← Book details Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Masoyan Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najeeb dake tsaye a bakin kofa yana kallon duk abin da ke faruwa sai yaji ta burgeshi bata daukan raini what a confidence abin da yace a ranshi kenankhalisat ce ta iso inda yake tana kuka tace amma yanzu big bro kana kallon wulakancin da yarinyan nan ta min baka yi komi ba ya lumshe ido yace toh me zanyi ke kika so wulakantata ita kuma ta riga ki lets go inside muyi wata magana.

Ko da suka shiga suka zauna yace lil sis na dade ina so mu samu daman nan ban samu ba sai yau khaleesat me aunty khadeeja ta taba miki bayan auran mahaifinmu da tayi tace babu banda kishi da take yi da mah din mu yace dake take kishi ko da mah ita sa'arki ce ina ruwanki da shiga abinsu na manya kin manta kema macece zakiyi aure a wani gidan maybe gidan sarauta mai dumbin zuriya ya zakiji in daya daga cikin zuriyar ta rainaki??? Jikinta yayi sanyi hakan da ya gani ya bashi damar cigaba dayi mata nasiha da nuna mata illolin halin da take yi kuka take shabe shabe tana neman gafararsa yace ni me kika min wadanda kika hurting zaki nemi yafiyar su bayan na Allah tace toh ka rakani pls ina jin kunya murmushi yayi yace ok toh muje.

Tana shiga side dinsu aunty ta rufeta da masifan ina ta shiga sama da awa 2 tana nemanta ta kira wayarta bata dauka ba ta dan turo baki tace aunty fa wayar na silent ne banji ba amma ina cikin gidan nan face toh dai ki kiyaye lauratu ban son kina nisa dani ina tsoron in kuma rasaki sai jikinta yayi sanyi tace aunty kar ki damj zan kiyaye barin canza kayan nan laptop nake buqata gashi ban san ko'ina a garin nan ba tana tafe tana magana taje ta canza ta sa gown ta fiti tana cewa aunty yamzu aunty ya za ayi ko driver zan nema turus tayi dan ganin aunty da su najeeb khalisat na tsugune tana kuka tana rokanta aunty tace ba damuwa taso diyata allah ya yafe mana gaba daya shigowar laura palon yasa khaleesat karasowa ta rumgume ta tana fadin sister dan Allah kiyi hkr da abin da ya faru dazu ta dan yi murmushi ba komi ni ya kamata in baki hkr amma yanxu dai let bygone be bygone suka yiwa juna .

Aunty tayi murmushi tace toh masha Allah,Allah ya kara hade kanku suka ce amin tace lauratu banji kin gaishe da yarimanmu ba ta dan tura baki ciki ciki tace ina wuni ya limshe ido kafin ya ansa da lafiya aunty tace Allah ya kyata batun fitarki kuma ga yan gari nan tayi wucewarta ta barsu khalisat tace sister ina zaki je kai ta dan sosa kafin tace wallahi laptop nake so in siyo ban da shi and i need one khalisat ta juya ta kalli yayanta tace yaya muzo muje hada rai yayi yace ah ah ina da aikin da zanyi ki nemi driver marairaice fuska tayi tace yaya plssss tashi yayi ya fita ba tare da yace musu komi ba tabe baki laura tayi ita dama bata nema ba don dai kar ya zama ta gwasale khaleesat ne yasa tayi shiru khaleesat tace ohhhhh na so ya kaimu dan shi bai cika son fita da guards nima haushi suke bani amma yanzu bamu da yanda zamu yi are u ready laura tayi murmushi tace alway suka yi dariya gaba daya.

Bangaren Najeeb kuma abinda yasa yaki kaisu baya son abinda zai kusanta shi da laura ne dan ba karamin dimautashi take ba ita laurat dai ba faa bace chocolate kala ce bata da tsowo bata kuma gajarta wato average height ce bta jiki siririya ce tana da nonuwa ma daidaita basu cika girma ba basu yi kanana ba a tsayae suke cak kaman an dasa su bangaren hips kuma hips dinta madaidaita ne amma sai tudun duwawu gashinta natural coil ne wato kanannade suke irin kaman an tsafe kitso din nan ita haka nata yake naturally kuma shoulder length ne wato dai dai kafadarta ta fanni fuska tana da ido madaidaita su ba manya ba sannan kuma ba kanana ba hancinta bai cika tsawo ba tana da dan karamin baki da take yawan turoshi karshen haduwa dai ta hadu dai dai ita wannan dalilin ke saka najeeb baya son kallonta sosai dan tunaninta begenta da sha'awarsa hana shi sukuni suke su hana shi bacci yau kam nace bacci ai bai ga idonshi ba tunda ya ganta kusan tsirara.lol
[7/17, 06:27] YAYA HAYAT: 💖MASOYAN JUNA. 💖

By Sawwama Ameen.

Page 23.

Laure ta mayar da pool din Najeeb tamkar nata duk da bata san mamallakin wajen ba,da zarar ta bushi iskanta zata saka bikini dinta ta daura after dress mai kauri taje ta sha wankanta tun aunty na bincikan inda take shiga har ta hakura ta kyaleta dan ta san dai tana cikin masarautar.

Haka Najeeb ya san lokutan zuwanta wajen dan ya tambayi masu tsaron wajen suka gaya mishi in har yana gari toh yana bedroom dinshi na sama yana lekenta farooq har mamakin yawan hawanshi sama yake don bai cika son saman ba amma sai ya danganta hakan da kadaici da kuma rashij sanin takamamen inda astral dinshi take hakan yasa ko da yaushe yake kwantar mishi da hankali da kuma tabbatar mishi da inshaa Allah zai ganta harma ya aureta.

Magana tsakanin farooq da lauratayi nisa har iyaye na shirin shiga ciki. A halin da ake ciki yau ake sa ran zuwan mahaifin farooq Alh auwal da abokinsa sai wan mahaifiyar farooq da kaninta .

Ana ta shirye shiryen tarbansu anyi girke girke kala kala bayan sunci sun sha memartaba ya bude taron da addua sannan ya dora da cewa alh auwal ranan wanka ba a boye cibi duk da na san mu ba bakin juna bane na san bazaka rasa sanin ba nine mahaifin lauratu ba nan dai ya kwashe labarinsu ya fada musu gumi ne sosai ya wanke Alh auwal da alh sa'ad kanin mahaifiyar farooq duk da a c din da ke palonsauran yan palon sai jimamin tausayawa yarinyan suke alh auwal yace ran kai dade menene kace sunan ita wannan yarinya da kanwar mahaifiyarta memaryaba yace khadija yarinya kuma lauratu alh auwal yace dija da diyata laure ba shakka kowa sai ya maida hankalinsa kan alh auwal cike da mamaki.....

Maimartaba ne yayi karfin halin cewa alh auwal me kake nufi alh auwal ya dan ja dogon numfashi kafin ya basu labarin zamanshi da su margayiya laure lokacin da yan boko haram suka tarwatsa su me martaba yace shakka babu lauratu diyarka ce amma bari in kira ita khadijan da yarinyan nan ne alh sa'ad yace nima labarin yarinyan yayi dai dai da na yarinyan da na tsinta shekaru goma da suka wuce shima ya basu mamaki kowa ya cika da mamakin wannan ikon Allah nan take memartaba ya dau waya ya kirawosu .

Sallamu suka yi suka shigo palon ko wacce a cikinsu sai ta daskare hade da zaro ido laura ce tayi wani murmushi sannan tace DADDY da gudu ta nufe shi alh auwal da ya tsaya kallon ikon Allah yana mamakin irin kamannin da laura tayi da mahaifiyarta laure sai dai mahaifiyarta fara ce sol yaji ta ambaci daddy kuma ta nufo su da gudu dai yayi zaton da shi take ya manta alh sa'ad yace ya santa kawai sai ganin yayi ta shige jikinshi tana murna................

yace sweetheart u are alive muna ce kin mutu da muka ga motanki a kone what happen ta goge hawayen da ya zubo mata tace nothing dad just wanted to come back sosai yaji tausayinta ganin yanda ta boye abin da momynta ta sgmhirya mata mai martaba ne yayi gyaran murya hankalinsu ya dawo jikinsu sai kuma kunya ya kamata da taga mutane a palon ashe fa neman auranta aka zo har i zuwa lokacin khadija na tsaye kaman an dasa ta sai da alh auwal ya karasa inda take tsaye yace dije tabbas nine lawal hawaye na gangaro mishi ai basu ankara ba ta sulale ta fadi me martaba ya san za a rina dan akwaita da firgicewa ruwan sanyi aka yayyafa mata taja numfashi ta farfado ta nuna shi da yatsa tace moddibo kana raye ka manta da batun mu ka manta da yarka yar da ka haifa haba sai ta fashe da kuka laura ce ta fara ja da baya tana fadin no no no this cant be mahaifina ni ya mutu ni marainiya ce banda wani uban da ya wuce wannan ta nuna ahl saad alh auwal na kuka ya durkusa a gaban su yace saurara kuji a lokacin da mahaifiyarki ta rasu bayan haihuwar ki nayi matuqar bakin ciki duk da ba ita bace matata ta farki nayi kuka nayi kuka nayi da na sanin barinta da cikinki a nawa wautan da bata haifeki ba da bata rasu ba hakan yasa nayi fushi na tafi ban kara waiwayenku ba hakan kuma yana da nasaba da barina kasar sai da aka kusan shekaru goma na gane ban muku adalci ba daga lokacin na wakilta dan uwanki umar ya fara nemanku amma ba labarinku da kaina naje ruganku akace ba sma san inda kuka shiga ba nayi kuka nayi nadama na dora laifin dukka akaina da ban kula da ku ba Allah shaida farooq shaida hakan yayi dai dai da shigowar farooq din da najeeb da saukarsu kenan a garin subhanallahi me ke faru abinda suka furta a tare kenan suka karaso ciki nan suka samu labari me rikitar da kwakwalwa wai laura kanwar farooq ce ta jini haba shi yasa yake jin kaunarta a ranshi yana ce soyayya ce ta aure haka dai aka yi farin ciki aka bawa juna hakuri .

Alh auwal yace to baza fa mu fasa abinda muka zo ba wato neman auran laura a wajenka kai mai martaba ina nemawa dana Najeebullah auran diyarka Lauratu.
Chapter 10 · 0% Book details