← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 57

Sashe 36

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Omar kafin ayi jeren Iklas har ma'aikata yasa suka kara yin adon golden jikin ginin Wanda yafi na da iri iri,ko ina sai ka rantse adon zinari akaiwa ginin wajen Iklas, komai dark brown da Golden ne,har labile idon gari.tsayawa fada muku yanda part din Iklas ya hadu iya haduwa karshe ya zarta tunanin me tunani,sai na gama novel din nan kaf ban gama ba,
Iklas koda suka dawo ma Omar na busy bata Ganshi ba,Iklas manya tsabar gyara duk inda ta zauna kamshinta sai yayi kusan 1wk bai bar wajen ba,ko gidan mutane taje to sai tabar musu tsarabar kamshinta.

Washe gari dangin su Mama mutum biyar sunzo raka amarya gobe,haka dangin Baffa,ga frnds din Iklas zuga guda,Rana ta Uku ranar kai amarya,da wuri Iklas taje wurin Saloon da lalle,masu mata lallen mutum uku ne ,sai mai gyara gashi,Karfe 4pm Iklas driver ya dawo da ita,kunga Iklas kuwa yanda ta koma?tab zankadaziyya kenan,dama gata fara kwal,ga lalle yayi kyau over,
Tana shiga room dinsu mero lallausa tana jiranta,nan itama ta hau nata gyaran,gashi sai bata abubuwa akeyi ta shanye wannan ta cinye wancen,Lallausa da Mama sun koya Iklas harkoki sosai na mata da ake amfani dasu,Mama da Ummi sun hada mata wasu da yawa an kai gidan,store kuwa both na Iklas Dana Sahar an dankareshi da kayan abinci haka kitchen ma.

Karfe biyar su Omar suna can suna Walima,amarya an shiryata tsab jiran angwaye kawai akeyi,Ummi da Maman saleem sun sa Iklas gaba da nasihar bin miji,idon Iklas Kamas ko kuka babu tunda wajen Omar ne bata da Matsala.
Ummi tace to kinji dai abinda muka fada miki kishiya gareki wlh kija mutuncinki,ban son tsokana nasan halinki,kuma ba a dambe da kishiya jahilci ne,ki kiyaye,zaman aure ne ba jin dadi kikaje ba ibada ce,dole sai da hakuri da juriya,ki farantawa mijinki,komai ba musu,sannan kinji na rantse Iklas kikaje kika tashi hankalin Omar da fadace fadace da kishiya Allah sai na saba miki,
Ki rike mijinki nasan dole kin San dai dai da rashin dai dai abinda ya shige miki duhu ga Mama ga ni ki bugo mana waya,haka dai suka dinga yiwa Iklas fada,kawayenta ma sai nasihar iya shege suke mata,
Amarya banda rowa a wangalewa oga cinya etc.
5:30 yan daukan Amarya suka zo,motoci Jere na alfarma aka dauki amarya da yan rakiyarta zuwa gidanta,Iklas fa har yau idonta tarwai har hira takewa angel kawarta,,
Gida ya hadu kowacce sai kallon tsaruwar gidan sukeyi,gidan Omar dan gayu gidane na alfarmar gaske,upstairs kadai part uku ne,haka downstairs ma karshen haduwa ce,bare compound ba a magana,kayan da akayi ginin Omar wasu da yawa basu zo kasar mu Nigeria ba,domin turawa ne sukayi masa ginin gidan.

Sahar da kawayenta yan magaa tantiran yan banaline da codine ne suna Palo sai shewa sukeyi hade da habaici kala kala,idan suka ga wata cikin yan kawo amarya sai kaji zagi da ashar na tashi.

Kowa tausayawa Iklas yakeyi sabo da Sahar da suka ga abinda takeyi,ita kanta Iklas ta shiga damua sai taji duk ta tsorata,gwiwowinta sunyi sanyi,gashi bata San ya Omar zai karbeta ba tunda ba sonta yakeyi ba,
Ummi na kusa da Sahar sunyi jugum jiyo muryar Sahar da sukayi tana ta zunduma Ashar.Iklas ji tayi dama bata yarda an daura aurenba,tasan Sahar watarana maybe kasheta ma zatayi.tsoro ne ya kama Iklas,amma har yau zuciyarta bata yi raunin da zatayi kuka ba,

Yan kawo amarya duk sun mata sallama sun tafi har Ummi amma still Iklas ko kuka babu.
Tana zaune tana tunani 9pm Omar, sultan,Raj sai Usy suka shigo dakin amarya Iklas,tana ganin Omar taji wani sanyin dadi,idon amarya kiri kiri mayafinta a kai amma bata rufe ido ba,haka aka bude da addua,sukayi musu nasiha da barkwanci,suka ajiye mata kudi Omar yaje ya Rakasu sannan ya dawo wajen Iklas fuskarsa a sake,ita kuwar gogar ji takeyi kamar ba aurenta akayi ba,normal tunda ta saba da Omar dama

Gyalen kanta ya cire mata yanmata Amarya,ya kk,a hankali tace lfy,yau najiye miki dadi abar da kika Dade kina kallon shape dinta a boxers ko a towel gata yau har gida,sai kin gaji,yau zan baki ita,tunowa Iklas tayi da kallo tabi Omar kamar zatayi kuka,
Cike da shagwaba tace ban taba kallar maka abu ba,kawai bangon dakin nake kalla amma kake ganin kamar idona a kanka yake, murmushi Omar yayi ganin yanda Iklas ta tsorata,bai taba sanin tana da tsoro haka ba sai yau,dama tsokanarta yayi.
Tausayinta yaji ganin bata San kowa ba sai shi,bata saba da kowa ba sai shi,kwantar da hankalinki amaryas tsokanarki nakeyi,da Sauri ta rufe idonta tana daria,tare da furta ai nasan Sir dama tsokanata kakeyi,

Omar a ransa yace zakiga tsokana yarinya nan da wasu kwanaki bazan iya jure kallonki ba ga sonki da ke ragargaza min zuciya,a fili yace dama ni salihi ne uztazu kece kike Neman lalatawa Mama ni,
Je kiyi wanka muyi Sallah,ko na miki?murmushi tayi ba yanzu ba sai watarana,zaro ido Omar yayi yau ga amarya Mara kunya wai Iklas yar yarinya amma tasan zasuyi wanka ma wato nan gaba,inda take birgeshi ba boye boye irin na mata dan a kallesu a nutsatsu, abinda ke ranta zata fada koma wanne kallo kayi mata kai ka sani.

Iklas ta saba da Omar bare ace zata ji kunyarsa,dama kuma ita bata cutar kanta da kunya a cikin arna ta taso shi yasa ba komai ke bata kunya ba,gogayya da mutane bata tsoro da Shakkar mutane bare ta bari a cuceta tayi fa talla a kwalta readers kar a manta.Iklas kwai wayo sai ta siyar da mutum a gabansa bai san anyi cinikinsa ba...
Mikewa tayi ta tube gaban Omar daga ita sai towel ta Shiga wanka,ta dan jima ta fito,Omar ya fita yana Room dinsa ko takan Sahar bai bi ba,tunda ya shigo shi da frnds dinsa ta kama zage zage,shi Sam bai dauki Sahar a me hankali ba,baya sata cikin jerin mataye,duk yasan irin bin mazan da Sahar ke yi,yana da labarin komai,shi yasa yanzu bazai iya hada makwanci da ita ba koda sau daya,

Shuru kawai yakeyi sabo da Baffa kar yayi laifi,kuma yana so lallai ya koyawa Sahar hankali ta gane aikin Gomnati ba shine gatan mace ba.
Sahar kuwa frnds dinta ta Sallama,ta shige dakinta tana hucin kishi,sai yau tasan lallai tana son mijinta,ga kudi ga kyau ya hada komai da ake bukata,

Tunowa tayi sanda Omar ya taba saduwa da ita,duk da ita keyin komai tayi enjoying fiye da mazan da take harka dasu,akan tayiwa namiji biyayya ya biya mata bukatarta gwara ta rike aikin Gomnatinta ta nemi maza ta biyasu kudi suyi mata abinda take so.cewar Sahar.
Haushin Iklas ne ya tasowa Sahar,har akwai wacce ta isa tayi kishi da ita ta kwana lfy,wlh yau babu Wanda ya isa yayi bacci a gidan.
Omar wanka yayi ya shirya cikin rantsatsun fararen kayan bacci na maza marasa nauyi sannan ya dawo Room din Iklas, a gaban mudubi ya ganta tana tufke gashinta,sanye da da wata rigar bacci kadan ta wuce pant dinta me siririn hannu tasha kyau,sai cinyoyi santala santala lumi lumi dasu farare tas,Omar da kyar ya danne zuciyarsa a ransa yana yabawa Iklas wurin kula da kanta,tasan kanta basai an koya mata ba,

Jikin mudubin Omar ya taka har bayan Iklas, tallafota yayi ya kwantar da ita a jikinsa,cikinta ya shiga shafawa tare da warware jelar gashinta data tufke,sai shinshinata yakeyi tayi mukui da ita tana zukar kamshinsa tare da yaba taushin fatar omar.

Bakin gadon ya jata suka zauna da kyar ya fisgo tunaninsa murya a dishe,idonsa yayi wani ja,tashi muyi nafeela,skert tasa tare da hijab sukayi Salla raka'a biyu da addua,
Suna idarwa tace ya Omar yunwa nakeji ina kazar tawa?daria yayi sosai wlh ban taba ganin amarya irinki ba.
Baki ta cokalo ni ka bani abinci naci Dama ina jin haushinka ka daura min laifi wurin Ummi rannan ka tafi,murmushi yayi tare da kallonta yana mamakin wai bata manta ba,shi ya Dade da mantawa,

Leda ya jawo mata gashi kici ki ture,Indai kazace akwai ranar da sai kin biya ni bashi kika ci,daria Iklas tayi Ai Allah bazan Biyaba Sam bata gane nufin Omar ba,bude mata yayi ledar kaji dakwa dakwa,yogourt da juice sai sauran kayan ciye ciye,kafada ta make haka ake bawa amarya kazar? To ya akeyi cewar Omar nifa kin San komai sai kin koya min,haka kakewa Sahar din?kai ya gyada mata wai ae,tabe baki tayi tab haka ake love din?shi yasa ta gama rainaka in zaka mike ka mike kayi maganinta ka nuna mata namijine kai,ka zauna lalaci,jifa sunanka wurin Sahar wai Holoko.hmm maganar nan tana kona min rai,amma kai ko ajikinka,ka tabbatar kayi maganinta ato rai bace Iklas tayi maganar kamar itace Mama.

Omar yasan maganar Iklas gaskia ce fa,dama tun farko ya samu Sahar yayi maganinta yayi mata kaca kaca,amma yanxu bazai iya hada jiki da ita ba tunda ta koma Neman maza.baya sonta,tana masa rashin mutunci amma yana iya kokarinsa ya biya mata bukatarta da abinda takeso shi ba wani karuwa yakeyi da ita ba amma kullim burinta ta yanka masa rashin mutunci.

Iklas ce ta katse masa tunani ta hanyar riko yatsun Omar tana wasa dasu,never mind idan tafi karfinka ni zan gyarata.kajifa karfin halin Iklas,murmushi me tsada Omar ya saki yace ko ta gyaraki ba,ki dai kiyaye dan zaneki zatayi idan bana nan,ban son abu ya sameki,a ransa yana jin dadin yanda Iklas ke damuwa da damuwarsa, jawota jikinsa yayi ya dinga bata naman a baki,yanko naman yayi shima zai sa a bakinsa hannunsa ta rike,ta sa bakinta ta kwace a hannunsa ta cinye,daria yayi sosai,da hannunta itama ta fara bashi yana ci itama yana bata,abin shar fa,
Sunci sun koshi sosai,lemo Omar ya kurba a bakinsa ya tallafo fuskar Iklas da hannayensa biyu bakinta ya nufa da nasa bakin,ya dan dago da kanta a hankali sannan a nutse cike da nishadi da shaukin so ya hade bakinsu wuri daya da harshensa ya bude bakinta ya juye mata juice din daya kurba a bakinta,ji kake makwat Iklas ta shanye tare da lumshe ido,
Kallon juna sukayi kowanne dauke da murmushi a fuskarsa,a sigar rada Iklas tace ya Omar kafa hadu ai ka fi kowa iyawa ma,ko novel ban taba karantawa ba,ai a karatuna na theory banzo nan ba.
Chapter 36 · 0% Book details