← Book details Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 57

Sashe 48

Ma'aikaciyar Gomnati Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowannensu part dinsu suka wuce,Suna shiga Mama ta kallesu Babana fada min gaskia me ya faru ban yarda daku ba,ganin Basu Umma Rahina Iklas tace Mama Najja ce fa ta zageni tace min yar tallar Apple and egg shine mukayi fada amma saboda Ya Omar yafi kaunar danginsa ya mareni a gabanta kalli inda ta cijeni Mama, su biyu suka rufarmin wai su ga yan uwa,Mama wai mutum ya daga hannu ya doki matarsa ta sunna ai ya fadi ba nauyi,
Omar mukus yayi yace Mama..... rufemin baki shashasha sosai Mama taji haushin Omar,fushi sosai tayi da Omar,Ummi kuwa tasan dole Iklas Nada laifi a zancen nan amma Mama taki yarda,duk suna zaune Palo kowanne tsit kakeji in banda Mama da ta dage tana yiwa Omar fada, ka samu mace me sonka haka ka fara shirme akan Wanda basu da makiyi kamarka etc Iklas sai taji bata son fadan da Mama kewa Omar, sai taji ya bata tausayi gashi Mama na fushi dashi,Ummi sai Hararar Iklas takeyi, Omar ne yayi magana Mama kiyi hakuri haka mana,ai duk ita ta jawo baki San tsokanarta ba,duka Mama ta danawa Omar a bayansa, me makon aji Omar yayi kara Iklas ce ta gantsare ta saki kara,tare da cuno dan bakinta gaba Mama dan Allah Ku kyaleshi haka nifa kawai fada miki nayi ba dan ayi masa fada ba,sai dukansa kikeyi kiyi hakuri ki kyaleshi dan Allah mama kinji,Iklas harda marairaicewa,a hankali ta tayiwa Omar magana mu tashi mu tafi gidanmu kawai.hangame baki Mama tayi tana salati,Ummi kuwa daria tayi gwara da tayi miki kika gani,na fada miki yaran nan idan kina shiga fadansu kunya zakiji ba yan goyo bane.

Mama tace ga zahiri na gani to wlh Ku tashi Ku tafi tun wuri, tunda sukazo suke samu magana kamar yaran goye cewar Ummi. Da sauri Omar ya mike,Iklas ta dauki Jakarta da gyale Omar ne yace kuyi hakuri Mama....Ku je Allah raka taki gona marasa kunya. Iklas sumi Sumi tabi bayan Omar wai ita kunya.

Sahar ihu takeyi tana kuka da Neman taimako tare da susar gabanta tana kiran Mummy, da Gudu mamanta ta fito tare da Daddy sukayi kanta a gigice,dan danan Mummy ta fara kuka ganin abinda Sahar keyi.
Sunkutarta Daddy yayi ya sata a mota sai asibiti, sunje an basu gado tare da yiwa Sahar Allurar bacci, amma a banza sai da akayi mata Mayan allurar bacci har 3 sannan aka samu bacci ya dauketa.
Tubeta likitoci sukayi wasu tsutsotsi farare birda birda cankam a cikin al'aurar Sahar kuka kawai iyayenta keyi, su Kansu likitocin basu taba ganin cuta irin ta Sahar ba.kowa saida ya tausaya mata domin da Allurar baccin ta saketa zataci gaba da ihu da Susa tana birgima, ba irin kudin da Daddyn Sahar bai kashe ba,magani sukeyi both na asibiti Dana gargajiya, amma abin ba sauki, Daddy ya gaji ya maidata Canada can ma ba sauki.

Tun a hanya Omar ya tsaya ya siya musu gasassun kaji da kayan makulashe tunda suka taho Omar bai kalli Iklas ba itama haka kowanne da tunanin dan uwansa ya masa laifi.kowanne buri yakeyi aje gida ayi wacce za ayi.
Iklas daya room din taje tayi wanka tayi Sallah tana jira ayi isha tana ta azkar dinta, Omar kuwa yana masallaci sai da yayi isha ya dawo, Iklas kuwa wata kwalliyar ta tsantara ta hade cikin wando 3qtr fari da T-shirt ja,ta daure gashinta da Jan ribbom jelar gashin na lilo jambaki ma ja.
Da Sallama Omar ya shigo fuska ba rahma,amsa masa tayi ciki ciki kafarta daya kan tana kallon wani American film a mbc 2,zama Omar yayi a wata kujerar wacce ke facing din tata,sai wani mayen kallo yake binta dashi na so da kauna tare da tsantsan sha'awa. Tasan yana kallonta amma taki kallon inda Omar yake bare ma yasa rai zata kulashi gashi so yake su hada ido amma taki yasan shima yayi laifi kuma mata sai da siyasa ake iya saitasu,dole sai da dabara musamman irin su Gomnati da sukeji da tashen kuruciya.
Tasan Omar ita yake kallo tana sani ta dinga murguda Baki tana fari,sai murguda bakin takeyi taki dainawa, dariya ke Neman kwacewa Omar, suratul Fil ta karanta ta koma ayatul kursiyyu Omar ya ganeta waishi mayene shine take karatu kar ya cinyeta,
Baice mata komai ba,ta wani Dora hannu saman dukiyar fulaninta ta kara dagosu Sama ta gyarasu ta kama rera tsohuwar wakar Hausa ta kwalele,ta dauki wayarta tana latsawa ba tare da ta kalli inda Omar yake ba taci gaba da wakarta wata kalar a hankali tace ka gani ka gani kwalelenka. Gani tayi Har yau Omar kallonta yakeyi mikewa tayi tare da yin wata mika wacce ta rikita Omar, tafiya tayi cike da yanga da karairaya ta je room ta jawo ledar naman da Omar ya siya.
Omar shigowa yayi ya fisge ledar kajin tare da turata baya, a hankali yayi mata amma sai da ta fadi dama a zaune take, Omar kuma a tsugune,kuka ta farayi masa dama Omar hanyar yi mata magana yake nema,zuwa yayi da niyyar lallashinta,ai kuwa Dane bayan omar tayi saida suka tintsire kasa ta shake wuyan Omar bada karfi ba ita a dole shakeshi tayi wai yaji zafi, chakulkuli ya fara yi mata tana hawaye tana daria,tsayawa yayi yana kallon dariyarta me matukar kyau da birgewa,tsawaya tayi da dariar itama sai kuma ta fara sheshekar kuka kwanciya tayi flat a kansa kamar ta hau katifa,ta rungumeshi kam kam taci gaba da rera kukanta bilhakki tana cewa ka.....ka....ka...mare...ni... Ni.... A...a....gabanta....am so sorry to ya isa indai akan mari kike ta wannan fushin tashi ki rama abinki,ba tare da ta dago ko daina kukan ba tace ai....ai...dan...ka...San...ba...bazan....iya.... Ramawa...bane....murmushi yayi kece wifey ba kya jin magana,yan uwana ne fa,ko ba komai suci darajata,dama....dama...haka zaka....ce mana...tunda....ni....ba...yar....uwarka....bace....lika....maka.... Ni...akayi....shine....ka... Min..... Wayo....ka....gama... Shanye... Min.... Zumata....yanzu....ka....tsaneni...yau Omar yaga ta kansa da Iklas taki shuru,taki tashi daga jikinsa kuma.ci gaba tayi amma..ni..a gabanka tace min...me Apple and egg....to baby am sorry tashi muyi magana haba yan matana, ninefa honey ki.

Asmabaffa

Tnx alot readersⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

175-180

By
AsmaBaffa

Ci gaba da lallashinta yayi yanzu fa kika fansoni wajen Mama har dukana tayi kanki kinga kinji tausayina, a kaina kika kekashe idonki gaban Mama ki hanata yi min fada ko?
Ni...ni... Ba tausayinka naji....ba....kawai...dan kar amana daria ne aji sirrinmu....murmushi Omar keyi tare da shafa bayanta yace a'a gaskia kin kara birgeni ba duk mace ce zata rufawa mijinta asiri haka ba kamar yanda kika min,na gode Allah miki Albarka,dadi Iklas taji tayi abun kirki wai ana yabonta.
To tashi kiji wata magana,mikewa tayi ta zauna ta tankwashe kafafu kamar me zaman tahiya.

Goge mata hawayen Omar yayi yana kinga duk kin bata min kwalliyar,hannayenta ya riko gaba daya fuskarsa ba alamar wasa,Wifey in tambayeki? Kai ta daga ae,kina sona kuwa anya?kai ta daga wai ae,magana zakiyi mun,mugun Sonka ma nice number 1 cewar Iklas,Omar ne ya nisa to dole kiso yan uwana,bai dace kina biyesu kuna fada ba,bayan kin San baki da gaskia,yes sun miki laifi kema amma ke kika fara tsokanarsu,ko ba komai duk sun girmeki fa last burn dinta ce kawai bata girmeki ba.

Kina so ace na auri marar tarbiya da hankali,a'a amma ai dai kasan ni bana tsokanar mutum sai da dalili,kuma ai ma kai na tarewa fada tunda ba sonka sukeyi,to na gode sosai kin kyauta da kika tare min kinji,Allah tsundumaki a Aljanna,tana zuburo Baki tace Ameen,Omar yaci gaba bana son tsokana da jaye jayen rigima kin San fada dasu baya mutuwa fa,to ni tsoronsu nakeji ai ni in fada ma banki mu kwana muna yi ba,kasan sunana kuwa sanda ina jss case buyer ce ni,cewar Iklas

Siyen fada nakeyi a schl na tarewa mutum a bani kudi,nayi business na fada,to ai naga ke ba karfi gareki ba kuma matsoraciyace tsokana kawai kika iya,dariya Iklas tayi tace lallai na waje baiga gari ba,baka San muguntata bane in na dinga hadawa mutum gadar zare sai ya raina kansa kaga dai yanda na tsillewa Sahar mazaunai ko? to ba komai nayi ba yanzu kawai a nutsatsiyata ka aureni ka godewa Allah da har kai zan hada a marin nan da kamin,yanzun ma kawai dan kai mijina ne kuma kaci sa'a ina sonka .

yanda take tawa Omar kuri sai tsoron tsiya.naji case buyer cewar omar yanzu dai Allah kinji na rantse na kuma ji ko a labari kinyi kokawa da wata musamman yan uwana zaneki zanyi ba mari ba,
Bakwa son Zaman lfy,yan uwana daban ke matata daban,karama dake sai rigima,idan karfi kikeji,duk sanda kika ji kina jin karfi kizo ki nuna minshi on bed,kuma dole ki so yan uwana idan basu sona case dinmu daban kema namu dake daban ne, na gama magana.kekebewa tayi zatayi kuka hannunta ya saki je kiyi kukanki ba a jikina ba.

Ni kuma Marin da kaminfa?haushi kika bani kin bari anji miki ciwo a banza a hannu,jiba hannunki yanda aka cijeshi kin San yanda naji ne danaga jininki na zuba,kai dai kawai kace kafi son Yan Uwanka zaka min wani wayo, sai kiyi kuma ai Omar ya furta, insha'allah ni kuma bazan kara zuwa part dinsu ba,tana dan coko lips tace kayi hakuri Allah huci zuciyarka bazan kara tsokanarsu ba,in dai akan yan uwanka ne, amma bazan zauna dagalolo a dinga cin mutunci na ba,saboda gani me hakuri,bazan dauki raininsu ba,ni tunda na aureka ai na zama Antynsu amma ko gaisheni basuyi ba,kai kadai suka gaisar,me yasa baka nuna musu muhimmancina ba?idan gaskia kake so a maganganunka,ka fadawa wannan me jikin talo talon indai ko kallona ta kara yi sai na zubar mata da hakoran gaba, daria Omar yayi lallai manya kalli hannunki yanda ta cijeki fa amma kike kurin zubar da hakora.
Chapter 48 · 0% Book details