← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 57

Sashe 23

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iklas da gudu ta karasa wajen Omar tare da fadawa jikinsa tayi lamo a kirjinsa shi kuwa ya kankameta a jikinsa,hannuwanta tasa tare da tallafo kumatunsa tana Sir sannu ya Omar ciwon nan ya baka wahala,Iklas ina ta Neman ki su Mama basa tausayina,no ya Omar sunfi kowa tausayinka fa,riko hannunsa tayi zo muje na baka abinci juyowa sukayi sai sannan Iklas ta tuna da mutane a wurin kunya taji zata zame hannunta daga na Omar taji ya kara damkeshi rada ya mata a kunne muje ni wlh yunwa nakeji.

Su kuwa su Mama Murna da Mamaki sukeyi ganin Omar na Rike Iklas ya warke ya dawo sumul Mutum kamar kowa.Sultan ne yayiwa Iklas Magana ya kika tsaya kuma kuje ciki gamu nan zuwa,ki kaishi part dinsa akwai komai ciki har abinci an kai.

Asmabaffa

[31/03, 17:52] Nabila maishanu Fbk Gusau Zamfara: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GIMNATI
ⓂⓂⓂ

75-80

By
Asmabaffa

WANNAN SHAFIN NAKUNE MASOYANA.

Rike yake da hannunta har suka shiga part din Omar.Su sadiya wani uban tsaki suka ja Ashe shegiyar marar kunyar yarinyar nan ce take wannan iyayayin da shishigi, Aisha tace haba no wonder ina ganinta naji na tsaneta Ashe yar bakin gida ce wlh sai tayi dana sanin zuwa gidan nan.
Part dinsu suka koma kowa na fadin kalar nata muguntar da zasuyiwa Iklas.har palonsa Iklas ta kaishi dole tare suka zauna kamar chewgum haka ta zuba masa abinci ya tsaya yaci sosai da yawa sai da yajishi dam sannan ya Kali Iklas ina Ummi da Suhaila yanzu zasu shigo Good yace.

Yana son ya saki hannun Iklas Gudun kar Mama ta ganshi yana jin kunya gata ita ba matarsa ba,yana wannan tunani su Mama suka shigo gaba dayansu,suna masa sannu,mamakin Omar yaga Sam su Ummi basu damu ba da suka ganshi rike da Iklas.
Baffa ne ya shigo tare da malamin nan kowa waje ya samu ya zauna,Malam Usman ya kalli Baffa yace Alhmdllh mun godewa Allah lallai Allah da iko yake,dama Baffa ya sanarwa Malam usman batun auren da sukayiwa Omar yaji dadi shima malamin yace dakyau kar a sanarwa kowa yanzu tukun a bari ya warke. yanzu wannan yarinyar dole ta zauna kusa dashi har ya gama shan ruwan adduarsa Wanda a kalla na 3wks ne,a dakinsa zata dinga kwana dashi har agama komai,Omar kansa ya kulle sabo da cuta za a sabawa Allah su kwana 1room da wata.

Kallon Baffa yayi Baffa kwana 1room da itafa haramunne za a sabawa Allah,karka damu Umaru ba abinda zai faru mun yarda daku,ta lafiyarka mukeyi cewar Ummi.
Shuru Omar yayi zuciyarsa cike da tsoro,kwalayen ruwan faro aka shigo dasu na addua,dama malamin yanda sukeyi Ku zaku kawo ruwan roba carton din dasu ke addua ciki su Baku abunku a tsaftace ba shan cuta,Omar ma su Baffa kwali biyu suka kai na faro,sai kudin su za a basu masu tsada domin dubu Dari da hamsin malam usman ke yi ba ragi.

Bayanin maganin ya fara musu a bashi yasha da safe Rabin jarka ragowar Rabin kuma da dare ya zauna a kan towel a shafe masa shi a jiki gaba daya,ga wannan ya mika musu man zaitun shima an Masa addua ciki kullum a shafa masa da dare a jikinsa,yau Ku fara bashi su.kome ake ciki Alh kamin waya..Godiya sukayi Masa ya mike ya tafi.
Sultan da Raj ma jaddadawa Iklas sukayi kan ta kular musu da abokinsu sannan suka tafi gida,tuni su Suhaila sunyi bacci,Mama yau har hira kadan sukayi da Omar ammafa har yau rike yake da hannun Iklas,hannunta yayi gumi ya gaji.

Baffa ma jaddawa Iklas yayi cewar ta kula da Omar ta Saki jiki ba kunya.sanna suka wuce part dinsu ita da Baffa,Ummi ma tayi nata sannan ta tafi,shi kam Omar tunani yake wai meke damun su Mama zasu hadashi daki daya da balagaggiya
Kallon Iklas yayi yaga ita Sam ko a jikinta,harkarta takeyi tana latsa waya.kina jin fa su Mama wai ki kwana Room dina,ba tare da ta kalleshi ba tace to ya na iya?me zan yi ciki lfy fa za a nema maka.muje ciki kayi wanka ,fuska ya daure in sa'ankine zaki dinga sani abu wai?ko na miki kama da yaronki?lallai ka samu lfy sir ,muje pls ni bacci nakeji gwara ma ka taso,ni dai yarinya baki isa kin hau bed dina ba wlh,ba dan iska bane ni.

Murmushi Iklas tayi to badan tsoro ba ka sakar min hannu mana yanzu a gani,baza a saki ba din,to kaga kuwa ai Kaine babban......sai ta tuna Oga ne fa wannan da sauri ta kulle bakin ta,saukar wasu rankwashi taji kwas masu zafi a kanta Omar ya zuba mata,
Ouchshsh.....tayi kara tana Sosa kai,shice da shagwaba tace da zafifa zaka kasa kwakwalwata ta hadu da jini.
Mikewa yayi rike da hannunta suka shiga Room dinsa,sakin hannunta yayi ya shiga toilet da kyar yayi wanka saboda ciwon ya tashi,kafin ya fito ta dauko kayan baccinsa tana ta sauri ya fito kar ciwon yayi karfi,
Ai kuwa a wahale ya fito da sauri ta matsa kusa dashi ta rike hannunsa sai dayaji ya dawo normal ya kwace hannun ke nifa kina yawan sani aikata sabo kin dameni fuska daure yayi maganar,
Fushi Iklas tayi ta mike fuuu ta dauko maganinsa da malamin ya kawo,to ko shima wannan din baza ka sha ba,ae bazan sha ba kije kira min Mama, fita tayi direct part din Mama taje kofa ta kwankwasa Mama ta fito Iklas lfy? Wlh Mama Ku fada masa ni matarsa ce yaki yarda ma yasha maganin komai fada yake min wai iskanci ne,kalla inda ya rankwasheni fa Mama,

Kuma yace kije wai, murmushi mama tayi rigimamme ke kuma in banda abinki hakuri akeyi ai da marar lfy kuma kin San bai San matarsa bace ke,ni bazanje ba babu abinda zan masa kece me yin duk abinda ya dace kuma mun koya miki komai sabo da haka kije kowa yaji da mijinsa,nauyi ne kanki kije ki kula da mijinki.

Jeki Allah tashe mu lfy,komawa iklas tayi itafa an takura mata an lakaba mata aure.komawa tayi ta sameshi ciwo ya tashi gadon tahau ko kulashi batayi ba ta dauko addua ruwan faro ta tsiyaya a glass cup ta mikar dashi zaune da yake ciwon na cinsa karba yayi ya sha,ta kara bashi sai da ya sha rabi kamar yanda malam yace sannan ta dauko zaitun nan ma da kyar ya bari ta shafa masa yana ta lumshe ido sabo da dadin yanda take shafa masa kamar kar ta daina,sai mamaki yakeyi yarinya karama da abun mamaki,kato dashi take iya kula dashi haka,rigar ta dakko zata sa masa ya bige hannunta kin ma isa ke wai ni danki ne?mikewa tayi ta koma wata hadaddiyar kujera ta hutu ta kwanta,badai haka zaki kwana ba? kazama kije kiyi wanka,itakam ta gaji mikewa tayi tayi wankanta ta fito sanye da kayan jikinta,kije ki dauko kaya mana,mikewa tayi ga mamakin Omar yaga ta bude sip dinsa ta dauko farar jallabiyarsa ta koma toilet ta fito sanye da ita a jikinta,tayi kyau sosai.shanya waccan kayan tayi a toilet dinsa,fresh milk ta tsiyayo ta bawa Omar a baki ta sha itama suka kora ruwa tayi kwanciyarta,shi kuwa Omar ciwonsa yakeji,sai masifu yake karba

Iklas tuni tayi nisa a bacci bata San me yake ciki ba,karfe daya na dare nishin Omar ya tasheta da gudu ta haura kan bed din yau ciwon na Omar ya banbanta da Wanda yakeyi wannan nishi kawai yake fitarwa da gumi shar shar,
Iklas sosai take tausayawa Omar halin da yake ciki,tallafoshi tayi jikinta da kyar ta iya daura kansa a cinyarta ta jingina da jikin bed sai addua take tofa masa tare da shafa kansa,Omar bai San halin da yake ciki ba kawai dai yaji ciwon ya warke nan take bacci ya kwasheshi,Iklas tun tana masa addua har itama tayi baccinta a zaune jingine da bango hannunta kan sumar Omar haka suka kusa kwana,wurin 4am ta zameshi Daga cinyarta ta kifa jikinta ana Omar gashinta me matukar tsayi ya rufesu basu ma san a yanda suke ba haka suka dinga kwasar bacci,har rana ta fito basu sani ba,9am Mama da Ummi suka nufi dakin dan ganin ko lfy anjisu shuru,

Ummi ce ta fara murda handle din tana zura kanta ta juyo ta fito tana mu koma Hajia yaran nan yan zamani ne ,Iklas ba kunya gareta ba ,murmushi Mama tayi tace Allah dai yasa karta fadawa Babana nafiso ya fara furtawaa tukun...to ameen dai cewar Ummi.

10:30am Omar ne ya fara farkawa ji yayi kamar an danneshi hannu yasa zai ture Iklas daga jikinsa dan shi ya manta ma akwai Iklas,bai sani ba dai dai boobs dinta hannunsa ya sauka wani lutsum yaji kamar ya sa a flour,da sauri ya cire hannuwansa ya janye jikinsa,sai sannan yaga Iklas ce, a ransa yace kan uba dama yarinyar nan a bed dina ta kwana?
Wannan batajin magana mayyar mazace,amma koma me ya faru su Mama ne suka jawo wlh ni ba ruwana.tunanin irin laushin jikin Iklas da yaji yakeyi,shi kam gaskia yarinyar nan zata tasar masa da sha'awar da zai kasa control.

Da wannan tunanin ya shige toilet,Iklas kuwa tun farkawar Omar ta farka kunya ce ta hanata bude ido,kai yau sunsha bacci me dadi,Iklas tace yau na shaki kamshinsa da yawa bama na rigarsa ba na jikinsa.

Mikewa tayi tare da mika ta gantsare tana salati sai murmushi takeyi ta fice daga room din da gudu,tana zuwa Palon Mama taja birki tayi turus ganin,Baffah, Mama, Ummi, Sultan da Raj.suhaila suna room suna buga game,Abdallah na koya mata da suleim.
Kunyace ta kama Iklas musamman da tasan da jallabiyar Omar sanye jikinta,ganinta za ace mata mayyar miji,tunda Omar bai San da auren ba.
Komawa tayi Inda ta fito da gudu su Mama kuwa daria ma ta basu,tana shiga dakin Omar ya fito daga wanka idonsa jajir yana jin ciwon amma ba kamar na da ba,da sauki sauki,
Kallon Iklas yayi wai nikam tare aka haifemu ko mene,kin hanani sakewa sai kallon tsaraicina kikeyi bazan dauki wannan abunba ni,to ka bari nayi wanka nayi tafiyata mana.na fita wurin Mama naga mutane su sultan da Raj,
Chapter 23 · 0% Book details