← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 24

Sashe 1

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

[6/24, 13:14] my number: 21

Wannan wani irin zuciya yake dashi ne?? Mtseww mai zuciyar dalma kawai". Magana kike yi? Taji Muryar sa ta kuma katse ta...kama bakin ta tayi saurin yi kamin cikin sauri ta girgiza kai tana cewa " A'a ba magana nayi ba". Tayi maganan tana nufan dreesingmirrow don ta kimtsa jikin ta. Shafe jikin ta tayi da mayuka masu daɗin ƙamshi ,kana ta tayi saurin ficewa zuwa falo". Kallon ta yake a sace har ta fice daga bedroom ɗin yana ganin yanda take tafiya ,dauriya ce kawai irin nata , rauni biyu kenan ga hannu ga kuma wannan babban al'amari". Cigaba yayi da yin binciken sa ta laptop don bai taɓa shiga ƙasar Japan ba ,wannan shine karon sa ta farko ,amma kuma Sosai yake jin nishaɗi a wannan rana ,wanda ya rasa na meye?". Sai da yayi kusan mintuna sha biyar kamin nan tuni ya gama duk wani abu da yake Son gani,falon ya fito yana hango Zainabu a tsakiyar falon ta baje abucucuwa daban daban ,kaman wanda ta shekara guda bata ci ba . Zama yayi a kujerun falon ,yana bin kallon plsma ɗin tashar G.M.A , ita ko Zainabu bi takan sa batayi ba, tun bai bi ta kanta har idon sa ya dawo kanta ,taɓ ɗi yaga yanda Zainabu ke bige abinci ta sha lemu taci nama...kallon ta yayi kawai yana giegixa kai a zuciyar shi yana faɗin " Wannan wacce irin yarinya ce mai cin tsiya? Wai dama mata nada irin wannan cin Abincin?? . Wai bawan Allah wannan kallon fah? Ai sai ka sani na ƙware". Zainabu tayi maganan tana fiddo da idon ta cike da tsiwa". Hummm ɗan taɓa baki yayi yana kai hannun sa haɗi da shafa sajen gyefen fuskar sa ,shi sam baijin cin komai ,jin sa yake a ƙoshe tun da ya samu abun da zuciyar sa ya daɗe yana marin.... lulun idon sa ya watsa mata kamin ya buɗe baki yana murmushi da sai da Hushiryar sa ta bayyana yana cewa " ina nan ina mmki ne". Mmki ?? Na mene?? Zainabu tayi maganan tana yagar hanta tana lumtsumawa a baki". Haɗi da raunata tamkar wacce take jin haushin ci ko akayi mata dole". Gyara zaman sa yayi yana passing ɗin ta ,don ji kawai yayi yana Son yaga ya baƙanta mata. Wannan cin Abincin naki ai dole nayi mmki,ban taɓa ganin mace mai ci irin naki ba! Yayi mmgn yana mata dariyar rainin hankali . Amaimakon yaga ta ɗauke fuska ,ina sai gani ma yayi ta wani kece masa da dariyar mayar masa da Aniyar sa ,kana tace " Aiko yau ka gani akaina Ni Zainabu, shiyasa indai ƙarfi ne akwai Ni dashi kamar Shari'a". Waigawa yayi kaɗan yana kallon gyefen sa ,kamin ya taune lips da ɗan ƙarfi yana jin ba daɗi da baiga komai a fuskar ta ba. Kenan bata ji haushi ba! Yayi maganan a zuciyar shi". Hummm iska ya furzar yana saukowa ƙasa carpet ɗin da take ta tanƙwashe ƙafa , kallon ta yayi kamin yace " Wacce mai ƙarfin? . Cuno masa baki tayi don ta fahimci cin mutunci yake Son yayi mata". Ina tambayar ki ,wa ɗazu yayi ta kuka da magiya?? Haushi ne da kunya duka suka kama zainabu ,kawar masa da kai tayi tana dakatawa da cin komai". Wannan yasa shi jin daɗi da sai da fuskar sa ta nuna". Babu amsa? Ya kuma mata maganan yana tallabo Fuskarta tana fuskantar shi. To bari yanxu mu ƙara sai inga da Ni dake wane yafi ƙarfi!! .

Matsawa tayi saurin yi tana ɗaga hannun ta tana shirin bugawa da royals ɗin gyefen ta. Saurin kai hannun sa yayi yana riƙowa ,kamin ta kalle shi tana jin bugu , kai kaiiii , Wayyo Ni Zainabu ,Allah ya haɗani daaaaa wai menayi maka ne a rayuwa ka tsaneni ? . Hannun shi na riƙe da nata yace " Au har kin manta , ma me kika mun?? Hummm". To baya wuce ba ko ba'a yafiya a rayuwa ,kuma Ni zafi ne dani ban yarda da wargi ko raini ba". Humm sannu mai zafi, kuma sai nagan ki ɗazu baki ya mutu ba kukan ,don kin san ko kinyi a banza. Wannan mutumin tantiri ne ,wai shi ko kunya ma bataji yake wannan maganan". Nima bari na nuna masa ƙaryar tantiranci . Ehhh ɗin wallh na tsani iskanci ". Ni kuma ina So". Ya bata amsa yana zama kusa da ita ,cikin sauri tajah baya tana cewa " Ni kuma na ba haka nake ba". Ni kuma haka nake". Mtseww ɗan tsaki tayi a hankali,wanda yasa shi kai hannun shi yana murɗe bakin ta sai da tayi ƙara sannan ya saki, cikin wani irin murya mai kama da raɗa yake ce mata" yanxu fah komai da kike ji da taƙama dashi ya ƙare , saboda na gane su kuma na mori daɗin su". Kaga bana son irin wannan maganan Habab , komai bai ƙare ba , kodon kaga nace ina Son ka?". Shiiii kar ki ƙara wannan maganan ,ai ba soyayya a tsarin lissafin rayuwar Habab".

Kallon sa tayi kamin tace " Baka isa ba ,dole ka So Ni ,yanda nake Sonka". Saboda ka naƙasa mun hannu na, kuma kazo ka rabani da mutunci na , duk ya tafi a banza kake nufi?? Tayi mgnn cike da tsiwa da yarinta". Murmushi yayi kana yace " Kawai sha'awar ki nake bayan nan ba komai a zuciyata game dake ,wannan yasa ma na ɗaga maki ƙafa daga azabar dana tana da maki. Ai haka ne ?? Zainabu tayi maganan tana miƙewa daga tsaye hadi da kama kwankwaso". Murmushi yayi cike da duniyan ci yana miƙewa shima haɗi da rumgumo ta yana manna shi da jikin shi.....Duk cin da kike cewa kina dashi ,duk na banza ne ,kedai na ɗaya ba wani ƙiba ba , gashi ba ki da ƙwari". Fixgar jikin ta tayi daga nashi ,tana masa wani irin kallo , Habab ka sani indai sha'awa ta kakeji yanda kace ,to wallahi Ni kuma Zainabu ka bar ƙara taɓa jikina bare har kayi wani abu ,don dama niba haka nake ba ,nadai tausaya maka ne saboda naga kana shirin mutuwa....Saboda Son Zainabu na gab da ɗaukar rayuwar Habab wannan yasa Ni na baka kaina da jiki na ,amma ka sani daga yau wallhi ba ka isa ba,sai dai kaje ka nemi wata.

Shiru yayi kaman bazai mata mgn ba ,sai kuma yace " Okay amma kin san xan samu irin ki ɗari idan naso ko? . To shknn naji kaje kaso ɗin". Ni kike mawa rashin kunya?? Yayi maganan yana shan murr fuska babu alamun wasa. Ƙwallah ne ya ciko idon Zainabu na rainin hankali n habab ,tasan ta cika matsawa zai mata komai ,hakan yasata cewa " Ai ba rashin kunya nayi maka ba ,gaskiya na faɗa maka , wallahi Habab indai baka furta cewa " Kana So na da gaske ba , kuma a gaban mutane biyu ba baxan taɓa baka jiki na ba". Tana faɗa masa hakan ta juya fuuu tana nufar bedroom ɗin ta.
Chapter 1 · 0% Book details