← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 57

Sashe 29

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kyale Baffa tayi saida ta bari yana part din Maman Omar suna Palo gaba dayan yan part din Mama sun hallara ana ta hira ana ciye ciye,Haj Rahina ce ta kara fadowa palon tare da watso pics din jikin Omar tana wallahi baza ku jawo mana bala'i a gidaba,kallon Iklas tayi annamimiya karuwa,kafin kace me su sadiya sun cika palon Mama,
Suna jiran suga hukuncin da Baffa zai yanke,Mama ce ta kwashi pics din ta kalla daria ma abin ya bata,zama tayi tana murmushi,Ummi ma tana ganin pics ta ja tsaki ta ci gaba da kwasar girkinta,
Iklas kuwa daria take sosai ta kalli su Umma da su Aisha shekeke gwalo ta musu tare da furta kun makaro mission failed..Ku sake new.
Gaba daya su Sadiya baki suka saki ganin ba wanda yayi mamaki ko bakin cikin ganin pics din bare ace har an yankewa Iklas da Omar hukunci.

Omar ne kadai ya shiga matsananciyar damuwa da tsoron abinda Baffa da ma
Mama zasuyi masa sai gumi yake hadawa Abdallah ma hannu yasa zai karbi pics Omar ya bige hannun tare da kwace hotunan,kishin Omar kar Abdallah ya kalli jikin Iklas.
Rahina tace algungumi in kana da gaskia ka bashi ya kalla mana,kasan bakayi dai dai ba,kallon Iklas tayi ke kuma muje zuwa sai kin bar gidan nan.
Ran Baffah ya baci ganin yanda Rahina take wa su Omar sharri,tsawa ya daka mata sai me to me sukayi a nan? Ke kullum bakya son zaman lfy,kinfa isheni ki guji ranar da zan yanke babban hukunci kanki.
Alhaji kasan me kake fada kuwa cewar Rahina,kalli irin iskancin da yaran nan keyi amma ko a jikinka,sai ma Goya musu baya da kakeyi wato an gama dakai.
korarsu baffa yayi daga part din Mama gaba daya.suka fice da borin kunya

Shi kam Omar mamaki yakeyi sunyi laifi babba amma ko damuwa su Baffah basuyi ba sai ma ci gaba da sukayi da hirarsu cike da nishadi,kunya ce ta lullube Omar gani yake ya aikata babban laifi a ransa yace lallai iyayensa ba karamin sonsa sukeyi ba sabo da son da suke masa sun kasa masa fada kan mummunan laifin da suka aikata.

Gashi har sonsa da suke ya shafi Iklas itama sun ki yimata fada.kunya ta cika Omar har ya kasa zaman Palo ya dauki key din mota ya fita,
Shopping mall yaje ya dankarowa Iklas siyayya ta kayan sawa Dana kwalliya,sai kayan zaki da ya siyowa Suhaila da Suleim.
Mama da Ummi suna ganin yanda Omar keta faman jin kunyarsu kayan ma daya siyo yar aiki ya bawa ta kai musu.har waya ya siyowa Iklas sabuwa dal Infinix ta dubu Dari da hamsim,Iklas sai murna takeyi tana godewa ya Omar.

Mama da suke kitchen ta kaiwa kayan ta nuna musu,sosai suka ji dadi,Suleim da Suhaila da gudu suka ruga room din ya Omar suna ta masa godiya nan suka zauna palonsa suna ta surutu Omar na jinsu yana latsa waya,
Ya matsu yaga Iklas,Sam baya jin dadi in bata kusa dashi,jiranta yake tayi ta Shigo don ya matsu dare yayi yasan dole zata zo bashi maganinsa,
Tunanin daren jiya kawai yakeyi ba karamin dadi da Ni'ima yaji ba a jikin Iklas.
Ji yake dama tun farko itace matarsa,shi burinsa bai son auren mata biyu burinsa ya zauna da mace daya irin su Iklas ta isheshi.

Masifa Ummi ta farayiwa Iklas. Da tsohon Daren nan kike tsara kwalliya haka,wlh ki dai kiyaye namiji baya jira ciki zai miki a banza,kuma kin San duk da kuna da aure shi fa bai sani ba,kuma baice yana sonki ba,ki kiyaye kanki har ya furta.
Baki Iklas ta zumburo daga mutum yayi wanka nasa turare da powder sai lipglow fa kawai,so kike naje furkai furkai wajensa,tana shagwaba kamar zatayi kuka taci gaba bayan ke kikace duk son da mutum ke maka in baya tsabta wanka da kwalliya komai fes cikin kamshi in bakayi sai yaji baka birgeshi ka fara sire masa,kuma zanyi kince wani waye waye,me kike so nayi to mutum da mijinsa ke a zamaninki wa yasan me kikayi.

Salati da sallami Ummi ta fara yau mun shigesu,ga marar kunya a fili karara,yanzu daga cewa ki kula sai kinmin gori,ke ga me miji ko?Iklas yanzu tun baki tafasa ba zaki kone,akan namiji ke a dole dadi miji, Allah yasa dai muma mun taba auren nan...ae naji din cewar Iklas....marakunya yar banza wuce ki tafi ki barmin daki,hijab Iklas ta dauka zata fita Ummi tace dauki wayarki kuje Ku Karachi rashin kunyarku,naga umaru ma da bai San ke matarsa bace ya fiki rashin kunya.

Tuni Iklas tayi hanyar dakin Omar tabar Ummi da babatu,tana zuwa Palo taci karo da Mama da Baffa zaune kunya taji sosai sadaf sadaf ta wuce tare da cewa sannu da hutawa tabar Palon cikin sauri
Murmushi Baffah da Mama sukayi na manya cike da jin farin ciki.
Tana danna sabuwar wayarta ta shiga Palon Omar yau a Palo ta sameshi yana aiki a system dinsa dagashi sai singlet fara da short, dagowa yayi ya sauke kyawawan idanuwansa a fuskar Iklas,wani kallo ya mata tare da dan guntun murmushi,itama haka sannu da aiki ya Omar harda wani rusunawa ita a dole biyayyar miji,kujera ya dan buga da tafin hannunsa yana mata nuni kenan ta zauna ba tare da yayi magana ba,shi kuwa yana kasan kujerar data zauna,sosai yake shakar kamshinta,gajiya tayi ta cire hijab dinta ta lunke taajiyeshi gefe,wasu kayan bacci ne a jikinta Riga me gajeren hannu iya gwiwa da wandonta dogo masu laushi pink color.
Sun mata kyau,wata hula tasa me Kyan gaske pink itama gashinta kuwa ya kwanta a gadon bayanta Omar har satar kallonta yakeyi.

Mikewa tayi ta dakko masa juice ta tsiyaya masa yana danna laptop dinsa yana zukar lemo me sanyi,a ransa sai yabon Iklas yakeyi,wasu takaddu dake gefe sunfi Dari ya kwaso ya mikawa Iklas Biro sakko ki min signing a papers din nan ma'aikaciyar Gomnati,cike da jin dadi ta sakko kasa itafa yau duniya sabuwa tana taya aiki yau gata ga papers wai yau itace zatayi signing a papers,
Shi kuwa Omar dan kawai yasa Iklas farin ciki ya bata tayi masa,sai dariya yakeyi a ransa yanda yaga Iklas ta kuke sai signing takeyi cike da nishadi har zancen zuci takeyi.
Kasa yin aikinsa Omar yayi ya tsaya kallon Iklas kamar tana Office,babu bata lokaci ta gama du tana mika masa tace a kwai wasu,murmushi yayi sai next time,OK Oga Sir,biro ya kwala mata a kai,na hanaki fadamin Oga da Sir bakyajin magana.

Wajen ta Sosa mantawa nayi fa ya Omar to ki kiyaye gaba if not a bakin aikin ki.ko ki fasa komawa schl,hakuri ta dinga bashi,
Aikin ya gama ya shige bedroom zaiyi wanka har yayi shirin bacci Iklas tana palo,kayan wuta a kashe ya koma room Iklas na biye dashi,magani tabashi yasha ta mika masa na shafawa gashi ka shafa ai kaji sauki,
Omar harga Allah yafi so ta shafa masa ko zai rage zafin radadin sha'awarta.kallonta yayi je ki kira min Mama ko Ummi su shafamin tunda me zaman jiyyar bata da amfani.

Turo baki tayi taci gaba da yin shinfidarta a kasa ta kwanta abinta,haushi Omar yaji taki shafa masa a jiye maganin yayi a kasa yayi kwanciyarsa,Iklas tana kallonsa da ido daya.

Saida ta tabbatar yayi bacci kana ta lallaba ta cire masa Riga ta shafa masa a hankali dan kar ta tasheshi tana gamawa ta koma wajenta ta kwanta duk abinda tayi Omar na jinta don idonsa 2 baiyi bacci ba.
Sai dadi da murmushi da ya dinga ji ba tare da Iklas ta sani ba.

Bikin su sadiya sai karatowa yakeyi,suna ta shirye shirye,saura 3wks bikin.su Umma ba zama sai karbewa Baffan su Omar kudi takeyi komai suce hidimar biki ce.
Ibzzy Boy ya hana kansa sakat akan Iklas shifa dole su wankan tsinke su rakashi gidan zaije da kansa.

Baban Sahar da Mum dinta ne sukayi sallama giidan su Omar ba kalar zagi da cin mutuncin da basuyiwa Baffa da Mama ba,duk abinda sukayi a kunnen Omar dan haka yace su je zai aiko da takardar Sakin Sahar.
Dadi sosai sukaji sun rabu da kaya.

Iklas na kitchen tana shirya dinner food Kiririn karar text taji a wayarta da ke gefe,number Omar ta gani,da Sauri ta bude text din
KINA INA?kawai ta gani,reply ta tura masa
INA KITCHEN GIRKI NAKEYI. Minti daya wani sakon ya fado
JAGWALGWALO DAI,KIYI SAURI NI KI TAHO KI BANI MAGANINA, reply tayi
KASAN INDA YAKE KASHA MANA PLS
kirrrrr sai ga kiransa tana dagawa cike da fada banson shirme kiyi sauri ki zo,kuma ki kawo min girkin naki na dan Dana naji yayi ko baiyiba ok dit ya datse wayar.

Kallon wayar tayi ta saki murmushi sannan ta gyara kitchen ta ebi na Omar ta shirya a lafiyayyen tire na yan gayu,
Wanka tayi tayi shirinta na kayan baccinta masu kyau,abicin ta dauka ta shiga part din Omar.

Asmabaffa
[06/04, 02:49] Dan Fbk 2: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

105-110

By
Asmabaffa

JANNAT AND ZULAIHAT NA GODE DA COMMENTING READERS GABA DAYA.👍👍

Kwance yake headphone makale a kunnensa yana saurarar karatun Alqurani ta shigo palon bakinta dauke da sallama,a hankali ya amsa mata yana mata kallon kurilla
Sanyi yaji ya mamaye zuciyarsa,farin ciki yake tsintar kansa da zarar yayi tozali da Iklas,itama Iklas ta rasa dalili kullum idan basa tare da Omar bata jin dadin rayuwarta,
Chapter 29 · 0% Book details