← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 57

Sashe 4

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta iklas duk tsaiwarta a titi bata taba ganin mota irin wannan ba,su kuwa ma'aikatan gidan sun San bazai wuce Omar ko mama ba.sun San irin wannan babbar harka sai iyayen gidansu Wanda suke jin dadin aiki karkashinsu,shi kuwa Omar tun shigowarsu kansa na kasa yana duba jarida,driver ne ya fito da sauri ya bude masa kofa,subhanallah shine abinda iklas ta furta a ranta ganin takalmi da kafafuwan Wanda ke fitowa,

Basu gama sumewa ba sai da Omar ya fito gaba dayansa daga mota,wani daddadan kamshi ne ya mamayesu gaba daya,iklas tana kallonsa gabanta ya fadi ji kake daram dam,sunga zallar baiwar kyau da kwarjini da cikar zati,iklas tace tab yau ga Wanda ya takeni a kyau,ido ta lumshe hade da bude kafafen hanci tana shakar ni'imantaccen kamshin Omar, shi kuwa Omar iklas ya fara hangowa da tsangalalliyar rigarta,kasancewar fara ce kar sai ta haske gidan. Gonar gaba daya,kallo daya ya watsa mata shima gabansa yayi mugun bugawa,bai taba ganin dan Adam me kyanta ba,duk kyansa sai yaga ga wata yarinya ta fishi,shi bai taba jin faduwar gaba ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinya,

Fuska ya yatsina kamar yaga kashi yayi mata kallon kaskanci ya wuce ta gabanta,da mutanen wajen maza ya gaisa ya mika musu hannu,sannan suka dan kebe da babban me kula da wajen suna magana.

Iklas kuwa ta cika fam sabo da irin kallon banzan da ya mata,bata son raini,dan suna talakawa shine zai yatsina mata fuska,hmm duniyace a ranta take wannan magana,ana haka har akazo wajenta aka cika mata botikinta ta mika kudi,lokacin Omar ya gama da wajen kwai ya wuce wajen fruits,da kyar take daga bokitin ta karasa wajen fruits itama ta mika kudi aka cika mata katuwar ledarta da apple,ta juya zata wuce sukayi karo da da botikin kwanta tayi karo da mutum gwaraf,amma batafi saman cikinsa ba,botikin kwai ya tuntsire wajen guda ashirin sun fashe,shi kuwa take yaji wani mugun shock a jikinsa zirrrrrrrrrrr wanda bai taba ji ba,sakamakon haduwar jikinsu,daurewa yayi ya dawo hankalinsa,tsaki yaja ya furta psycho kawai,haushi ta karaji ya mata abu maimakon hakuri sai zagi,ledar hannunta ta apple ta ajiye gefe,gabansa ta sha ta rike kugu hade da harara,malam kamin laifi da barna ka kasa bani hakuri sannan ka zageni,da nayi niyyar yafe ma amma wlh tunda ka zageni ka kasa bani hakuri to ba kira ba abinda zaici gawayi,sai ka biyani each and every egg da ya fashe,dan akanka bazan dauki asaraba,

Daria yace ta kamashi ya danneta,bai taba haduwa da funny girl haka ba sai yau,yar yarinya da Karin magana haka,ga masifa har wani jijjiga takeyi gaban katon namiji kamarsa.

Allah ya taimakesu ba wasu mutane wurin sai masu shirya fruits,tasowa sukayi daya daga ciki yace haba gomnati basai kinyi fada ba za a biyaki,shine me wajen,a fusace tace dama haushinsa nakeji ni time din daya shigo yamin kallon Tara saura kwata,dan haka wlh sai ya biyani,tofa wannan yarinya da kuruciya sosai kanta ga tsiwa cewar Omar aransa. Wasu ma'aikatanne suka zo wajen suna haba gomnati ikon allah bamu sanki da haka ba,wani ciki yace the manager wannan oganmune fa,murmushi ta saki jin an kirata da sunan da tafi so wato gomnati, Wanda ya tafi da imanin Omar, tace to na yafe masa sabo da Ku

Gefe ta matsa tana gyara bokitin kwanta hade da kunkuni kawai an cuci mutum,wannan days fashe ni haushina ma daya asararsa da akayi,yanzu wannan ya ishemu mu soya muci da su ummi har na 5days,ko mu soya doya da kwai ta kwana biyu,ai kuwa da munci dadinmu.duk surutun nan da takeyi Omar na jinta,sai daria yakeyi a zuciyarsa,yarinyar so funny,ya dade rabon da yayi nishadi irin na yau,kwai aka kawo mata guda 100 a Leda,kallon mutumin tayi laaaa ai nace na yafe masa wlh,ai oga ne yace a baki gashi guda 100 ma aka baki kinci riba...no na yafe ai,fafur iklas taki karban kwan nan,,sunyi sunyi taki karba,Omar ne ya karba hade da daka mata tsawa karba ban son shirme,tsoro ne ya kamata,taf aka cika botikinta da kwai,aka kara mata apples da yawa sannan aka mika mata kudinta,mamaki tayi sosai ta kalli Omar a tsorace na gode oga Allah kara arziki,sosai yaji dadin adduar ta matarsa bata taba masa ba,sai wata a titi,it's OK zaki iya tafiya, uhm....uhm.....dama oga dazu kaga fadan Dana ma,nayi ta masifa rainane ya baci kanwata na aika taki zuwa,shine raina ya baci,amma maganar gaskia bada kai nake ba,da kanwata nake.

Murmushi Omar yayi Wanda yasa iklas sandarewa ganin kyau da dimple na Omar,shi kuwa a ransa yace yarinyar nan da wayo take.a fili hade rai yayi ya tabe mata baki ya shige mota driver ya ja suka wuce.itakam taji haushin tabe mata baki da yayi,ya rainata.anyway sun sami kudin abinci lallai yau tazo a SA'A.

Yau taga lailatulqadari sunan da ta lakabawa Omar kenan kayanta ta dauka da kyar ta nemi taxi,kayan sun mata nauyi,ga murna an vata komai kyauta,shi yasa yau ta shiga taxi,ta matsu ta koma gida ta bawa kaka ummi labari.

Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

5

By
Asmabaffa

Har kofar gida me taxi ya sauketa da kayanta,da sauri ta shiga da kayan ta fara kwalawa ummi kira tsohuwa kaka ummi...ummi...tsohuwa wai kina ina haka,ke lfy kike rafka min kira haka kamar kina bina bashi cewar kaka ummi,iklas ce ta rungume ummi tana ummi lailatul kadari na gani yau,kinga yau komai kyauta aka bani kwai da apples ummi sai nayi 1wk banje sari ba,duk na kyauta zan siyar,kinga kudin yanzu zamu tafi kasuwa dama abincin mu saura na kwana daya,

Kaka ummi ce ta kalleta da murmushi tana mai cike da farin cikin kalaman iklas,to iklas wai waye lailatul kadari naga ta kaina yar nan karfa kiyi mana sabo,ummi oga ne me gidan kajin ya bani komai kyauta,nan ta kwashe labari ta fadawa ummi,ummi taji matukar farin ciki,dama basu da abinci ba kudi,

To alhmdllh iklas kece wacce ta iya tsari da lissafi sai muyi shawara,ai ummi yau baza mu islamiyya ba,dan kasuwa zamuje da suhaila,Biro da jotter ta dauko suka zauna a tabarma nan iklas ta fara planning,dama iklas akwai iya planning din rayuwa,nan ta rubuta abubuwan da suke bukata ta tsara komai,ta bawa ummi na cefane taja hannun suhaila suka wuce kasuwa.

Omar direct gidansu ya wuce wajen mama,cike yake da tunanin yarinyar da yaji ana kira da gomnati ko manager sunan ne ya bashi daria,ya kara nanatawa a ransa bai San sanda ya saki murmushi ba,nan take ya shiga tunanin yanda take masa tsiwa a gidan gona,a haka ya karasa palon mama

Zaune ya sameta suleim na gefenta suna game ita da abdallah,sallama ya musu ya kwanta Shana Shana cinyar mama yana shagwaba sai shafa masa gashi mama keyi tana wani lallabashi,dining ta jashi ta zaunar dashi,da kanta take bashi a baki har ya koshi,

Mama sosai take tausayin dan nata sabo da yanda tasan halin matarsa bata da hali.adduarta kullum Allah masa chanjin alkhairi.Omar yayi aure amma kullum a gidansu yake rayuwarsa,kullum babu Wanda zaice ya taba aure,Rabin kayan sawarsa gaba daya yana room dinsa a part dinsa bangaren mama.bashi da banbanci da gwauro.mama kuwa bata hanashi.

Direct room dinsa ya wuce,wanka yayi hade da sallah ya kwanta sai bacci.iklas kuwa Niki Niki suka shigo gida dauke da kayan abinci dai dai kudinsu.ummi ta kawo musu farar shinkafa da miya hade da salat harda kifi,dan iklas duk talaucinsu bata yarda aci fara da yaji ba sai in suna sha'awa ko da dalili,dan gaskia tana da son cin dadi,ita ta yarda su rasa komai suci abinci me kyau,tunda suna Sana'a kuma suna samu ba laifi shi yasa take musu cefane me kyau na talaka.Rabin rayuwar gidan kaf a hannun iklas take

Wanka sukayi suka zauna hira kafin magrib ta karasa,bayan sunyi sallar isha iklas ta shiga kitchen ta dafa musu indomie da dankalin turawa harda kifi,a baki ta bawa suhaila taci ta koshi,sannan suka ebo littatafansu sukayi karatu,nafila sukayi sannan suka haye gadonsu suka kwanta,kaka ummi kuwa dama a katifa take kwana,wai gadon ji takeyi tayi sama dogogo.suhaila da iklas a katon gadonsu,

Haj rahina tana ta kulle kullen mugunta kawarta na hango suna zuba hirar mugunta a zaune a palon umma,ita da babbar kawarta hajiya binta suna shirya tuggun da zasu kullawa Omar da mama,rahina tace binta ko wajen bokaye zan je ne?daria binta tayi tace share bokaye watarana aikin baya ci,kin San munafukar akwai addua,mufa mata ne ba irin tuggun da baza mu iya kulla musu ba Wanda zai jefa su cikin wani hali,ke in ta kama har gidan nan sai sun bari,tsabar iya tuggu da sharrinmu,haba rahina kin manta mu ne, tun muna yara kin San tsiyarmu.daria da shewa sukayi hade da tafawa, su sadiya yaran rahina sunaji sai murna suma sukeyi suna tafawa,dasu ake shirya komai.sai kara zugasu sukeyi,

Iyaye da dama na kuskure manya manya duk wani gulma,munafunci hassada sai a dingayi gaban yara,ana daria kaga wasu har tafawa sukeyi da yaransu mata ana cin naman wasu,duk iyaye masu haka su sani suna gurbata tarbiyyar yaransu,da haka zasu taso suma sunayi,kuma uwa ko yaushe batawa yaranta fada,tana wasa da daria ko yaushe da yara baza su taba jin maganarta ba,rainata zasuyi,ba a hana hira wasa da Jan yara a jiki ba amma a dinga sanin kalar Wanda za ayi,kuma wasa ba ko yaushe ba,shi yasa za kaga yara na dakawa uwarsu tsawa,ta sasu abu sukiyi, suma fada mata direct baza suyi ba,sai kaga idan ubane an masa da wuri a na rawar jiki,da yace a bari an bari,ba raini,amma mu iyaye mata mu ke zubar da kimarmu gaban yaranmu,matsala iri iri,Allah sa mu gyara.
Chapter 4 · 0% Book details