Sashe 6
Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tausayin danta ne ya lullube mama tace kayi hakuri babana nasan komai,ka dage da addua Allah zai ma canji mafi alkhairi,Allah zai baka wacce kake so take sonka,kaci gaba da biyayya.muje kayi breakfast,bayan yayi break ya wuce office,tunani yakeyi a office ya zai yi ya kara ganin wannan yarinyar me talla.idi driver ya kira ya karbi key din motar so yakeyi yayi driving da kansa yau,bai so asan ina zaije.
Sadiya da Aisha ne suke hirar samarinsu,Aisha tace anty sadiya ya kamata kiyi aure haka karfa ki tsufa,tsaki sadiya ta ja dalla yanzu kudi da kayan gyaran jiki basa bari ka tsufa,yanzu duk wacce ta bari ta tsufa to ta rako mata duniya,samarin nawa gaskia naga basu da kudin danake bukata gwara ma wani alhaji Adam shi kuma yana da mata daya,bai taba haihuwa ba,Aisha tace ni a ganina ki fito dashi guy din akwai kudi,kina aikinki kinga zaki huta,kuma gidanki ke daya zai Gina miki,ga aikin gomnatinki heeeeee suka rangada shewa suka tafa,sadiya tace haka za ayi yar gari,kefa Aisha ?tace aini kin San wa zan tsayar,yaseen zan tsayar a turai yayi rayuwarsa ga kudi ga wayewa.haka sauran matan gidan ma suka shigo sai hira sukeyi.
Iklas kuwa dawowarta kenan daga schl,sallah tayi taci abinci daga nan ummi har ta dafa mata kwai kawai tallanta ta dauka ta tafi gefen titi.shi kuwa omar 11am yaje wurin da yaga iklas na tsayawa talla amma shuru bai ganta ba,ba jiran da baiyi ba bai ganta ba,motar sa ya parker ya kira wani yaro me talla ya kwatanta masa yanayin iklas yaron yace ohhhh gomnati kake nufi,yeah ita cewar omar,yaron yace ai yanzu tana schl sai 1to1:30 take zuwa nan tallanta,take omar ya tuno time din da suka ganta jiya,
Kudi ya bawa yaron ya hau mota ya koma office,1pm dai dai ya sake dawowa wajen danjar da iklas ke talla,nan ma bai ganta ba,shi kadai yake Jan tsaki,can ya hangota ta fito daga wani lalataccen lungu,dakyar take daga kafarta sabo da nauyin kayan,botikin kwai a kanta ledar apple a hannun ta,Tausayinta yaji sosai kamar yayi mata hawaye,yana cikin motarsa yana kare mata kallo,yana kallonta har ta fara talla,omar ne ya daga waya ya kira wani ban San me yace ba,ba a kai 10mnt ba wani ya parker a mota dai dai wajen kayan iklas,cewa yayi yana son apples da eggs amma duka zai saye mata,juye zai mata,da murnarta ta siyar masa gaba daya,yana tafiya ta kara irga kudin sai taga ya mata Karin dubu biyar akan kudin,dubu biyar din kai ta cire ta boyesu daban,da niyar in ta kara ganinsa zata bashi abinsa in bata ganshi ba zata yi masa sadaka dasu.
Tsalle tayi tana dariar farin ciki an siye mata du,baki har kunne tace kai ni me sa'a ce,duk abinda takeyi omar na mota a gefe yana kallonta har ta tafi gida,shima yaja motarsa ya koma office,amma ya rasa dalilin da yasa yake jin nishadi yau.tunda yaga gomnati yaji damuarsa ta gama yayewa.hajiya rahina sun shirya cewar baza su fara makirci ba sai alhaji Baban su omar ya dawo gida Nigeria.Washe gari karfe 1 na rana omar yana gefen titi a wata kalar motar tasa,yana jiran fitowar iklas daga layinsu da yaga ta fito jiya.
Asmahbaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
7
By
Asmahbaffa
Yana zaune a motarsa yana shan a.c ta fito dauke da botikin kwanta yau yaga ba ledar apple a ransa yace to ko ta kare ne apple din tata?baki ya tabe hade da daga kafada.ta karasa danja tana tallanta,omar ya kunna motarsa ya hau kan titi yana zuwa saitin iklas ya gangare gefe yayi slow da motar,batasan waye ciki ba ta famfaro da Sauri sauri gudu gudu ta kara masa ledar kwai a glass na window side nasa,glass din ya sauke kasa wani kamshi da sanyin raba ya bigeta,ba tare da ta shirya ba ta kalli cikin motar,oga ta gani a mazaunin driver,lekawa tayi da murmushi sannu oga yau ma kazo wucewa?bai amsa mata ba kuma fuskarsa a tamke take,sai ya nuna kamar bai taba ganinta ba,kunya taji na disgata da yayi,a sanyaye ta juya zata wuce,keee cikin kakkausar murya ya kirata,juyowa tayi itama ta tamke fuska,ya akayi cewar iklas,a ransa yace wai ni zata wa tsawa haka hmm.a fili yace wai baki da wata Sana'a sai wannan?kullum kina gudu a titi cikin maza,kuma bakya sa kayan arziki na musulunci,duk maza an gama kalleki.
Kallonsa tayi ta watsa masa harara to ina ruwanka,ina ruwan biri da gada,taso ta watsa masa bakaken maganganu wanda suka take wannan amma kwarjini da cikar zatinsa baza su bari ta fada masa ba oga omar ba kalar raini bane,Sam fuskarsa baya fara'a baka isa ka rainashi ba,in banda ma iklas ta goge da mutane da word daya baza ta iya furtawa gabansa ba,amma gashi har tsiwa take masa,a hankali tayi maganar amma ita wai nan a dole masifa tayi masa,sai ka zata hira me dadi sukeyi,shi omar daria ma ta bashi,a fili yace hey chill yan mata,I don't mean to hurt u,tambayarki nayi fa kuma dole ki fada min,lallai zaka Dade a tasha baka samu mota ba,murmushi yayi jin kalar Karin maganarta to naji next time zan dawo zo ki bani na siyi kwan naki,lallabata yayi don yasan gomnati akwai tsiwa,ya fahimci akwai son a girmamata,yauma duka ya siye mata kwanta tana tafiya ya bita a baya a mota ba tare da ta sani ba,har gidansu yaga gidan da ta shiga,juyawa yayi ya koma office cike da mamakin lalacewar gida irin nasu gomnati,da gani suna wani hali.
Tun daga wannan rana iklas bata kara ganin omar yazo ba,tayi tunanin ko fushi yayi kan maganar da ta fada masa,ita da kanta ta gano bata kyauta ba,tunani ya hanata sakat kan maganar da ta fadawa oga omar,ta zama butulu ta manta halaccin da yayi mata,tun damuwarta na boyewa har ta fito fili,yau Saturday tayi jugum tana tunani kaka ummi ta leko dakin,ke yar nan ki raba kanki da wannan bakin tunani da kika dorawa kanki kwana nan,na rasa gane miki,alhmdllh muna ci muna sha,ga makaranta kunayi dai dai gwargwado Allah ya hore mana amma sai tunanin banza kikeyi,ummi wlh lailatul qadarin dana fada miki me gidan kaji?ae ina jinki iklas..to ummi shine ya tambayeni kan Sana'a ta amma na manta alkhairin da yayi min da yawa na masa rashin kunya,to har yau ban kara ganinsa ba,fatana ma ace lfy yake.ummi wlh baki ganshi ba me kyau dan gayu,ya fini kyau fa,kuma ga iya wanka ummi,sai ma kinga murmushinsa.
Kaka ummi ce ta rafka salati lailahaillallahu ni kam naga ta kaina,iklas karfa aljanu su shigeki,ko dai sonsa kikeyi ne,dama tunda naji kin saurareshi har ya miki kyauta kin karba nasan da wata a kasa,ke da bakya karbar kyautar namiji,kullum kice suna baki ne dan su lalata miki kuruciya, gashi wannan har murna da ihu kika dinga yi,duk ranar da kika ganshi sai kin hanamu bacci da labarinsa.akan wannan har kika damu kanki tab,ai sai ki tayi aiki ya ganki,
Baki ta cuno kaka ba haka bane bafa,haba ummi ke bakya ganewa,nawa nake kwata kwata da zan San wani so.rankwashi ummi ta zuba mata tashi sha sha sha ki mana girkin dare wlh iklas ki kiyayeni.kara ta saki ochch haba ummi zaki sani ciwon kai.
Shi kuwa Omar tun bayan da ya siyi kwai a titi ya tsaya ya rabawa almajirai ya dauki daya ciki yaci,tunani yakeyi ta ya zai San tarihin yarinyar nan,har yasan wanne irin taimako zai mata,baya son ya bata kudi sabo da gudun kar ta yi masa mummunar fassara, tausayinta yakeji ya rasa dalili.
Baffan su Omar ne ya sanarwa iyalansa zai dawo nan da 2wks,su haj rahina sai murna Sukeyi burunsu ya kusa cika,kamar kullum yau omar yana gidansa a Palo yana cike ciken takaddu,sahar ce ta karaso wajensa tana zuba wani matsiyacin kamshi,ga wata Shiga da tayi ta alfarma kamar zata cin gasa.zama tayi kusa dashi,shafa fuskarsa ta Shigayi,yana dagowa ya kwadawa sahar mari lafiyayye,idonsa yayi jajir u r very stupid,me kika daukeni wawa ko me,duk abinda kikeyi ina kallonki kyaleki nakeyi sabo da biyayyar mahaifina.
Dafe da kunci sahar tace what omar in ka sa hannu a lafiyayyar fuskata ka Mara,wlh sai kayi dana sani,sai kasan ka mari mai girma sahar, kuma bari na fada ma duk dunia babu namijin da ya isa na masa biyayya dan yana mijina,sabo da ina da komai na kudi,babu abinda zan nema wajen wani.
Dama sallama nazo yima zan tafi kano wata seminar sai nan da 1wk zan dawo fuuuuuuu ta dauki trolley dinta tayi gaba tsaki Omar ya ja,har airport driver ya kaita ta hau jirgi sai kano.
Omar kuwa wanka ya fesa yau Wednesday bai je office ba sabo da akwai inda yake son zuwa, cikin shigar wata rantsatsiyar farar shadda kal ya fito,dinkin zamani kamar a jikinsa aka dinka,ga sumarsa ta kara yawa luf da ita yana shining, komai fari yasa agogo ma na azurfa ne,
Yau ma bai gayyaci driver ba,wata shegiyar farar mota ya shiga,su Kansu ma'aikatan gidan omar cewa suke oga yana kashe kala a garin abuja,oga na tsiya a kasar nan.
Layin 1:40pm ya parker motarsa kofar gidan su iklas,kowa dake layin kallon motar akeyi,ko waye zai wuce sai yabi motar da kallo.yana cikin tunanin yaron da zai aika gidan sai ga suhaila cikin uniform ta dawo daga schl,kallon yarinyar yayi tabbas wannan kanwar gomnati ce,sunyi kama sai dai gomnati ta fita hasken fata duk da itama suhaila farar ce,motar ya bude yace pls young girl?da sauri ta juyo sai kallon dan gayu takeyi,nan ne gidan su gomnati?yeah nan ne cewar suhaila,pls ki min sallama da dadynku,daria tayi ai mu bamu da dady uncle,ok umma fa,kai uncle ba ummanmu bace tare da kakarmu muke zama mu 3.OK good girl yi min sallama da kakar taku to.OK ta shige gida da gudu,Minti kadan sai ga kaka ummi ta leko sanye da wata tsohuwar atamfarta,da wani yankwanannen gyale amma fa kar kar suke ,omar tunda yaga suhaila da kaka ya tabbatar gidan masu tsafta ne.