← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 57

Sashe 3

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya ce ta parker motarta kuuuuuuuu ta fito dawowarta daga wajen aiki kenan,direct part dinsu ta wuce,duka yan matan kannen nata da umma suna zaune suna gulma da zage zage,sadiya ma zama tayi dabar kasancewar ita ce ba,umma kice tsinanne ya dawo kasar,Aisha tace na tsani yaya omar wlh waishi dole me kyau,me kudi,umma tace duk Ku saurara shi din banza wlh sai nayi maganinsu gaba daya har uwar tasu,

Zainab tace wlh umma karki daga musu kafa,naja tace har mu zai nunawa kudi aikin banza wai wannan sahar din matarsa har ta isa ta ganni tamin kallon banza,yanda take ji ita me kudi ce muma haka,domin aikin gomnati ne muma shi mukeyi,

Sadiya tace hmmm umma zatayi maganin ogan nasu ai,haka suka kai har dare suna zage zage,a karshe suka yanke zasu je masa sannu da zuwa don sugano kwakwaf,

Ita kuwa baiwar Allah mama tasa danta gaba yaci ya koshi dan tasan matarsa ba matar kirki bace,addua take Allah masa canjin alkhairi,amma ita kam wulakancin sahar ya isheta,nasiha ta masa sosai tare da Jan kunne wajen dagewa da addini,sannan ta turashi kan dole yaje ya gaida hajiya rahina umma,

Badan yaso ba bayan sallar isha ya isa part din,da zuwansa ya gansu a Palo rida rida a kwance ko wacce na latsa waya,umma na gefe,suna ganinsa dukkansu gabansu sai daya fadi dan mugun tsoronsa sukeyi,ga kwar jini da yake musu, Sam baya musu ko murmushi,dama duk zaginsu a bayan ido sukeyi,risunawa yayi ya gaida umma,da kyar ta amsa tana masa kallon harara,su kuwa yan matan kowacce yaya sannu da zuwa ka dawo lfy,lfy kawai yace ya ficewarsa cike da kasaita
Yana fita suka dasa gulmarsu kunga maye yanda ya kara kyau ga iya daukan wanka,ko wanne kaya yasa kyau suke masa.wurin mama ya wuce ya roketa kan ta barshi ya kwana gobe sai ya tafi gidansa,kyaleshi tayi dan tasan matarsa ba kula take dashi ba,

Suleim tana manne a jikinsa sai bacci takeyi,washe gari da safe uban yan daukan wanka omar sakkowa yayi daga sama yana zuba kamshi,sanye yake da wani yadi fari Sol ya matukar masa kyau,hattana takalminsa fari ne,ba hula a kansa sai gashi kwance luf.sallama yawa mum bayan ya cika tumbinsa ya basu tsaraba,wucewa yayi gidansa dake zone 11princess suit,gidan ya tsaru,

Driver ne ke tukashi har gidansa,tun daga compound yake jiyo hayaniya sama sama,a nutse ya shiga palon da sallama,frnds din sahar ya hango arna da musulmai maza da mata suna jin kida hade da hira,ga kayan ciye ciye nan,

Ran omar ne yayi mugun baci suna masa magana amma ko kallon su baiyi ba ya wuce room dinsa,ita kuwa sahar baki ta tabe hade da Jan tsaki,

Saida wata kawarta zuby tace sahar kije wajen mijinki kinga kamar ransa ya baci,tsaki sahar ta ja to sai me yanzu akansa zaku tafi haba mana frnds,next time zamu dawo yanzu kije wajen mijinki cewar wani saleem abokin aikinsu,bata so ba suka tafi ,yar aikinta ta bugawa tsawa kan tazo ta gyara wajen,direct dakin Omar ta nufa tana cika tana batsewa,sanye sahar take da T-shirt baka da skert din atamfa sun kamata kam,kanta ko dan kwali babu,

Tana shiga ta ganshi kwance kan gado yana latsa waya,baki ta turo ta kare masa kallo gaskia mijinta me kyau ne,ga iya wanka,a nan take sha'awar Omar ta motsa mata ba abinda takeso sama da ya biyaa mata bukatarta,gashi tasan fushi yake yi yanzu bare ya mata abinda take so,

A gefen gadon ta zauna sannu da zuwa baby ya hanya?tunda yaji haka yasan tabbas sahar wani abun take so ya mata,dan bata aikin banza sai da dalili,ko kallonta baiyi ba,sha'awace ta kuma lullubeta tace baby kayi hakuri nasan na ma laifi,kallonta Omar yayi tabbas yasan da dalili,sahar baza ta taba bashi hakuri ba tare da kudirin wani abu ba,a hankali yace ya wuce,in mutum yayi da kyau shima ya sani in ya bata ma ya sani,kisani ke baki isa ki sani bacin rai ba,Wanda ka damu dashi shi ne in ya bata ma rai kake damua,sahar taji haushin kalamansa amma sabo da tana neman wani abu tayi shuru ta kara cewa am sorry hade da hayewa kan bed din,yana kallonta ya gano me take nema,sha'awa ya hango zalla a idonta,kwancia tayi a kirjinsa,dan sahar ita bata da kunya ko kadan.

Shafashi ta fara tana wani shagwaba,babyna I missed u alot,tabe baki yayi yana kallonta ta fara cire masa Riga,baya son ya wulakantata,kuma yasan hakkinta a kansa musamman da ya tafi London ya Dade bai dawo ba,sabo da wannan dalilin ya biye mata yayi manage ya biyamata bukatarta,sahar tana jinta zam zam dan Omar gwarzon maza ne ya tsaya ya biya mata bukatarta sosai taji dadi har jinjina iya sex na Omar takeyi,guy ya hadu ta fannin romance da sex,ni kuwa nace danma ba zabinsa bace ke,bashi da feeling akanki.

Sahar tana jin zam zam ta mike tayi ficewarta,shi kuwa Omar baiji wani dadinta da yawa ba dan sahar ko dan gyaran da mata keyi na shan tsumi bata yi Sam,ita fa indai ba aikin gomnati ba to bata ganewa komai.washe gari Omar ya shirya tsab cikin suit baka yayi kyau yana baza kamshi ya sakko cike da takama da kasaita,dakin sahar ya shiga tunda ya tashi bai ganta a bed dinsa ba,room dinta ma wayam bata nan,Palo ya zo ba kowa sai hindatu me aikinta,ina sahar take cewar Omar,har kasa hindatu ta duka ta gaisheshi da sakin fuska ya amsa,yanlabai ta tafi wajen aiki tun 6am wai tana da tiyata,

Tsaki yaja ya fice gaba daya daga gidan ko dining bai kalla ba,yana mamakin yanda sahar ta rainashi ace matarka ta fita ko fada ma baza tayi ba,tsaki yaja hade da ci gaba da karanta jaridarsa yayinda ya kame a bayan wata luntsumemiyar motarsa Wanda takai milyan 40,driver ke gaba yana tukashi,shi Omar Sam bai damu da driving ba yafi so a tukashi kaji manya fa readers.

Hadadden gidansu yace a kaishi direct wajen mama ya nufa,a Palo ya sameta tana turaren wuta rungumeta yayi hade da gaisar da ita,mama kintashi lfy?lfy babanmu ya gida,great mama,to alhmdllh.mama breakfast fa?juyowa tayi da alamar tambaya gidanka ba a baka ba,wlh mama kin San dai komai,yan aiki keyi ni kuma kin San bana son kazanta,kuma yau mama inaso naje na duba gidan gonarki da kike kiwon kaji,kinga an Dade ba a duba ma'aikatanba da sauran abubuwa,murmushi tayi yawwa babana Allah maka albarka,da har na yanke shawarar zuwa da kaina,haba mama da raina da lafiyata na barki ki wahala.to Allah maka albarka.su abdallah suna schl ae ai ka sani.OK.

Haj amina tana da shahararren gidan kiwon kaji dake wajen garin abuja,baffan su Omar ne ya gina mata ya bata kyauta ganin haj rahina na aikin gomnati shi yasa ya bata wannan kyauta.
Haj rahina umma ta tafka bala'i akan wannan kyautar ta baffa,haka ta hakura.

abinci yaci ya koshi yawa mama sallama ya wuce office,karfe 2pm ya bar office ya wuce gidan kajin mama.

Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

4

By
Asmabaffa

1:30pm iklas ta shigo gida ta dawo daga tallanta,domin schl din da ta koma 8to12 ce ta irin manyan mutane ce Wanda basuyi karatu da wuri ba,irinta ta koma sabo da tallan da take zuwa domin da shi suka dogara,dan haka 12 tana dawowa zata tafi talla kan titin kwalta,1-1:30pm ta dawo,tana cin abinci zata shirya ta tafi saro apple da egg,tana dawowa sannan suhaila ta dawo sai su shirya su tafi islamiyya,Saturday Sunday kuwa da safe take zuwa talla zuwa 3 to 4pm ta dawo,haka take rayuwa kullum ba Hutu,gashi watarana har girkin gida ummi take sata dan bata so iklas tayi aure bata iya girki da sauran ayyuka ba,dan haka take sata dole,shi yasa ta iya komai dama gata jaruma,

Wanka tayi ta shirya cikin wata yar rigarta doguwa itama wata Igbo ce ta bata ita,light blue ce me ratsin ja ja da digo digon baki,daga sama ta dan matseta kasa ta bude amma itama da kadan ta wuce gwiwarta,basu da kayan kirki,dan ma waiyayenamure na taimakawa su basu kayan da suka musu kadan,wasu kuma har sabo suke basu,ita ma suhaila tana samun na yaransu,wasu kuma iklas na kokarin sai musu gwanjo,shi yasa kusan kayansu gaba daya English wears ne,tsangalallu ne badan suna sa dankwali ba sai ka dauka arnane suma saboda rashin wadata.to daya suke samun na ci ma.

Bakin gyale siriri ta yana kanta,batayi kwalliya ba powder ta shafa kawai sai Vaseline da ta shafa a lips dinta,tayi kyau dama me kyau ko ba kwalliya me kyau ne,wani takalmin roba me igiya baki ta saka,shima wani ne da yake siyarwa ya bata kyautarsa yaga tana da hankali,ga babu ta zauna musu.tayi kyau sosai a nutse ta dauki botikin saro kwai da ledar siyo apple ta yiwa ummi sallama ta wuce,a kofar gida suka hadu da suhaila ta dawo daga schl,anty har kin shirya?yeah iklas ki jirani muje tare mana,no je kici abinci ki huta ki shirya zuwa islamiyya kafin na dawo OK.OK anty sai kin dawo,Allah tsare shafa kanta tayi ameen suhaila,tana matukar kaunar kanwarta.

Tafiya tayi da dan nisa ta isa gidan kaji domin siyo kwai da apple,mutane da motoci birjik sunzo sarin kwai da apple suma,gaskia kowa ya kalli gidan gonar yasan an kashe dukiya,part part ne wurin kaji da kwai daban,part din fruits daban,kifi daban,ga sauran tsuntsaye da abubuwa kala kala.

Da araha suke bada sarin shi yasa ake cika gidan gonar,shi yasa iklas ke saro nata can dan ba karamin riba take ci ba,ratsa ciki tayi ta shige,ma'aikatan ciki sai fara'a suke mata suna gaisawa,dan sun saba da ita,gashi sun karanci nutsatsiya ce me mutunci da kamin kai,suna tausaya mata mace kamar ta tana sa'a irin wannan,da gani suna cikin talauci,shi yasa suke Mata arha fiye da kowa.

Tana tsaye tana jiran a sallami Wanda suka rigata, wata arniyar mota ta shigo cikin wurin,kowa bin motar yake da kallo,babu Wanda ya taba ganin kalar motar,har jira ake aga waye me motar,
Chapter 3 · 0% Book details