← Book details Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai hankalinshi ya tashi yaje yana rokanta ta saurareshi hannu ta daga mishi✋🏼 tace me za ka ce min sa'eed ni dama na San ranan nan yana tafe ranan da za a aura ma ka er kasarku na yaudari kaina da nayi tunanin ni kadai zan mallakeka ta Dan ja hanci kadan tace gwara in koma inda na fi wayo ta bude drawer ta fara fitar da kayanta shamatanta yayi ya rungumeta da karfi ta fara kokarin kwacewa tsam ya riketa sai da ta gama turje turjenta ya fara magana cikin sanyi najma ke kin sanni ina sonki ba kadan ba hasalima tsananin son da nake miki ya hana min kara aure tun shekaru coma sha da suka wuce da baffana ya so in Kara aure ke shaida ce akan haka yanxu najee dan baffa ya yanke hukunci akaina ke ba me tayani yi mishi biyayya bane baffanmu ne fa haba najee. Hanci ta Dan ja sannan ta dan zame jikinta kadan tace ni ban hanaka yiwa baffa biyayye ba kawai... Saurin katseta yayi da cewa toh in dai haka ne let's not question his decision karamar yayarinya ce fa ba kowa bace ba er kowa bace hasalima ko makaranta batiba kar kiyi tunanin zata iya kwaceni a wajenki am urs alone ke kin San da haka ya dan kashe mata ido haka dai yayi ta lallashinta da dadadan kalamu irin nasu na maza har ta sauko amma ta tabbatar mishi ita dai ba ruwanta da amaryarsa da bata son raini yace hakan ma yayi tunda dai ta amince.
An daura auren khadija (dija) da maimartaba sa'eed a ranan juma'a inda ita dija bata San waye mijin da aka mata aure da shi ba sai da kanwar ita memartaban ta zo ta dinga bata shawarwari akan zaman auren gidan sarauta kuka ummi dija ke yi sosai ta rasa wani irin godia zata yiwa Allah ina ma ace Laura na tare da ita.
***** **** *****
BAYAN SHEKARA 5
Zaune suke a wani coffee shop su hudu ne Regina Brett da Allison Mills Rebecca indigo sai ta hudunsu LAURA MUHD magana suke akan prom night kokari suke su convincing Laura taje ita kuma ta dage baza ta ba Becca ce tace loh mun san ba kya son zuwa parties kuma iyayenki ma suna goyon bayanki amma wannan prom night din mu ne fa babe all those years in high school we are finally saying goodbye to high school Gina say something ta juya ga Regina haka dai suka yi ta kokari har suka convincing dinta tana amincewa Allison tace ai sai a tashi a tafi shopping nan take ko suka tashi cike da farin ciki.
Mall kala kala da boutique kala kala suka je bayan sun gama siyan kayayakin su ne suka deciding suje su ci lunch bayan sun gama sun fito ne ya hangota ya illahi who is this beautiful creature abin da ya fada kenan sosai ya shagala da kallonta har suka shiga motarsu Rebecca ta bata wuta farooq ne ya lura hnklnsa baya jikinsa ya girgiza shi yana fadin dude meke faruwa? Shit! Abin da ya fada kenan ta wuce farooq yace wacece? A kideme ya rike hannun farooq yace bestie da gaske baka ganta ba wata yarinya gatan dai chocolate average height ta sa loose skirt and top ta rolling gyale ko Dan kwali ne whatever tana tare da frnds dinka guda3 yes da ita 4 kenan saurin taranshi farooq yayi yace dude hold on hold on sai zuba kake kamar ba kai ba what is it about her runtse ido yayi tare tura hannunshi daya cikin gashi yace isn't obvious dude am into her I want her farooq yace toh yanxu meye abin yi? I dunno maybe in dawo nan gobe ko zan ganta murmushi faruuq yayi yace huh? Sai kawai yaja bakinshi yayi shiru suka wuce
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA💖
By Sawwama Ameen.

Page 12.
Allahuma taqabbal minna wa min kum.
Sadaukarwa ga members na Novel, make up and kitchen by admin of admins YAYA HAYAT.

PROM NIGHT
Sun yi kyau sosai su hudun ko wacce a cikin dress dinta Laura ce kawai ke sanye da gown har kasa light blue ne sai ta sa silver jewelry da silver purse and hills tayi kyau sosai tana tsaye daga gefe yayin da sauran suka je wajen date dinsu Gina ce ta zo tare da saurayinta suka tsaya ta mika mata soft drink suna sipping sai zuwa ake ana gaisawa da su kasancewar su popular crew na high school Rebecca ce tazo janye da hannun brody saurayinta ta daga murya saboda da kidan da aka sake tace brody thinks I should have my first drink (beer) Laura da Regina a tare suka ce NO Gina tace wait till u turn 18 ta kalleshi ta daga kafada alamun kaji sai kawai suka cigaba da hiransu.
Sanar da fara rawa akayi suka shiga cikin filin rawan suka barta a tsaye sunyi sunyi ta zo suyi tare taki maza da yawa en class dinsu sunzo suyi rawar tare amma taki tana tsaye ta shagala da kallon irin rqwan haukan da Becca takeyi tana dariya taji an mata rada a kunne wai ko za tayi rawa juyawan da zata yi sai ta ga Scott ne football captain na school dinsu da most popular guy hada rai tayi dan ba tun yau yake damunta ba har gida ya zo ya sameta wai ta zo prom da shi tace baza ta ba gaba daya gashi yanzu sun hadu juyawa tayi ta dau hanyan fita dai dai lokacin da Karen date dinshi ta hango ya riko hannun Laura kallon shi tayi ranta a bace ta zare hannunta a hankali dan masifa har cinta yake amma sabida bata so ta causing scene a prom dinsu ya sa tayi shiru ta kama hanyantq biyota yayi karen na ganin haka ta bi bayansu dai dai za ta fita Becca ta hangota sannan ta hango Scott ya bita ga Karen ma ta bisu tace oh no this is going to be bad ta tabo su Allison suka biyo bayansu da sauri amma ina sun yi latti dan suna isa suka tarar da Laura a kwance jini na biyo karkashin kanta Karen sai kuka take yi yayinda Scott ke kokarin kiran ambulance kafin kace me har gurin ya cika duk students din sun fito ambulance na zuwa Becca ta shiga tare da ita yayinda su Gina suka biyosu a motarsu bayan sun kira iyayenta Scott ma da Karen bin bayansu suka yi haka principal da daya daga teachers dinsu karen sai kuka take yi kasancewar ita ta tureta ta fadi da steps din tana ta bawa iyayenta hakuri tana fadin ita bata san haka zai faru ba Allison ce ta shako ta da kyar aka banbareta a jikinta suna nan tsaye har asuba doctors din suka fito it was successful tana bacci sai lokacin hankalin kowa ya kwanta daddynta yace Scott ya kai Karen gida suka tafi yace su Regina ma su tafi suka ce wai sai ta farfado duk su suka janyo da suka tilasta mata sai da tqje yanxu gashi sun sa tana kwance yace musu ba damuwa.
Bata farka ba sai wajen goma a lokacin su Becca sunje yin breakfast a restaurant din asibitin iyayenta ne kawai a dakin magana take a hnkl amma bata bude ido ba saurin karasawa wajenta suka yi kuka take ta na fadin kusu wadi munyal a tare mom and dad dinta suka ce fulatanci kuma iyakar sanin da suka yi su kanuri da Hausa kawai suke mata a gida dan basa so su dawo Nigeria bata iya Hausa ba a waje kadai take turanci toh fulatanci daga ina zaro ido mumyn tayi ta kalli mijinta tace are you thinking what am thinking? Gumi ya share da handkerchief duk da ac din da ke asibitin yace yeah Allah dai ya bata lafiya shine ya fi mahimmaanci a hankali ta bude ido ta sauke a kansu kallonsu kawai take ta san fuskansu amma kanta ya daure a hankali take binsu da kallo har su Becca suka shigo da gudu suka fado kanta suna Murna sai surutu suke suna gaya mata yanda hankalinsu ya tashi ita dai sai binsu take da ido a haka doctor ya shigo ya mata gwaje gwaje sannan ya kira Alh sa'eed ya mishi bayanin ba komi komai ya dawo normal anyi nasara ma jinin da ya toshe mata wani jijiya ya bude tunaninta ya dawo kuma bata manta komi ba hamdala yayi aka discharging dinsu suka dunguma sai gida har lokacin ba tacewa kowa komi ba har su Becca suka fara damuwa sai da mumynta tace maybe stress ne su barta ta huta suka mata sallama suka tafi.
Sai da tayi kwana uku tana hutawa a hankali ta dinga tuna rayuwarta da umminta da wadannna bayin Allahn sai dare yayi tayi ta kuka ita kadai yanda ba Wanda zaiji tana rokan Allah yasa waziri bai aikata mugun nufinshi a kanta ba to wai ma ya akayi ta zo hannun wadannan ita iya abinda take tunawa bayan zuwansu US ne bata San ya akayi tazo wajensu ba amma tana tuna dukkan rayuwan da suka yi tare da duk wani kyautatawarsu a gareta.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASAYON JUNA💖

By Sawwama Ameen.
Afuwan zaku ga mun sa mu page 11 biyu kuskure aka samu yanxu a page 14 zamu tashi ba 13 ba

Wannan shafin naki ne er uwa rabin jiki ke kika farkar dani,ke kika tabbatar min zan iya rubutun nan Allah ya kara hada kan zuriyar AG amin ba kowa bace kharimatu AG ce mrs mai iyali😜lol
Chapter 4 · 0% Book details