← Book details Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Page 14.
Najeeb ya rasa sukuni yaje restaurant din da yaganta yafi a kirga ko mai kalarta bai gani ba gaba daya ya rasa ina zai tsoma ranshi hutun da suka zo yi ya kare amma ya kasa komawa farooq har ya gaji da bashi baki yau satinshi uku da ganinta kenan amma ba wani improvement haka dai suka lallaba suka dawo nigeria dama sun gama law school dinsu ne suka zo yawonsu US ya hadu da wannan fitinar injishi fa ba inji sawwama ba😊 atoh ko da suka dawo haka yake ba wani kuzari har suka kama aiki a federal court of Nigeria a matsayin cikakun barristers kuma suka hada jari suka bude company jeweleries na zallan precious stones 😉 wai abin na manya ne.
***** ***** *****
Zaman umm Maimartaba alhmdlh bata fuskantar matsalar komi maimartaba naji da ita kasancewarta mai yawan biyayya gata da sanyin hali girkinta ta cigaba da koya domin da kanta take yiwa mai martaba a halin yanzu yaranta uku a cikin shekara biyar kuga ikon Allah kuma dukka maza 😀mu'amalarta da haj najma kuma toh dai gashi nan ne ba sa hurda sai su fi wata uku basu ga juna kasancewar kowa da part dinshi bata zaginta ko hararanta ko hantararta ah ah sabgarta ce kawai bata Shiga babbar yarta ko naja'atu in tazo gari tana shigowa wajenta ta wuni ba ruwanta da kishin da ke tsakaninta da mamanta aunty take ce mata haka najeeb ai shi kam dan gidanta ne komi yake son ci aunty komi aunty tun mamin shi najin haushi har ta zuba mishi ido haka shi da farooq zasu je suta a ga in suna gari aunty kaza zamu ci tace toh dukkansu biyu tana ji dasu Dan baza ta taba manta farooq ba shine silar jin dadinta a yau randa farooq ya ganta a maysayin matar mai martaba yayi mamaki sosai tare suka Shiga da najeeb shi ya gayawa najeeb ita wacece najeeb ma yayi mamaki amma be ce komi ba tabe baki kawai yayi a lokacin da farooq ya tambayi ina laure tana hawaye ta gaya musu abinda ya faru sosai suka tausaya mata mussamman najeeb da yake cike da dana sanin abinda ya aikatawa laure gashi yanxu bata.
****** **** *******
WASU 'YAN SHEKARU
Ko bayan da alh sa'ad da haj Selma suka gayawa laure yanda suka sameta itama ta basu nata lbrn sun tausaya mata sosai kuma haj salma ta tabbatarwa da Laura ba abin da waziri ya mata sun kuma yi alqawarin zasu maidata masarautar kuma su tsaya mata a kwatar mata yanci wurin tsohon banzan, suka kuma nemi alfarmar ta jira su kammala abinda ya kawosu US Kafin su maidata hakan yasa ta Shiga university inda take karantar English language cikin shekaru uku ta hada degree dinta kasancewarta m hazaka ta fito da result me kyau a shekarar kuma suka yi haramar dawowa gida Nigeria sosai kawayenta suka yi kukan rabuwa tare da mata alkawarin zuwa wani lokaci.

***** ****** ******
A firgice ya farka duk ya jike kanshi ya rike da hannu biyu wannan wani irin masifa ne sai kace wacce yayiwa fyade toh koh dai ba mutum bace tunda dama cewa aka yi ta bata innalillahi wa inna ilaihi raju'un abin da ya furta a fili kenan kafin ya tashi ya Shiga bathroom ya watsa ruwa yayi Alawla yayi sallan la'asar wayoyinshi ya dauka dan tsaki yayi me yasa be bi farooq borno yin weekend bane mtsw ba zai iya zama ba bauchi zai tafi da sauri ya sakko ya kira driver ya zo ya driving dinshi sbd ya dawo da motan isansu airport din ya sallameshi ya shiga yana cikin yankan ticket kaman ance ya juya ya hangota da trolley ba zai taba manta fuskar nan ba hanyan waje suka nufa da sauri ya bi bayansu yana fits tana shiga mota driver naja rasa yanda zaiyi yayi sai ya naushi tayan taxi din dake gabanshi dan ko yace zai bisu a taxi a yanda aka ja motan kafin su juya ma sun musu nisa haka ya hkr ya koma ciki ya hau flight din bauchi
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA💖

By Sawwama Ameen.

Page 15.
Tunda suka dawo Nigeria Laura ta rasa sukuni bata da wani buri da ya wuce ta ganta a masarautar bauchi taje taga wani hali ummienta take, shekara uku zuwa hudu da dawowar hankalinta amma bata je taga umminta ba? Ko tana masarutar ma oho ko tana raye wa ya sani. Ji tayi hankalinta ya tashi sosai baza ta iya jira sai sunje borno wajen familyn su daddy ba kafin ta ga umminta yau fa satinsu uku da dawowa zuwa zata yi gaskiya tacewa dady ita a tafi bauchi gobe ta mike ta zari slippers dinta ta sauko kasa momynta ta gani da wata mata suna hira suna shewa ta gaishe da matar da take mata wani kallon sha tara sannan cikin harshen kanuri ta tambayi mom dinta inda dadyn yake momyn ta mayar mata da hausa yana study room dinshi hanyan ta nufa tun kafin ta kulle taji matar na cewa momy ke ko hajiya salma ina kika samo yarinya kyakyawa haka hala er dan uwanki ne kaman baza ta tsaya taji amsan da momyn zata ba ta ba dan bai wuce tace erta bace da mamakinta sai taji momyn nacewa haba hajiya kaltume har kin manta yarinyan da nace miki mun tsinta shekaru kusan goma da suka wuce kafin tafiyar mu US? Rike baki matar tayi tace tab itace haka lallai kinyi sake da kika rike yarinyan da baki da alakar jini da ita salon ta kwace miki miji ji wani banzar shiga da tayi wai ita a dole ta waye ta girma a turai(a lokacin wata er karamar rigace a jikinta da 3 quarter) kuma a haka mijinki ke ganinta tsaban dabbanci ma yanxu wurin shi ta nufa wa ya san badakalar da suke miki in ba kya nan auzubillah shine kalmar da ta furta a hankali ta shiga study room din tana mamakin kawar momynta.
Ko da ta sami dadyn da batun tafiyarta gobe hkr ya kara bata yace ta bari zuwa next week ya gama abin da yake yi bata so haka ba dan ta tsorata da maganganun hajiya kaltume.

***** ***** *****
Abu kamar wasa haj salma ta canzawa Laura sai ta dinga hade mata rai ko ta hantareta sosai abin ya bata mamaki yanda ta dauki zuga tashi daya
Kwana hudu da yin maganansu haj salma sai ga haj kaltume ta dawo ita Laura din ma bata San ta zo ba kasancewar tana study room tana duba wani littafin turanci ta fito kenan taji wani abu da ya gigita mata kwakwalwa haj salma ke cewa dadin abin cikin satin nan zamu maida ta inda ta fito sai haj kaltime tace yaji dadin zuwa neman auranta wajen yan uwanta kenan ke wani sa'in kaman baki da wayo yanxu ki bar min komi a hannuna gobe ki aiketa airport road zaki ga aiki da cikawa kina ganin yanda ta saba da hutun nan zata iya zaman kauye ko bauta ne komawa study din tayi da sauri tana mai da numfashi tsoro ya cikata sosai me suke nufi ne wai Allah sarki daddy bai taba kallonta da wani manufa ba amma MUGUWAR KAWA na gurbata tunanin momy.

***** ****** ******

Abinci suke ci a kan food mat amma ko cokali daya ta kasa kaiwa bakinta ga al' amin nan sai wasa yake da abincin shi amma bata tsawatar mishi ba abinda ya ankarar da maimartaba kenan kasancewarta mace me kula da table manners khadijahh ya kira sunanta kusan sau uku kafin ta farga riko hannunta yayi yace me ke damun matata duk nake ganinta doll kwana biyun nan fada mun matsalarki hawaye ne ya zubo mata tace yallabai wlh kwana biyun nan mafarke mafarken laure nake yi sai dai in ban kwanta bacci ba in kuma idona biyu toh tunaninta ya ta crossing mind dina kenan(su dija anji turanci)😜ban San me me ke faruwa ba ya Allah in yarinyan nan na da rai Allah ka bayyana ta in kuma mutuwa tayi Allah ka karawa kabarinta haske hannu ya sa yana goge mata hawaye cike da tausayawa yace kar ki damu zamu tsananta addua kuma zan sa ayi ya kamata gobe muje mu duba su hajja da daddare gaba dayanmu harda najma gyada mishi kai tayi tare da kwantar da kanta a kafadarshi najeeb ne yayi sallama suka amsa aka bashi izinin shigowa kasancewar wajen is private ko borori basa zuwa wajen a hka ya same su shikan rayuwan mahaifinshi na bashi sha'awa yanda ya ke nunawa matansa so gwanin sha'awa yana fatan allh ya hada shi da yarinyan nan ya nuna mata so kwatankwacin yanda abee dinshi ke nunawa matanshi ko ma fiye da haka su zama abu daya MASOYAN JUNA.
[6/30, 8:48 PM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA. 💖

By Sawwama Ameen.

Assalamu alaikum dan Allah kuyi hkr da wannan bana wani jin dadine dauriya ne kawai ga rashin charge. Na gode
Chapter 5 · 0% Book details