fita, dan har ya riga Zahida barin gidan,dan yanzu kuma gaba daya hankalinsu ya koma kan binciken asibitin ABM da kuma Br, a baya daukar al'amarin suke yi karami sai kuma yanzu da suka samu kansu cikin kasa nemo shaida daya da zata sa su gano waye br,haka a bangaren asibitin duk da cewa suna bi suna kama wasu mutane da suke ganin suna da dangantaka da asibitin dan tuhumarsu da yi musu barazanar mutuwa,sai dai babu wani labari maganar daya ce basu sani ba ko da kuwa zasu kashe su ne, wannan abu ba ƙaramin tayar musu da hankali yake ba, dan kasuwancin ma a yanzu sun dan lafa masa saboda sun fuskanci mutane sun yi matuƙar sa musu ido musamman da yawan mace_mace ya ƙaru a sibitin nasu.

Ta fannin Zahida da kuwa ganin aminatu ta dawo gidan sai kawai ta kirkiri tafiya dan kawai ba zata iya jurar ganin aminatun a garin kuma tana numfashi daidai da nata ba,aminatu kuwa ko ajikinta bata ma san tana yi ba walwalar ta take yi ta yadda duk wanda ya ganta zai shaida cewa bata da wata damuwa.

Khalid ne zaune shida aminatu tana koya masa assignment, isma ne ya shigo falon wanda tun dawowarsa gida basu taba haduwa da aminatu ba saboda shi din ba wani zama yake ba, sannan isma dan sharholiya ne na bugawa a jarida shi yasa yawanci ya fi kwana a waje,Dan can wajen yafi sakewa yayi shaye shayensa ba tare da sa idon mus ab ba.duk da cewa har yanzu mus ab bai san boyayyun halaiyar isma ta shaye shaye da Neman mata ba, wannan dalilin ne yasa yake Dan zaman gidan dan kar wata rana mus ab ya fahimci banzar dabi'ars.,zama yayi a kujera yana ƙure aminatu da ido yana tunanin wannan hurul inin kuma daga ina? Khalid ne ya katse masa tunani ta hanyar gaidasa ,firgigit yayi yana dan shafa ƙeyarsa kafin yace ,"Khalid wannan wacece,?", dariya Khalid yayi tare da cewa "kai uncle isma adda aminatu ce baka sani ba?" Sai a sannan ya tuna yaji Nana tana yawan ambatar sunan,oh na tuna ya fada yana kannewa aminatu ido cike da nuna duniyanci,harararsa aminatu ta yi har da jan siririn tsaki kafin ta fara tattare littafan da suke a baje a gabansu dan barin wajen,sai da ta hade su tsaf ta mike zata bar wajen, ganin haka da isma yayi sai kawai ya yi saurin sa ƙafarsa a hanya, ba tare da ta yi aune ba kuwa ta ci wani mugun tuntunɓe da kafar isma, sai gata kif ta wadi kasa, ta ji zafi kuwa sosai dan take ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya,Anne ce ta fito tana cewa "to yar fama yar mai, yau dai masu sangarta kin basa nan idan kika kuskura kika min taɓara zaneki zan sa ila yayi",khalid ne ya jawo hannunta yana kokarin dagata idanunsa cike da hawayen damuwar kukan da aminatu take yi,isma ya ce "rabu da ita Anne Ni ne nan na yarbar da ita,dan iskanci ni da gidanmu amma na shigo yarinyar nan ko kallo ban isheta ba sai kace wata yar karuna, to ko shi karunan ba zai nuna mana girman kai da iya shegantaka ba",Anne ta ce "yauwa dan albarka sai yanzu na samu me goya min baya dan ita zahidar da basa mutuncin itama ba ɗaɗa ni ta yi da kasa ba bare na dinga sata tana ci min ubanta,amma yanzu tunda Allah ya kawo min kai takaicina ya ƙare", ta karasa maganar da zabgawa aminatu harara,isma kuwa gyara kwanciyarsa yayi saman doguwar kujera yana cewa,"ke me idon mage maza je ki kawo min abinci nan ko yanzu na kwakule idanun,"da sauri aminatu ta yi gaba sai da ta je dab da upstairs din mus' ab,sannan ta juyo ta ce,"naki ba zan kawo ba ,kuma Allah ya isa na ban yafe ba mugu dan shaye shaye", wata mahaukaciyar ashar isma ya yiwa aminatu wadda tasa ta haura sama da gudu tana masa gwalo,shi kuwa gaba dayaa kansa ne ya daure ta yaya yarinyar da yau din nan ya fara ganinta ta san halinsa da ko uwarsa da ubansa basu san yana yi ba,tashi yayi ya fita daga falon yana fadin lallai yarinyar nan watan mutuwar ki ne ya kama dan idan ba ki iya bakinki a gidan nan ba sai na illataki.anne kuwa zagin aminatu ta shiga yi wai ta yiwa jikanta sharri.

Isma ya jima ya na mamaki da son gano ta yadda akayi wannan yarinyar me kama da aljanu ta san yana shaye shaye, sai da yaga yana neman zautuwa saboda tunani sannan ya hakura da zama akan cewa hasashe aminatu ta yi, dan haka ya ci burin gallazawa rayuwarta tunda har ta shiga gonarsa.

Da misalin ƙarfe shida na yamma aminatu ce ita da Nana da larai a kiching suna karasa hada dinner, nana ce ta dubi aminatu ta ce,maza aminatu ku karasa jera kayan bisa dinbin Ni kuma bari na je na yi alwala tunda nasan ke bayi za ki yi ba,idan yaso sai ki ɗauki na Anne ki Kai Mata,ke kuma larai ki kaiwa isma nasa can bangarensu", da sauri aminatu ta ce,bari na kai musu larai kuma ta karasa jerawa a dinning",nana ta ce to kin san dakin nasa ne"?kai tsaye qminatu ta amsa da ",EY duk kuwa da cewa bata sani din ba,amma ba zata bar wannan damar ta ramakon abinda yayi mata ya wuce ba, daukar kular abincin ta yi ta fara kaiwa Anne nata ta fito ba tare da ta kula da harara da habaicin da ta saba yi mata ba,komawa kiching ɗin ta yi,.bata samu kowa a kiching ɗin ba dan haka ta dauki kayan abincin isma din, juyowar da zata yi kuwa sai goshinta ya bigi kirjin isma da tun fitowarta daga ɓangaren Anne ya biyota zuwa kiching ɗin,a razane ta dago kanta tana kallon isma din da yake watsa mata wani banzan kallo da bata san da wane abu zata fassarashi ba, zube kayan da ta dauka.ta yi tana ja da baya cike da tsoron da ya bayyana saman fusmarta,Binta ya fara yana cewa wa na kama?" Kwaɓe fuska ta yi zata fasa kuka yayi saurin sa hannunsa saman labbansa yayi mata alamun ta yi shiru,hadiye kukan ta yi tana kuma ja da baya saboda kusanto tan da yake kuma yi,ƙafarsa da ke sanye da wani shegen takalmin ball yasa ya take yatsun ƙafaarta da karfi take aminatu ta kurma ihun da.yake.tafr dw wani irin kukan azaba,wanda haka. Yasa isma saurin ficewa daga kiching ɗin ta kofar baya,zubewa ta yi a gun tana kuka me taɓa zuciya,
Chapter 43 · 0% Book details