← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana faɗin haka tana takowa inda zainabu ke riƙe da marar ta da taji yana wani irin juya mata, numfashi ta sauke da ƙarfi ,wanda ya maido hankula n su Hjy Luba nan suka ga jini na bin ƙafarta ,alamun ɓari tana da ciki yana shirin fita ko ma ya fita.....baya tayi luuuuuu idon ta na rufewa ,wanda yasa Mom Salma saurin riƙe ta ,tana ƙara kirar police da sauri Hjy Raliya ta kama Zainabu suna ficewa da ita daga falon haɗi da nufar farfajiyar gidan ,wanda Tuni aka nufi da Daddy asibiti don ceto rayuwar sa..................

*Babban sirrin qamshi kisamu hadadden gaske Wanda y Sami qwararriyr me sarrafashi daga very expressive product like arabian,rasasee ajmal,and alharamaiin.masu asalin kyau d inganci er'uwa karkiyi sake d attitude naki qamshi shine ke bayyana ke wacece ko kinyi ado ko bakiyiba. Mummies kujini dakyau the beauty of turare is speak to ur hearts and hoply to someone else...namiji na iya manta komi amma Banda special qamshin ki daya Saba jii na yauda gobe farkon matakin Jan hankalin miji gareki shine y shaki qamshin daddadan turarenki.🥰💃🏻💯 Akwai wasu sirruka ajikin qamshi turaren da akeyinsa da wasu daga cikin itatuwan bishiyoyi ko saiwar wasu bishiyoyi Wanda ake Kira da (eriqh) wannan itatuwa ba kowa ya iya maintaining dinsu subada abinda ake bukataba da wannan zakuga d yawan masu turaren wuta insunyi turare yake qauri Wanda dazasu dage su sarrafashi yanda y kamata Ina me tabbatr muku ba boka ba malam kinadaga cikin gidanki Zaki siye zuciyr oga walhi kusamu lada hankali kwance💃🏻💃🏻💯 Wanda mu haka shine birinmu insha Allah. To ku marmatso kusa kuji shahararriyar Kuma hamshakiyr mesai da turarukan wuta wato UMSAD INCENSE ta tanadar muku turaruka masu inganci Kama daga jiki,gida,Kaya, turarukan tsuguno, turarukan daake shafawa a gashi batare da sunbawa gashi matsala ba ds.kudai kawai ku tuntube ta 08028827241 /09033791049 karku manta UMSAD INCENSE jindadinku shine namu 💯💃🏻💃🏻

*Littafin ƙwrtn mny na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932 "Tncuuu".🤝🏻*

*Mmn teddy🧸*
[6/30, 14:39] my number: *🕊️ƘWRTN MANYA🕊️*

_*Mmn teddy*_
32

*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932🤝🏻*

Mutane da yawa na tambaya na littafai na , akan wai na basu ko a tunanin su free books ne ban dai sani masu ba , Ni abun ma sometimes dariya yake bani wallahi🤣🤣 wai sai kawai kizo mun na baki code ɗin littafin ,nace maku na kuɗi ne , wasu ƴan anacen sai su rinƙa cewa " Ai suna dashi password ɗin kawai xan faɗa masu😹😹 to ke kika rubuta littafin ko Ni?? Haba don Allah , maganan gaskiya littafan Mmn teddy na kuɗi ne duka kaman su:
Ƴar aikina
Ƴar waye
Dijama Æ´ar Fulani
Bafullatanan Ruga
Siyasata
Kawaliya
Walijaam
Gidan ƙwarata
Habibi da'iman
Bintoto
Gidan zaurawa
Da dai sauran su ,Gamai buƙatar samun su ,zai iya mun mgn ta private . Gasunan dai da wanda ma ban faɗo su ba, duk dai na kuɗi ne plz...

******

Haka Hajiya Salma da Adda Raliya suka nufi asibiti da Zainabu cikin gaggawa. Tuni akayi emargency da ita ,wanda kamin ƴan mintuna tuni likitoci suka rufa mata , kowa na ƙoƙarin ganin sun ceto rayuwar ta....don a halin da take ciki komai ka iya faruwa da ita". Kai komo Dr Salma keyi kamin ta buƙaci ruwa don tayi alwala takai kukan ta ga Allah , yayi masu maganin duk wata damuwa".

Ɓangaren Alh Ahmadu kuwa duba da ƙwararrun likitocin da suka rufa masa ne yasa nan da nan suka shawo kan matsalar tasa ,tuni suka samu dai dai ruwar numfashin sa ,sai dai Oxcygen da aka saka masa sakamakon Guba da Hajiya Luba ta basa , wannan yasa numfashi n sa da ƙyar suka samu daidaituwar komai". Habab bai dawo hankalin shi ba sai da aka ce masa mahaifin sa ya farfaɗo kuma zai iya cigaba da rayuwa inshaallh". Wannan yasa shi sauke ajiyar zuciya yana hamdala ga Allah . Abun da ya ɗaure masa kai shine tun da suka isa asibitin ba Hajiya Luba ba labarin ta , haka ma ba Sobreen , Shema'u ce da Safiya ,wanda suna suna jin ance Zai iya cigaba da rayuwa nan suka silale suna guduwa daga Asibitin.

*****

Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un ,shikenan Ammie wallahi kin cuce mu! Yanxu ya zamu yi ,gashi kinyi yunƙurin kashe san ,amma bai mutu ba , kar mu tashi ba tsuntsu ba tarko mana , mu bamu ci dukiyar mahaifin namu ba ,kuma bamu ci na Habab ɗin ba ,Shema tayi maganan cike da hasala . Jikin Hajiya Luba tuni yayi sanyi ta rasa ta ina zata fara ,tabbas tasan ƙarshen duk wani sharrin ta ne ya zo". Sobreen ne cike da kuka tace " Ammie me yasa to baki haɗa su su duka kin basu guban ba? , Kalli fah Zainabu har cikin Habab take ɗauke dashi , yanxu ya zamu yi Daddy ya rufa asiri komai kar ya tona???. Cewan Sobreen tana juyawa ga Hajiya Luba dake girgiza kai cike da jin ɗaci tace " Ban taɓa sa hannu a abu ba'ayi nasara ba , amma shigowa r wannan yarinyar ta ruguxani ta lalatani, wallahi bazai sabu ba , dole cikin ɗaya za'ayi ɗaya.....Dole Nasan duk yanda xanyi Alh Ahmadu ya mutu a yau ,ko da nawa ne xan biya don ganin hakan ya faru".

Habab ne ya shigo falon fuskar shi a haɗe wani irin gumi ke karyo masa , mamaki ne ya kama sa , ganin sa yasa su duka miƙewa kowa tana rarraba ido na mare gaskiya". Ammie da gaske kece kike ƙoƙarin kashe Ni da Daddy? Wai ba mafarki nakeyi ba ,Ammie kece dai?? Yayi Magana n cikin wata irin murya ,kansa na sara masa ji yake tamkar zai fashe.......shigowa Hjy Raliya tayi tana goge hawayen idon ta kana ta dafa Habab tana cewa " Kayi kuskure Habab daka yarda da Ammie , Ammie bazata taɓa Sonka ba , tun da ba ita ta haifeka ba, kuma bata ƙaunar Mom Salma". Ka koma ka ba Momy haƙuri akan abun da kayi mata , haka yarinyar mutane da bataji ta gani ba , kayi mata wannan tijara".

Ke Raliya zan tsine maki ,yanxu da maƙiyana ne kika haɗa kai Raliya? Wallahi yau ina baki wasa ba zan tsine maki ". Tsinuwar ki bazata taɓa kama ta ba Luba!! Suka ji Muryar Daddy ya katse su da basu san ta ina yazo ba.....a keken marasa lafiya a ka ƙariko dashi tsakiyar falon. Hajiya Luba na riƙe ki tsakani da Allah ,ashe dama tuni don wani abu nawa kike zaune dani ,kina jirar wata dama ce , sai yau kika samu kika aikata ,kuma saboda zalunci ki kika laƙaba mawa yarinya bataji bata gani ba. Kije Hajiya Luba bana son ganin ki dake da duk wa'annan yaran naki , sunemi uba ba Ni ba , Kallon DPO Bashir yayi kana yace " Ku tasa su subar mun gida na ,bance gomnati tayi masu komai ba ,amma Allah zai masu don zasu ga sakayya inshaallh".

Kasa motsawa Habab yayi kaman an Dass shi ,wasu irin ƙwallah ne kebin kuncin sa ,wanda rabon da yaji su ya manta a rayuwa . Haka Cike da ihu aka tasa Hajiya Luba da gayyar ta suna ficewa daga gidan Alh Ahmadu , kaman wasu korarru.... Kamin su fice ne Ɗahatatu da taji labarin komai tuni ta shirya kayanta tana bin hanyar ƙauyen garin su".

Haka ma'aikatan gidan kebin Hjy Luba da Æ´aÆ´an ta da Allah tsine ,da jin haushin su akan abun da suka aikata ,ana masu alawadai....kamin kace kobo gaba É—aya Lagos ta É—auka kan abun da mata sukayi mawa wannan shahararren Attajiri wato Alh. Ahmadu Billionerer. Kowa da abun da yake cewa " kafofin sadarwa ba abun dake kai kawo sai hotunan Hjy Luba da faÉ—in abun da ta aikata mawa mijin ta da Æ´aÆ´an ta , har maganan Dr Salma sai da ya shigo kowa na binsu da ala wadai.....

Tsawon kwana biyu Habab ya kasa fita ko nan da can , kullum yana ɓangaren shi abun duniya ya ishe shi....Saif yazo shida Sadeeq ba adadi amma ina ,ba halin da suke ganin shi sai a na shan barasa da busa sigari kullum yana cikin wannan yanayi . Bashi da aiki sai na tunanin wani hali Zainabu ke ciki? Duk da Adda Raliya ta shaida masa da tana lafiya sai dai tayi miss carriage... So yake yaje yaga su amma kuma bai san wani magana zai faɗo bakin su su duka ba , don yasan tabbas a yanxu ko so hauka ne Zainabu sai tayi fushi dashi , addu'a r da ma itace Allah yasa bata daina Son shi ba a zuciyar ta.

A ranan rahadi ne Adda Raliya ta tsare shi akan cewa " Ya yake ciki maganan auren sa da Sobreen ,bai bata amsa ba fache miƙewa da yayi yana nufar bedroom ɗin sa ,can sai gashi da takarda yana miƙawa Adda Raliya , na sake ta tun a ranan bana jin xan iya zama da ko wacce mace in dai ba Zainab ba". Ita kaɗai nake So Adda Raliya,ya xanyi ta dawo gareni ? Ina Son Zeee ina jin komai zai iya faruwa da Habab indai ya rasa ta a rayuwar shi . Rarrashin sa Adda Raliya ta hauyi , don ita kanta ta rasa tayaya zata shawo kan Mom Salma .

******
Chapter 13 · 0% Book details