← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 57

Sashe 20

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iklas ta gaji ta yanke shawarar sanarwa da Ummi abinda ke faruwa da Ya Omar,tausayinsa takeji sosai gwara ta fada ko Allah zai sa a nemo masa magani,Omar kuwa kullum addua yakeyi sosai akan matsalolinsa,
Yau Ummi ce ta dauko naman ganda ta jikashi a cikin ruwa a wani bowl,Omar ta mikawa da soson karfe da wuka Umaru gyara wannan yau ganda nake son ci,ragadada zan bararraka mana,Omar kuwa bin naman gandar yayi da kallo Ummi wannan tsohon abin tun na last year ai ki bari a siyo mana fresh mana,yaushe za aci guba a ciki,kaga idan baza ku gyaramun ba to na dauke abina ban son iyayin banza,ke uwar yan lissafin duniya matso kema ki tayashi Ku gyara da sauri,yanzu in aka gyara wannan yaji hadi kamshi ne zai cika unguwar nan,murmushi Omar ya saki Wanda ya janyo hankalin Iklas ta kafe Omar da ido tana kallon kyan da murmushi ke masa,
Ummi nifa ban iya gyara abin nan ba cewar Omar tare da toshe hanci,sannu gayu mutanen Allah Iklas matso ki koya masa kuyi maza.

Hand globe Omar ya nemo yasa a hannunsa wai kar hannunsa ya dauki warin naman,Iklas kuwa tuni ta fara gyaran a garin yi ta fallatsowa Omar ruwan a fuskarsa ruwan ya sauka a kumatun Omar,sorry cewar Iklas tare da ci gaba da dirzar gandarta,kyankyami ya kamashi Omar ya fara wanke fuskarsa da ruwa bayan ya gama ya dawo yana wlh kika kara bata min jiki sai na miki wanka da ruwan wanke naman gandar nan,

Baki Iklas ta tabe ya Omar dama shan ice cream ka kaimu shi nake sha'awa muje pls da dare,harara ya watsa mata kin isa ma na kaiki daga nan ki kaini wajen su Baffa ko?haba dai ni na isa da wanne idon zan kalli Mama cewar Iklas to shike nan zan kaiki ke da Suhaila amma yau sai dare zamu fita,dadi Iklas taji sai washe baki take,kara fallatsawa Omar ruwan naman tayi a farar T-shirt din dake jikinsa,
Haushi yaji kin kara bata ni da warin abin nan saboda kin rainani fuskarsa a daure ya dan ebo ya shafawa Iklas a fuska sai daria take tana rokonsa ya bari,yatsunsa ne suka sauka kan lips dinta wani taushi yaji tare da shagala wurin shafasu yana yawo da yatsansa kan lips dinta,goce fuskarta tayi gaskia ya Omar baka kyauta min ba ,jiba face dina ta fada cike da shagwaba kamar zatayi kuka,

Sannu yan mata ni da kika min har sau biyu fa,Ummi ce ta fito daga daki tare da kallon bowl din taga ba abinda suka gyara kawai jagwalgwalo sukeyi musamman Omar ma,dauke bowl dinta tayi tace kuje Ku karaci shashancinku,haba Ummi ki kawo mu karasa miki cewar Omar,a'a kuje na yafe.

Cike da shagwaba Omar yace Ummi kalla rigata yanda jikarki tamini da ita gaskia ta tashi ta wankemin abata,yanda Omar yayi shagwabar abin daria kamar yaron da aka yaye jiya,Sosai ya bawa Ummi daria a ranta tana lallai Omar masu kudin gaskene naira da gata ya gama ratsa jininsu.

Iklas kuwa bata San sanda ta kyalkyale da daria ba dan shagwabar Omar abun daria gashi tayi mugun yi masa kyau,Omar kuwa ya manta Ummi ba Mama bace ga Iklas kusa zata rainashi dan shi a zahirin gaskia bai San yayi bama don kallon Ummi yake kamar Mama.
Daure fuska Omar yayi tare da shigewa room dinsa,kayan jikinsa ya cire ya fito ya fada toilet tare da sake feso sabon wanka kaji fa dan gayu readers,
Wasu kayan ya canja jean fari da wata tsadajjiyar T-shirt baka me rubutu fari an rubuta I do what I want da many an baki,
Kallonsa Ummi tayi Umaru sarkin wanka ga iya shiga oh matarka tana shan kallo.murmushi kadan yayi Ummi kenan na gode.

Kallonsa Iklas tayi da kyar ta iya Jan numfashi sabo da kyan da Omar ya mata,amma a fili tabe baki tayi cike da masifa wai ke Ummi an fada miki ya Omar bafa ya son matarsa kuma fa itama ta tsaneshi kudin sa take so,ita bata son aure tafi son aikin Gomnatinta,kuma yar isk......Omar ne ya cire kafarsa daga hadadden takalminsa ya dora tafin kafar a kan Iklas ya dungura kanta kasa ya danna sabo da Omar a tsaye yake jingine jikin bango yana danna waya.
Ba shiri Iklas tayi shuru tana nishi,Ummi kuwa ta gama gane Iklas kishin Omar takeyi amma ita kanta Iklas bata gane hakan ba.
Iklas ta dauka abin na Omar wasa ne,suna hada Ido taga idonsa ya canja yayi jajir kamar dai ciwonsa zai tashi don jikinsa har rawa yakeyi.da kyar Ummi tazo ta janye Omar tana ke in banda shirmenki Iklas me ya kaiki tsara karya kan matar mutum fada Ummi tayi mata sosai,ita kuwa Iklas mamaki abin na Sir Omar ya bata.

Maza ni yar banza me Jan fadan tsiya kije kiyi wanka ga magrib zatayi,da sauri Iklas ta shige wanka,Omar kuwa sai daya dauki like 5mnt ya dawo normal daga jin yanda zuciyarsa ke masa zafi.
Bayan sunyi sallar isha Iklas ta dan Dasa kwalliya tasha Riga da skert English wears tayi matukar daukan kyau,shape sosai ya fito ta dan yi acuci da gashinta tare da yana mayafi karami,kwas kwas tasha choge,tana fitowa Omar ya watsa mata wani kallon koma ki canja shiga,ba shiri ta juya ta sa shadda dark purple duk cikin kayan da Oga Omar ya mata ne.

Ummi suka yiwa sallama suhaila na bada sautun chocolate, suna fita already mota sabuwa dal tana waje kamar yanda suka saba,yau Omar ba fara'a fuska daure Iklas tsoronsa takeji kar ya shaketa,a tsorace ta miko masa hannunta gashi ka rike kar a samu matsala cike da bacin rai ya fisgi hannun sai da kashinta yayi kara.

Da sauri sukayi take away na abinda suke bukata suka shiga mota,suna hanyar fita daga wurin Sultan da security suka shigo wurin Sultan bai gane motar ba saboda Omar bai fiye yawan hawa mota kala kadan ba,kullum cikin sake motoci yake,

Omar ma bai ga shigowar su Sultan ba yana can ya Lula duniyar tunani,suna dawowa gida a bakin kofar Omar ya tsayar da Iklas kallon kallo sukeyiwa juna,u hv to be very careful wlh kika sake kika fadawa wani yanda ciwo na yake sai nayi maganinki ya fadi tare da tallafe mata keya tas ya zuba mata rankwashi kwas.

Kanta ta dafe tare da turo baki tana dire dire da kafafu kallonta Omar yaa tsaya yi sai kuma yaji ta birgeshi tare da bashi tausayi,nan take ya tsinci Kansa cikin farin ciki gaba daya damuwarsa ta yaye,
Hannu ya mika da niyar rungume ta,ita kuwa Iklas ta zata dukanta zaiyi da gudu ta goce ta zura gida da gudu wayyo Ummi ta fada palon, daria ma ta bawa Omar.
Yau ko girkin dare ba Wanda yaci abunda Omar ya siyo musu shi aka baje aka ci aka sha akayi dam.

Wurin 3wks kenan su Sultan suna aikin neman Omar amma shuru Allah baisa sun hadu da Omar ba,
Ummi kawo mu siyo miki naman miyar cewar Omar,to Umaru kuje da Iklas akwai dan nisa tsakaninmu da wajen da muke siyarwa,yawwa Ummi kinga ma dan wasa kafarmu cewar Iklas tare da zaro hijab dinta iya cinya me hannu,Omar kuwa jallabiya ce fara jikinsa,
Suna fita ya rike hannun Iklas kamar kullum suna tafiya amma Iklas ce kadai ke bashi labarin babanta da babarta da suka rasu,
Sai kallonsu akeyi kamar sabon aure kowanne naji da nasa radadin kyan.
Sunsha tafiya a kafa har baabban titi suka tsallaka sun siyo, sun bar wurin me naman kenan wasu suka parker da motoci wajen guda biyar,kartai ne manya manya wajen su biyar suka fito daga cikin mota daya, basuyi wata wata ba suka fisge hannun Omar daga na Iklas tare da make iklas gefe can har sai da ta fadi kasa,da gudu Omar yayi kanta da niyar dagata,wasu manyan kartin ne suka sake fitowa su hudu,sukayi sama da Omar tare da cusashi a mota,
A gigice Iklas ta kama ihu da fadin barayi Ku taimakamin jama'a sun sace minji,kajifa Iklas wai miji, help me pls my husband oooo shuru babu Wanda ya jita wurin ba mutane gata abj ne,

Motocin sun Fara tafiya Iklas na kuka ta zo tsallaka titi mota ta banketa a kan idon Omar domin yana bayan mota sun daureshi tam tam da igiya saboda sunga ya fara fisge fisge kamar me aljanu,Wanda su basu gane ba ciwon omar ne ya tashi sosai ba Iklas kusa.

Omar na kallon mota ta bige Gomnati ya rushe da kuka a motar kamar yaro,ga zafin ciwo gashi mota ta bige masa iklas Gomnatinsa.
Tuni kartan nan sun sanarwa Baffa da Sultan cewar sun kamo Omar,murna sosai sukayi baren ma Mama.

Omar har yau hawaye yakeyi ga zafin ciwo,duk wani masoyin Omar suna nan sun hallara damkam a compound din gidan,ana son tarbarsa bakin kowa a washe.
Iklas kuwa tuni jama'a sun taru a kanta,labari ya watsu mota ta bige gomnati, kaji fa popular. Wani dan saurayine me dan saukin kyau ya fito daga motar da ta kade Gomnati,baiyi wata wata ba ya sureta sai asibiti.

Asmahbaffa

[29/03, 02:07] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

65-70

By
Asmahbaffa

Wangale gate din su Omar akayi tare da jera Shiga wakeken rangadeden gidan da motocin gaba daya wannan kartan sukayi,Omar Wanda ya gama galabaita gashi an kawoshi har gidan da bazai iya rayuwa ciki ba,ji yake kamar za a zare masa numfashi yayin da motar da yake ciki ta shiga cikin gidan iyayensa,kafin ka bude ido Omar ya fara shuru shure da make make,gashi an daure shi kamar wani huhun goro,mutanen da suka taru za a tarbi Omar jiran fitowarsa kawai sukeyi suna washe Baku,Abdallah da suleim sai zumudi sukeyi,yayin da kungiyar haj.Rahina suka tsaya suna zage zage da masifa,aikin banza akan wannan fasikin suka wani taru aikin banza cewar Aisha,
Chapter 20 · 0% Book details