Sashe 27
Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iklas na shiga palon Omar ya mike yana wani narkewa ya janye Iklas zuwa part dinsa, suma su Suhaila sunyi Mama ki kwarai ganin Omar na numfarfashi amma lokaci daya ya mike garau.
Mama basu San me akeyi ba suna daki.Iklas hankali tashe ta bishi har room dinsa sai wani lallabashi takeyi,a sofa suka zauna sai nishin karya yake tare da cewa mutuwa zanyi,da kyar idan zan tashi,wasiyata......sai nushi....a firgice Iklas tace dan Allah ka daina fadin haka Sir,no ni nasan me nakeji Iklas, fashewa da kuka Iklas tayi,ya ci gaba ban San dalili... ba.... sai.... naji bana son ganin.... mace da namiji.... tare.... ko wace Dana gansu sai ciwona ya dawo sabo.
Yaya to ai kuma gani ni da kai,wasu nace miki ba mu ba,Ashe bakya kauna na warke ban sani ba..... gashi nan kin kula wani ciwona ya tashi,tausayinsa Iklas taji to indai hakane bazan kara kula kowa ba,yawwa ko kefe idan kuma ba kyaso na rayu to....haba ya Omar ka daina fadin haka ai na daina ma baza ka mutu ba da izinin Allah.
Har Saleem bazan kara tsayawa dashi ba sai dai in dasu Ummi a wajen. dadi Omar yaji yayiwa Iklas wayo wani sanyi yaji a ransa.Ashe kinaso kiyi aikin Gomnati? zabura Iklas tayi tare da yake hakoranta masu matukar kyau da haske Allah Sir da gaske zanyi aikin Gomnati?kai ya daga mata yasan yanda take kaunar aikin Gomnati da wannan zai mata wayo.shi kam sai yanzu ya tuno ma Gomnati ce fa da kanta.
Ci gaba yayi da indai kin min biyayya duk abinda nace kinyi to aikin Gomnati sai kin zaba,sannan zaki zama cikakkiyar Gomnatin,dadi ya gama cika Iklas kallonsa tayi zuru kamar zata shige masa fuska ya ka ganni a mota ta?ina tukawa fiiiiii, nayi gidana me kyau,habawa ai wlh har Office zan kaika kyauta, Omar murmushi yayi yace har na hangoki ai kin ma zama Queen kawai,
Daria Iklas tayi me kayatarwa tace kai ai har rancen kudi zan dinga baka,Omar yace lallai zanfi kowa cin kudin kenan, da sauri tace sosai ma Kaine fa Ogana,
har kudin man mota du zan baka har ma rance in kana so kazo wajena,daria Omar yake sha kawai ganin shirmen Iklas da kuruciya,na biyawa Ummi makka,nima naje,Suhaila ma har schl zan tsaya mata. Cikin sigar rada Omar ya furta Good girl, mijinki fa? far tayi da ido aishi na daban ne amma bazan bashi ya min kishiya ba.kuma bazan ci dashi ba,dafa kafadar Omar tayi duk cikin labari bari ma kaji dai dai da eyeliner sai ya siya in ba haka ba yaga fuska ba kwalliya,kallonta Omar yake sosai yanda take zaro zance gata yarinya amma tasan wannan.
Uhum ina jinki gyaran jiki kawai zan tai maka na masa da kudina saboda kaina zanwa,Omar ya gane sarai yace mene kuma gyaran jiki bayan wanka da kwalliya? Baki Iklas ta rike yanzu kai duk auren da kayi baka da labari lallai an barka a corner. daria Omar yayi sosai yace to ni me na sani, lallai ka fado wlh,ina fadama zan kashewa jikina kudi alaji sai kowa yasan Gomnati ta kama kasa.
To ai baki fada min gyaran jikinka ko Wanda ake shafa muku halawa da kurkur indai wannan ne na sani, hmm kawai Iklas tace baza ka gane ba Sir,ana ma zancen gyaran gaske Wanda zai sa na zamo on top kana wani magana,assignment kaje ka tambayi matarka ni kunya zanji gaskia.
Mikewa yayi tare da yatsina fuska je kiyi sallah magrib tayi maza sarkin surutu ki gaida Ummi.Omar ya samu sauki sosai yanzu baya ciwon da rana sai dare idan yayi mugun mafarkinsa shima mafarkin ba kullum ba.
Najja ce yau tazo part din mama abin mamaki cike da ladabi ga mutunci sai fara'a takeyi,Mama tayi mamaki kwarai tasan wannan karyane da biyu.ruwa baya tsami banza.
Bayan sun gaisa da kowa kujera ta nema ta zauna tana baza ido tana so taga ta ina Iklas zata bullo,shuru shuru Iklas bata fito ba,tana zaune tana jira.
Bangaren su Ibzzy boy ma sun gama shiri tsab domin zuwa gidan su Omar wajen Gomnati domin tuni Ladi Pijo ta nemo address din su Omar, yayinda suka wanke Ibzzy suka karbi kudi me tarin yawa a wajensa suka shirya masa lissafin karya.
Jalila wankan tsinke da Fati Gocewa su suka dau wankan sukari Ibzzy ya basu radediyar motarsa suka shige sai gidan su Omar.Najja tana ta faman jira su wankan tsinke suka shugo suma,sai yanga sukeyi,Mama dai bata sansu ba,kuma ita tasan bata da yarinya mace babba bare tace kawayenta ne,yan aiki Suna ta kyalkyale gida suka cika musu gabansu da kayan motsa baki.
Cike da masifaffen ladabi kamar mutanen kirki suka gaishe da Mama,Ummi ma har tsokanarsu tayi da wasa tagansu masu ladabi.Gocewa tace Mama dan Allah Iklas na nan? Oh Allah sarki kawayenta ne ku?ae Mama,,to madallah an gode bari a kira muku ita.
Kallon juna sukayi suka kashe ido daya. Najja kuwa haushinsu taji zasu bata mata mission. Kafin Suleim ta dawo daga kiran Iklas Sahar ma ta danno cikin palon tana tauna chewgum, so take taga tsinaniyyar da akace tazo gidan su Omar ta manne masa.
Tunda Sahar ta shigo sukewa juna kallon banza Najja dasu Gocewa.Iklas kuwa tana can tana shirin raka Omar Office zaiyi wani signing da meeting shida wasu manya.
Tana gama shiri ta shiga dakin Omar sun yi kyau,shadda yar gaske dark blue tasa shi kuma wani yard sharara light blue sunyi kyau sosai Iklas sai girma takeyi ga kyau ya karu.
Kamshin dadi ne ya bigi hancinsu Sahar gaba dayansu,Mama da Ummi kuwa mikewa sukayi ko wacce ta bar palon.su Suleim ma sun tafi garden lilo za suyi.sakkowa sukayi daga sama harrrr idon su Gocewa gaba daya a Kansu.Jalila wankan tsinke bata San sanda ta kalli Sahar ba tace kut balaa'i na koka,wannan guy karshene wajen kyau wlh har na kamu.
Fati gocewa ta karbe baren ma macen kamar balarabiya wlh ya iya zabe har naji kishi.
Tsaki Najja ta ja ta gyara zama sai kallonsu takeyi ita kanta sun birgeta.Sahar kuwa Ashe lallai yau za ayi asarar rayuka ta kundumo ashar.Iklas mata ta hango damkam a Palo dan haka tun kafin su sakko ta sagalo hannunta cikin na Omar asanfa da aurensa kar ma wata ta so mijinta. Omar tuni ya hango Sahar shi yasa ya kara shiga jikin Iklas Sosai.
Har Palo Iklas ta sakko sannunku kawai tace ta juya tana yiwa Omar rada a kunne dan kawai matan su gani taga sun kafe Omar da kallo.Omar kam kallon inda suke ma baiyi ba bare yasan da zamansu.
Wankan tsinke sai yaba sumar Omar takeyi
Fati gocewa kuwa ji tayi basirarta ta kare kaf,zata sanarwa Ibzzy kawai ya janye wannan ba jagwal bace tafi karfinsa.
Sahar ba abinda tafi jin haushi irin yanda Omar ya nuna bai Santa ba,kamarma bai San da wasu biladama a wajenba.Iklas ta gama tafiya da nutsuwar Omar sha"awa ta addabeshi tunda Iklas tayi masa rada a kunne, dama kuma kullum cikinta yake,ga so da tunanin Iklas hade da tsatstsan kaunarta sun gama mamaye zuciyarsa,
Gaskia bazai iya ba gwara ya fadawa Mama a daura musu aure da Iklas ko zai samu sauki.
Naja ce ta kalli su Sahar sai a bar mana gida kuma ai,Itama Sahar wankan tsinke ta fara zagi ai kuwa fada sosai ya kaure a tsakaninsu. Duk sun jiwa Kansu rauni ta hanyar cizo da yakushin juna, da kyar Mama tasa security suka kori su Gocewa,
Sahar fuska ta kumbura da cizo haka ta bar gidan, Najja kuwa da kyar take tafiya an barkala mata yatsan kafa da hannu ga tafkeken cizon su Gocewa kwance a kumatunta.
Sai sannu su sadiya ke mata.Allah kara nace .
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ
95-100
By
Asmabaffa
MASU COMMENTING MASOYANA DA MAKARANTA WANNAN NOVEL INA MUGUN JIN DADI KUNA BIRGENI TARE DA KARA MIN KARFIN GWIWA.
Sadiya wacce ke kula da jikin Najja tace ke kika biyewa Umma na fada muku wannan tsinaniyar kodaddiyar yarinyar bata da kunya bata da mutunci,ki kiyayi shiga wajensu,Ku barmin komai a hannuna Ku daina daka ta Umma,
Da sauri naja ta daga kai tace ai nima na daina biyewa Umma kawai cin uban yarinyar zanyi da kaina ba wani mutunci.
Ko kefa ai shi ya dace kawai Ku nadawa shegiya duka cewar sadiya.
Wankan tsinke suna komawa gidan shakatawar Ibzzy suka shiga nan suka fara bawa Ibzzy lbr,Fati gocewa tace wuuuuuu Ibzzy mu hakura shawara tafi karfinka wannan zukekiya haka matar manya ce,kai kaga saurayinta hadadden gaske.
Wankan tsinke taja tsaki ni haushina ma yanda matan nan suka yakushemun jiki,Ibzzy Boy gaskia bazan koma ba na gama zuwa,Gocewa tace da ya aka barmu ma muka shiga gidan,shi kanshi shiga gidan su Omar duniya ne ko ina matakan tsaro ni kam na zare hannuna.
Bakin ciki Ibzzy yaji Mara misaltuwa huci kawai yake tare sa furzar da iska, Omar yake kowa dan uwarsa yarinyar Na A.C dey for labs da zai nace mata,Ku dan uwarku ni zaku rainawa hankali in kashe muku kudi kuma Ku dawo kuna raina min hankali.
Wankan tsinke tace kai dallah saurara ka daina zaginmu baza muyi ba ai munyi kokari ma kasa wasu suyi maka,mari ya kwadawa wankan tsinke Wanda ba shiri tana Allah ya isa ta bar gidan Gocewa ta mike zata tafi ya sa kafa yayi ball da ita saida ta fadi,da sauri ta mike tabi bayan wankan tsinke suka bar unguwar baki daya.an bar Ibzzy kamar zai Ciro zuciyarsa sabo da bacin rai.