← Book details Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani ikon Allah maimartaba ya rasa sukuni ya kasa fitar da dzija a ranshi. Me ke faruwa danine me zuciyata ke son janyo min tambayoyin da y a kasa ansawa kanshi kenan shi rabon da yaji irin feelings din nan tun zamanin farkon soyayyar sa da najma, ya na mutukar son matarshi asali tsananin son da yake mata ya sa ya kasa kara aure kaman yanda mahaifinshi ya buqata bayan wannan akwai tsananin kishi a tattare da najma da yake sa mishi fargaban kara aure. Ya sani matarshi macece me kirki amma akanshi tana da tsanani baya manta zamanin da suke karatu ko da course mate dinshi ta ganshi wani masifa ne. To amma ya ya iya da abin da zuciyarshi ta jijibo mishi, murmushi yayi tunawa da yayi iyayenshi zasu goya mishi baya da auran lumshe idonshi yayi a haka ya fada toilet Dan dauro alaula yayi nafila.
***** ***** *****
Satinsu laure biyu a US an samo mata lesson teacher da take koyar da ita alhamdulillah tana ganewa duk da dai ba wai tana jin turanci bane amma cikin ikon Allah ta kan fahimceta. Haka rayuwa ta cigaban musu watan su shida ta shiga middle school kasancewar tana ganewa sosai bata kula kowa abin da ya kaita shi take yi ,haka fannin Islam tana zuwa Islamic school kuma momynta kamar yanda take kiran haj salma da shi tana koyar da ita a gida rayuwarsu dai gwanin sha'awa.
***** ****** ******
Bangaren ummi dija kuma wata rana tana zaune kan darduma tana lazimi jakadiya tazo ta tisa keyarta ta fita da ita sai gidan tsohonsarki kasancewar duk a estate daya suke abin ya ba ummi mamaki sosai yanda ta ga hajja mahaifiyar memartaba ta karbeta ta sa aka shiga da ita wani kayataccen daki aka kawo mata abinci kala kala ga suturu an wadatata da shi da Ido kawai take kowa, sosai abin ke ba ta mamaki daga baya tayi tunanin suna tausaya mata ne sbd batar er ta.
Zama tayi na wata 3 cur a gidan bata aikin komi sai dai tayi wanka ta sa tsadadun kaya taci me kyau tayi ibada da karatun ta kasancewarta me wadatacen ilimin addini tuni kyanta da yarintarta suka kara fitowa ga wani irin shakuwa da tayi da hajja ita take mata lalle kitso da yankan farce sosai hajja ke Sonta tana kuma dada yabawa da hankalinta hatta girkin lamido ita take yi hakan yasa suka yanke shawaran daukan next step.
***** ****** ******
INA LABARIN NAJEEB?
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA💖

By sawwama ameen
Page9

Note banda yammata, matan aure zalla please

Yau sati biyu kenan da batan laure a yaune kuma me martaba ya bukaci ganin ummi dija tsaf ta shirya duk da ta rame sosai hakan be hana kyawunta fitowa ba idanunta sun canja launi daga farare tas zuwa ja ja ja sun kuma kankance sbd yawan kukan da take yi ta rasa ina za ta sa kanta taji sanyi laure ce kadai dangin da ta rage mata tunda yan uwansu sun wofintar da su tun daga auran margayiya laure ita ba don tana tsoron kar en rugarsu su tuhumeta ina laure ba da ta koma zuwa birni be tsinana mata komi ba ada tana mutukar farin ciki da zuwansu kasancewar tana ganin laure zata samu kyakyawa rayuwa da ilimi ingantace to ashe ba haka abin yake ba.
Jakadiya ce tayi mata jagora zuwa wurin shakatawar me martaba,zaune yake kan kujerarsa borori da fadawa suna ta aikinsu.
Sarki sa'eed na dagowa dan yaga mahaifiyar wannan yarinya da akace ta bata dammmm yaji wata muguwar faduwar gaba ganin er matshiyar yarinya da akace itace mahaifiyar yarinya er shekara goma. Da kyar ya daidaita kanshi yayi gyaran murya cikin kasaita ya nemi da ta gaya mishi dangantakar ta da yarinya ya kuma bukaci ya san mahaifin yarinyan hawayene ya silalo a kumatunta dan ita yanxu ta tsinke da lamarin laure. Cikin nutsuwa da dauriya ta dan takaita mishi lbrnsu.
Ya tausaya mata sosai ya kuma tabbatar mata da insha Allahu zai zage damtse a wajen neman laure kuma zai cigaba da tallafa musu. A haka ya sallame ta ta koma sashinsu ta cigaba da sana'ar ta ta wato kuka da nafila.
***** ***** *****
Ko da su cptn suka isa abj sai da laure ta kwashe kwana uku bata farfado ba tana dai samun kulawa a gida daga babban doc din asibitn da haj salma ke aiki ya tabbaatar musu in ta farka zata iya tuna komi za kuma ta iya mantawa na dan waniblokaci kasancewar ta firgita sosai,haka ko akayi bayan ta farfado sunyi iya yinsu ta tuna wani abu da ya danganceta sun ta kiran sunanta kasancewar ta fada musu tun farfadowanta na farko amma sai dai ta bisu da ido karshe ma kuka ta fashe musu da shi hakan yasa suka kyaleta suka fara mata shiryeshiryen tafiya .
Laurat Muhd aka mata passport da shi hikimar alh sa'ad na yin haka shine ko ma waye mahaifinta ba mamaki sunanshi is link with muhd kuma koma ba haka ba muhd sunan manzon mu ne.
Monday da dare jirginsu ya daga sai dai muce Allah ya sauke su lafiya.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA 💖

By sawwama ameen

Page11

Russia kuma najeeb ke kwance akan doguwar kujere yana kallon sama faruq ne ya shigo Palon yana mishi magana amma sai ya lura sam hankalinshi baya tare da shi taping dinshi yayi tare da kiran sunanshi a Dan razane ya tashi ya sauna ya tallafe kansa da tafukan hannunsa tare da lumshe ido faruq ne ya zauna kusa da shi ya dafa shi sannan yace frnd don't tell me is about that gal numfashi ya ja sannan ya fesar a hankali ya kalli faruq da yace gosh she keeps hunting my thoughts and dreams frnd I really regrets wat I did to her amma she won't let me be kai ka fi kowa sanin ba halina bane I don't know what came over to me that day dole in nemi yafiyarta ko zata daina bibiyana cike da kulawa faruq yace ba ita ke bibiyarka abin da kayine yake bibiyarka well alhamdulillah tunda u want to repent ur mistake duk randa muka koma sai ka nemi gafararta yace inshaa Allah hopely dai tana zuwa talla har lokacin da zamu koma kasan fulani da auran wuri faruq yayi murmushi yace kar ka damu tana cikin masarauta zaro ido😳najeeb yayi yace huh? How ? Me kake fada min tana gidanmu yace eh wow u are genius my frnd kana da kyakyawar zuciya Allah ya baka lada and nima u made things easier for me dariya sosai faruq yayi yana mamakin yarima wai zai ba er karamar yarinyan nan hkr wow Allah kenan Dan ya tsokane shi sai yace hmm the whole mighty prince wants to apologize to a toddler hahhahahaha🤣🤣🤣 pillow din kujera yariman ya dauka ya jefe shi da shi yana dariya ammi ce ta shigo tace ho ni falmata yara sun girma ba su San sun girma ba yanxu in kannenku ne suka shigo fa karab najieeb yace ammi sai muyi da su tace ku din? Lallai faruq ne yace oh su ammi an dage sai shiri ake za a tafi a barmu mu zama marayu dariya tayi tace zaku gane vaku da wayone yara hahhahahh😂dariya suka yi dukka najeeb yace kai ammi ko tausayinmu ba kyaji sai doki kike tace gidanku ai dai ban kai abi dinku ba ko danshi yana da babban dalili suka ce haka ne.
****** ***** ****-
Lamido ne da hajja suka sa dija a gaba lamido ne yayi gyaran murya yace khadija na San kin dade da tambayoyi fal a zuciyanki amma sbd tsananin biyayyanki ko da sau daya baki tana tambayan hajja ba da farko muna baki hkr akan batar er yar uwarki khadija wani alfarma muke so mu nema a wajenki bayan hannunta tasa ta share hawayen da ya zubo mata tace Allah ya Kara girma ku masu iko da nine ba wani Abu da zaku iya nema a wajena da ba zan iya muku ba asali ma nafi son kuce min kun yanke hukunci Abu kaza zai fi min sauki da ku nemi alfarma a wajena. Alhamdulillah shine abin da ke fitowa daga bakin lamido yace tashi kije Allah ya miki albarka ita da hajja suka amsa da amin.
Da dare mai martaba ne da haj najwa suka so kasancewar lamido ya nemi ganin haj najwa. Sosai ya musu nasiha Kafin ya sanar da haj najwa ya yanke zai yiwa maimartaba aure kuka take sosai suka bar gidan ba tacewa maimartaba komi ba har yana murnan plan dinshi yayi sai da yaji tana waya da airline akan tana son first class sit zuwa India wato za ta koma kasarsu kenan.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA. 💖

By Sawwama Ameen.

Page 11
Goran Sallah
Taqabbal minna wamin kum ina mana barka da sallah da fatan Allah (SWT) ya karbi ibadun mu ya sa muna cikin 'yantatun bayi.
Ina me baku hkr akan rashin typing akan lokaci inshaa Allahu za a gyara.

Wannan shafin naku ne sadaukarwarku ce members na Novel,make up and kitchen by admin of admins YAYA HAYAT. Allah ya barmu tare, Amin
Chapter 3 · 0% Book details