← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SLMHAB HOSPITAL babban asibiti ne a wannan ƙasar Japan , kowani babba anan ake kawo su duk iya girman mai girma kuwa ,don itama mai asibitin babban ƴar siyasa ce a wannan ƙasa ,da ta tara masoya ,kowa yana mata fatan hairan saboda don talakawan ta.... Waiting room Zainabu ta zauna Habab yana amsan wasu files yana cike mata can ɓarayi da ban....wanda yana yi idon shi na akan ta , don duk yana lura da irin kallon ƴan iskan maxan nan ke mata ....don ya riga da yasa su a zuciyar shi kawai ƴan iska sunan su ,tun da suna kallon masa Zainabu........wucewar matar ne yasa nurses jah baya wasu na cigaba da ayyukan su ,cikin zafi don matan tabbas macace mai kamar maza....fuskar ta cikin farin medical eyeglss yake da ya mamaye rabin fuskar ta , sai dai kayan jikin ta shiga ce ta mutumci.....riga da skirt na English wears ,wasu na riƙe mata da Wayoyin ta da lapcourt. Da'alama ƴar gayu ce ta ƙarshe .... Ganin wucewar ta yasa Zainabu saurin miƙewa tana bin bayan ta da sauri ,ta na ƙwaɗa kirar " MAMA!!! , Jin hakan yasa dukkan ilahirin mutanen hankulan su ya dawo kanta ciki harda Habab , da yake shirin mata mgn kawai yaga ta fice da gudu ,wannan yasa nurses da doctors bin bayan ta don sun san patients ɗin sune akwai yiwuwar bata da lafiya....Habab ne shima ya rakata yana bin bayan ta haɗi da kirar ta "Zeee!! Amma ina wannan matan take bin bayan ta ,da ita sam bata san da Zainabu n Bama". Doctor salmhab ce taji kawai an rungume ta ta baya an ƙanƙane ƙaƙaammmm sai sauke numfashi Zainabu take a hankali..... Wanda cikin sauri da kuma mmiki Doctor Salmhab ta juyo tana kallon Zainabu cike da kallon " Aina kika Sanni". Hawaye ne ya hau bin kuncin Zainabu , cikin Muryar kuka ta ƙara cewa " Mama....!!! Kece Maman Habab ko??? Wani irin bugawa ƙirjin doc. Yayi wanda cikin sauri ta sauke glss ɗin idon ta dai dai Habab yana ƙari sowa wurin". Kece kika haifi Habab ko????.................

*Littafin ƘWRTN MNY na kuɗi ne normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 ,zaki iya Turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account ɗin 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank*

_Masu fitar mun da littafi suna ɗaurawa a facebook da sauran wurare don Allah ku bari ,bana facebook amma ana yawon faɗa mun ,kuma Amin screen short , amma don Allah badon nuna Mmn teddy,adaina.... wannan shafin bonus ne ku yawata shi ko ina tncuuu🤝🏻🥰_

*Mmn teddy🧸*
[6/28, 07:15] my number: *🕊️ƘWRTN MANYA🕊️*

_*Mmn teddy*_
26
*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932 Tncuuu dearies🤝🏻*

*****

Tsayawa dukkanin su sukayi kowa na kallon ɗan uwan sa , kamin cike da mmki da Muryar kuka matar ta kalli Habab tana cewa " Habab !! Wani irin kallo yake mata da Zainabu ta kasa gane ta meye". Rungume Zainabu Tayi tana kuka ,kana cikin sauri ta nufi Habab wanda fuskar sa tayi kinini ,tamkar wanda aka aiko masa da Saukar ajalinsa. Ganin Doc.Salma na Son ƙoƙarin hugging ɗin shi yasa Habab Saurin jah baya ,yana ɗaga mata hannu na kar ta iso inda yake". Tsayawa tayi cakk tana kallon shi idon ta na tsiyayar da wasu irin ƙwallah masu zafin gaske ,tana bin Habab da kallo yau shine ya girma haka? Ashe dama zata gan shi a rayuwar ta???kamin tayi magana ne taga ya damƙi hannun Zainabu yana janye ta daga gareta ,wanda yasa Doctor saurin riƙo Zainabun da itama hannun ta ta riƙe". Habab Pls Mahaifiyar kace fah? Don Allah ka barni nidai bazan bika ba!! Juyowa Habab yayi a fusace fuskar sa da hancin sa har wani jah da saukar ɗigar zufa yake yi na masifa.... Wannan yasa Zainabu saurin cika Hannun ta ,tana kuka ,itako Doctor salmhab sam ta kasa Cikata riƙe ta tayi ƙaƙammm ,don batasan waccece ba a rayuwar Habab ,amma ko ƙanwar sace ,tasan ita ta dabam ce ,bata biyo halin uwarta Hjy Luba ba". Wani irin fixgeta yayi wanda sam ya manta da hannun karayar ta , don shi ya riƙe ,kuka ta sa masa tana riƙe hannun ,jin wani irin raɗaɗin azaba take , wanda cikin sauri securities ɗin wannan asibiti suka rufe mu , cike da tuhuma suke tambayar Habab waye shi a wurin Zainabu , yake shirin illata ta ,ba patients bace??? . Cikin masifa Zainabu da Doctor salmhab sukaji ya katse su da cewa " Ina ruwan su , matar shi ce ,babu abin da ya shafe su ,duk wanda yayi ƙoƙarin wani abu , wallahi sai yayi Shari'a dashi har ƙarshen rayuwarsa .....mmkine ya kama Doctor Wanda yasata sakin baki tana kallo Habab ya tafi da Zainabu , wanda jikin Doctor van da rawa na firgicin babu abun da yakeyi....fashewa da wani irin kuka tayi tana nufar moton ta cikin sauri haɗi da shigewa tana barin farfajiyar Asibitin....

****

Wallahi bazan yarda ba ,sai mun zauna babu inda zamuje !! Kawai saboda kagaaaaa....keeeee!!!! Taji ya mata maganan yana saka mata gigitaccen tsawa ,wanda yasa Zainabu yin shiru don dole....Ki haÉ—a koman ki na baki minti biyar ,idan kk wuce kuma zamu koma gida a haka babu koman ki....ina ruwan ki Zee?? Mom É—in a ce , kuma bana son ta ,bana son ganin ta a rayuwa ta".

Cike da Muryar kuka tace" Me yasa Habab? Duk lalacewar Momy mahaifiyar ka ce ,baka da bayan ta , baka da kuma tamkar ta a rayuwa , itace dai! Me tayi maka a rayuwa haka? Yo ko kasheka tayi bata cancanta ba Habab, ka mance da naƙudar da tayi kamin ta haifoka zuwa duniyar nan Habab ,ita fa nata rayuwar ta miƙa shi ga Allah ,wataƙil ta rayu wqtaƙil ta koma gare sa...amma duk ta jira don kawai ta kawoka duniyar kayi rayuwa kaman saura! Habab !!! Ta kira sunan shi da ƙarfi tana tsiyar da ƙwallon mai zafin gaske....ka So Momy ka ƙaunace ta baka da kowa bayan ita a rayuwa".
Kuma mgnn tafiya babu inda xani sai an gyara mun hannu na , ayau ka kira likitoci suka ɗorani ,to xan bar Japan ,amma ka sani xakayi nadamaaaaa....kamin ta ƙare maganan ne ya ɗauketa da wani shigaggen mari ,Wanda yasata jin komai yayi mata ɗifff na mintuna ,kamin ta dawo hayyacin ta ne taji yana cewa " Kar ki sa kema na ninnka tsanar da nayi maki ,akan wacce tafi ta da! Son ki nakeyi , ke ko Hjy Luba ce ta faɗa mun wannan maganan bazan ɗauka ba xan iya komai a kanta".

Komawa taga yayi ya zauna a Sofa ,ita ko kuka ta rushe dashi tana zubewa gwiwowin ta ƙasa , Habab na gaji to kawai ka maidani gidan mu! Ka taimake ni , bazan iya zama da mai taurin zuciya da baƙin hali irin naka ba...wani cutan zata iya kamani marar maganin. Kallon ta bai kuma ba ,sai gani tayi ma ya aje ruwar mayen sa giya yana dubawa haɗi da ƙwalɓewa". Miƙewa tayi da sauri tana nufar innrroom ,don tana bala'in takaicin ganin shi cikin wannan yanayi......

******

Itako Doctor salmhab tsawon lokaci ta rasa meke mata daÉ—i a cikin gidan ta , wannan yasata juyawa tana nufan asibitin ta haÉ—i da sawa a binciko mata file É—in Zainabu....bin sunan take da kallo ,sai hawaye n da take gogewa da hankie". Zeee Habab sunan da tagani kenan , Zeee!! Ta kuma nanata sunan , bin adreess É—in tayi tana É—auke shi ,kamin ta koma cikin sauri ta nufar moton ta don nufar gidan su Habab , kaman yanda tagani....

Ƙarar Door bell Zainabu take jiyowa a inda take ,wanda Habab da yasha yayi tatil sai busar sigarin sa yake motsa bakin sa ya kasa saboda baƙin cikin da ke masa yawo da zuciya". Fitowa tayi tana nufar kofar ,nan taji Muryar sa yana katse ta da cewa " Gida kika ce na maidake ko? Wurin su Umma? To xan mai dake ,Ni kuma nayi rayuwata Ni ɗaya. Kuka tasa mai ban tausayi kana tace " Habab bazan iya rabuwa dakai ba , pls don Allah ka Soni ko kaɗan ne, itama Mom ka So ta....a sannu a hankali zaka gane Mom bata da laifi a komai".

Meye ba laifin ta ba Zainab? Baki san komai ba!! Ƙofan ne suka ga ya buɗe ,wanda Doc salma ce ta shigo ,hakan yasa Habab juya baya don bai ma Son buɗe ido n sa akan ta". Na shiga uku na!!! Habab!!!?? Zainabu tayi maganan tana takawa zuwa inda yake". Bazan saurare ki ba Zeee har sai Mom tabar nan ".

Zan fita Habab ,amma ina roƙon ka ,ka bari na gyaraa hannun Zee. Saurin kallon ta Zainabu tayi dama ta iya " Hausa?? Tambayar da take mawa zuciyar ta kenan!! Juyawa Habab yayi a fusace yana barin wurin yana barin Zainabu da doc Salma da hawaye kebin kuncin ta nan tsayeeee......

*Littafin ƘWRTN MNY na kuɗi ne normal group₦300 ,Vip group₦500 Spc ₦1000 zaki iya Turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki Turo ta wannan account 6037312299 mohammed Aisha keystone bank*

Mmn teddy🧸
[6/28, 15:34] my number: *🕊️ƘWRTN MANYA🕊️*

_*Mmn teddy*_
27

*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932 Tncuuu dearies🤝🏻*
[6/28, 15:35] my number: *🕊️ƘWRTN MANYA🕊️*

_*Mmn teddy*_
27

*Night update🥱💃*
*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932 Tncuuu 🤝🏻".*
Chapter 7 · 0% Book details