← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 57

Sashe 50

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka gwangwaje da juna sannan sukayi wanka tare nan wani sabon babin murzar juna suka bude,sai wurin 4 suka samu nutsuwa tun safe ake abu daya,shiryawa Iklas tayi taci gaba da fushinta ta dauki Jakarta zata tafi,Omar ya zata Iklas ta dawo kenan Ashe bata huce ba,tafiya zaki karayi kuma?cike da fushi tace Allah kiyaye na dawo da kaina ai class dina ya zube sai anyi biko na ehe.ta fada tare da ficewa driver ya figeta sai gidansu Omar,
Omar in banda dariya ba abinda Omar keyi akan wai Iklas yaji tayi.

Tana komawa gida su Mama ma sun ganeta wajen Omar taje sai daria sukeyi a ransu,washe gari ma haka ta kara figar gyalenta driver ya kaita suka yini suna sheka love ta shirya tana cika tana batsewa tacewa Omar Allah bamu Alkhairi,yana dariya yace to ki gaida gida.
Next day da gamma 5pm ta shigo palonta,Omar ta gani yana kallon news a jikinsa ta kwanta ai kuwa ya shiga yi mata tausa saida ta huta kana ta gyara ko ina yana kamshi, tayi musu girkin dare lafiyayye suka ci suka sha,suka shiga aikin Sunna ba ji ba gani,kusan kwana sukayi sannan Omar ya kyaleta badan ya gaji da ita ba,
Itama Iklas haka bayan sunyi break saida tasa Omar ya kara xxx sannan ta shirya tace na tafi,Omar yayi yayi ta hakura ta zauna tace Sam wlh sai yaje bikonta baza ta dawo da kanta ba,

Dariya Omar yayi sosai yace to ki gaida gida ya zaro bundle na 1k ya bata,tace Allah kara budi,na gode Allah ya kareka daka dukkan masu sharri,har mota ya rakata ta shiga driver ya figeta sai gidan Mama.suka bar Omar yana ta dariya.shima ya shirya ha bar gidan fes dashi.shi kam yajin nan na Iklas gaba ya kaishi ba bayaba, dan sosai take bashi zumarta.

AsmaBaffaⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

185-190

By
AsmaBaffa.

Omar tunda ya tafi cike da bacin Rai a zuciyarsa,haka ya koma gida yaji gidan ya masa fadi wayam ba masoyiya, nan ma yaji ba sauki bazai iya rayuwa haka ba,mikewa yayi ya fesa wanka 3qutr yasa da riga T-shirt masu matukar kyau sun dace da jikinsa,gashin nan sai kyalli yakeyi,Omar ba dai kyau ba ,karshe wajen kyau
Yau da kansa yayi driving shopping mall ya shiga duk abinda yasan Gomnati na so shi ya jidar mata ya siyo mata lafiyayyun gasassun kaji da ice cream ya wuce gidan.

Sallama dauke a bakinsa ya shiga palo,Ummi ya gani da su Suhaila,Mama na gefe tana waya da Baffa,da Ummi suka gaisa suna ta hira har Mama ta gama wayar,cinyar Mama ya kwanta sai shagwaba omar ke zuba mata kan ta barshi ya zauna gidan,amma Mama bata kulashi ba bare ta bashi amsa,

Ya rasa me ke masa dadi a duniya,daurewa yay ya cije tare da mikewa,nasu kajin da kayan ciye ciyen ya mika musu,ya kwashi na Iklas yayi dakin Ummi kai tsaye,Iklas na zaune tana bincike a wayarta ya shigo da Sallama yana ta wani cin magani,kamar zai maketa,daria ma ya bata
Kallonsa takeyi yayi kyau sosai,sannu da zuwa zumana,ko kulata baiyi ba yayi zamansa gefen bed din yana fushinsa,tana sani tace waya taba min kai ne my soul?a office ne? Harara ya dalla mata,
Allah huci zuciyarka Ogana idan ma wani ne ya bata ma,zaki sani ne indai nine zan rama,yanzu nan tun akan
Maganar room ce kake fushi haka?kayan ya tura mata ya mike ya koma wajen su Mama ko cikakken minti 5 baiyi ba ya dawo dakin Iklas a fusace cikin fushi yace ke dole fa ki zabi room guda naki na fada miki,
Kin San Halina a gaban Ummi ba ruwana zan iya hugging naki da wasu abubuwan gwara ki rufawa kanki asiri ki koma wani room din da zama,

Kallonsa Iklas takeyi da cikinta a gaba har ya gama fadansa,dariya tayi wacce ke kara mata kyau,sai kallonta Omar yakeyi da sha'awa komai na Iklas me kyau ne,baya gajiya da ita,tsayawa tayi da dariyar tace to kullum kullum da katon cikin ma baza ka bari a huta ba,ko tausayina baka ji zama da kyar tashi da dabara amma kai ba ruwanka,yanzu an dawo dani dan na huta jiba yadda kake min rigima,kayi hakuri na haihu nayi Arba'in,a fusace yace au harma arba'in Ashe kece mijin ma,to Honey zoka danneni ka kwata,

Murmushi yayi Iklas rigima kenan,zaki ga sanda zan danneki ne ai,dan kawai yanzu kinyi nauyi ne dole a biki sannu amma da sai kinyi bayani,nasan zaka iya ai oya zo muci abinci ka daina rigimar kai kasanni bazan bar mijina cikin Matsala ba dole akwai mafita ka daina bata bakinka,nayi yaji ma na nemoka baka zo biko ba bare yanzu da dole nima su Mama sukayi min,Ummi kakata ce ba wata kunyarta nakeji ba,

Sai yanzu ya dan samu nutsuwa da farin ciki,matsowa yayi tare da zama gabanta murmushi dauke a fuskarsa zama yayi sosai a gaban yana shafa ckinta,daga bisani ya jawo naman yana yankowa ya sa abakinsa sanna ya hade bakinta da nata yasa mata naman ta cinye tana kada kai uhmmmmm kaji dadin bala'i kuwa,
Haka ya dinga ciyar da ita har ta koshi,yau Omar a part dinsa ya kwana gidan Mama ba tare da kowa ya sani ba,Iklas kuwa tayi tunanin dama Omar dakinsa zai kwana,dan haka gaba daya tausayinsa takeji hade da wani sabon sonsa,da sassafe ta shirya kanta cikin doguwar rigar a tamfa,sama ya matse kasa ya bude sosai ya boye cikin ta,fitowa tayi sadaf sadaf zata shiga dakin Omar,suhaila ta gani da suleim zazu tafi schl,Anty ina kwana suka gasheta sukayi gaba da gudu,ita kuma ta fada room din Omar a kan bed ta hangoshi yana ta baccinsa cike da nutsuwa,komawa tayi ta sa key a kofar saboda tsaro.

Tana dawowa ta haura saman bed din tare da rungumeshi kam tana shakar kamshinsa tare da manna masa kiss a goshi,a hankali ya bude idonsa masu matukar kyau,ganin Gomnati a jikinsa ba karamin farin ciki yayi ba.

Ba tare da bata lokaci ba shima ya Kara manneta a kirjinsa wifey I miss u da kyar nayi bacci jiya,baki zo ba har jiranki nayi,miss u more honey nayi niyyar zuwa bacci ya sace ni,cikinta ya Shiga shafawa ya gudan jini na lafiya yake?haushi Iklas taji yace gudan jininsa wato ya kwace mata mijinta,
Shinema gudan jinin naka,ni wlh shi yasa banso haihuwar nan ba,yanzu sai ka dinga daukansa ni kana shareni,dariya Omar yayi me kishi da danta haka akeyin Maman babyn?ta tsani danta? Kece fa zuciyata gaba daya,cike da shagwaba tace to ai jini yafi zuciya muhimmanci shine zaka ce masa gudan jininka ni a bani zuciya,saboda ka samu da,fari tayi da ido Wanda ya susuta Omar lokaci guda tare da cewa dadin abin ai kafin ayi dan ni aka samu,kuma ai da nane.

Dariya Omar yayi kinsan me kike cewa kuwa wifey? Wannan shine ba kano ba birni,ba cinya ba kafar baya, shi yasa tunda ke danki ne kinga shi gudan jinina,ke kuma zuciyata kinga ai kun kwaceni du ke da baby,ni dai Allah ban yarda ba cewar Iklas ,ok to a bashi zuciyar ke gudan jini ko?kafada ta make abinda nafi so zuciyarka shine zaka ce a bashi ita,dariya Omar keyi yace to na bashi liver ta,da Sauri tace tab bai isa ba bazan yarda ba,Kasan kuwa muhimmancin liver da zakace a bashi ita yama fini kenan sosai fa ina laifin ka bashi yar madaciyar jikin hantar taka tunda shi yaro ne,ko ka bashi timbi ko hanji,

Fashewa da dariyar shiriritar Iklas yayi tare da kara kankameta sosai abin dariyar Gomnati da yawa yake, tafin hannunta ya mannawa kiss yana bin hannun da kiss ya gangaro wuyanta nan ya fara lasar wuyanta cike da salon kwarewa tattare da nutsuwa a hankali ya dinga sarrafata tunaninta ya gushe nan fa suka dinga baje harka,bayan sun nutsu wanka sukayi cike da nishadi,Omar na ta zuba mata albarka, Iklas dinsa dabance,tana shagwaba shi sai abinda yake so,gashi tana fahimtar matsalarsa ko bata so sai ta faranta masa,yanda yake bata wahala bata taba nuna gazawarta,
Burinta taga Omar kullum hankalinsa kwance,gaban kowa tana nuna rashin kunyarta dan ta faranta masa.

Har kaya ita ta sawa Omar tare da shiryashi suka fito fes fes dasu,Ummi bataga Iklas ba tunda taga haka to lallai Omar yana gidan,Iklas ta birge Ummi da take kula da mijinta,
Suna hirarsu kasa kasa murmushi dauke a fuskar Iklas suka shiga wajen Ummi suka gaisheta Ummi tana in kaga Zara kaga wata,suna ta murmushi suka je wajen Mama, tana ganinsu haka taji dadi a ranta amma sai ta tamke fuska ta fara yiwa Omar fada Dama nasan baka jin magana Babana saida ka kwana a gidan nan sabo da mun dauko matarka, ka kiyayeni fa,jikinta ya fada haba Mama nifa gwara ki hakura ki kyaleni dan Allah,Iklas ce tayi magana cike da marairaicewa Mama kiyi hakuri ki kyaleshi.ai na kyaleshi Iklas ya zanyi da shi ya fiye rikici,that's my Mum cewar Omar.

Kuje ga breakfast can a dining,Mama ta kara da cewa Iklas yan uwanki na kasar Libya jiya sunyi mana waya ni da Ummi,nayi magana dasu cikin harshen turanci duk da ba wani iya turancin nan nayi ba sosai dama Abdallah ke koya min,sunce zasuzo ganinku nan da 3days sai Ku kirasu kuji komai,number tana wayar Ummi,sosai Iklas take Murna ko ba komai yan uwansu zasu zo dangin mijinta su gansu asan suma suna da gata.

Omar ne ya kira yan uwan Iklas a wayarsa suka tabbatar masa nan da 2days gasu nan ganin yaransu,ai kuwa Saturday na zuwa aka tura driver ya daukosu maza su biyu mata biyu,dayar macen Babba ce sosai ta manyanta,dayar kuma budurwa ce yar gidan best Frnd din Baban Iklas me suna KHAIRAT.
zankadediya itama,part guda Baffa yace a ware musu shima yana nan zuwa next day zaiga yan uwan matar dansa, Iklas ta rasa inda zata sa kanta sabo da murna,su Sadiya ma sunzo sun gaishesu,bangaren Hajiya Rahina ma an rakasu sun gaisa,ba tare da ta nuna musu wani dan hali ba,su Sultan,Raj,yan uwa da abokan arziki duk sun zo sun gaishesu,haka frnds din Iklas suma,Maman saleem,saleem da matarsa duk sun je.
Su Kansu mutan libiya sunji dadi sosai,
Chapter 50 · 0% Book details