← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana gyara Fillon dake bayan ta ...lumshe ido tayi tana tunanin abubuwa da yawa da suka faru tun daga farkon haɗuwar ta da Habab da yanda ta sharara masa mari a mall wai taje siyayya da kuɗin hannun ta da basu kai sun komo ba... Dariya ta keche dashi tana girgiza kai kurum. Ɓangaren Safiya kuwa tun da wannan abun ya faru labari yayi tangwarma har gida jen Auren su ,yanda kowa labarin da yake bada wa akan su daban....Masu cewa sun haɗu zasu kashe mahaifin su saboda son abun duniya su suka fi yawa. Wanda jin hakan yasa a lokaci ɗaya mazajen nasu suka basu takardan sakin su da cewa " Suma da suke zaune dasu ba don Allah bane , Suna samun wata dama zasu idda nufin su akan su. A kwana uku Hjy Luba da mabiyan ta sun rasa inda zasu saka kansu ,duniya tayi masu faɗi matuƙa ,kullum a cikin zullumi da fargaba suke , ga baƙin cikin tijarar da Mahaifiyar Sobreen tayi masu , don koda suka je gidan ta da sunan ta basu mafaka , sai korar cin mutunci tayi masu kaman bata taɓa sanin ɗayan su ko su duka a rayuwa ba . Cewa ma tayi a subar mata gida tana lallaɓa auren ta kar su zo su kashe mata , hummm tabbas Hajiya Luba a lokacin tasan meye rayuwa ? Musamman idan kana dashi ka dawo babu! , Shema'u ce mai'aikaciyar asibitin gomnati under federal wannan yasa ta sama masu gida a cikin Staff couters . Don babu ɗayan su da ya mallaka gida na kansa, a tunanin su kawai Alhaji Ahmadu na mutuwa zasu danni arxiƙi ,gida jen sa da koman sa nasu ne. Sai dai yanxu duniya ta juya masu...wannan yasa a ɗan kwanakin nan har rama sukayi na wahala da tashin hankali. Ana haka a satin aka kori Shema'u daga aikin nata , wanda wannan yasa Hajiya Luba har suma tayi nan take gauuuuu....a dai asibiti ta farfaɗo tana kukan nadama da baƙin ciki na rasa inda zasu nufa kuma!
******
Bayan Mom Salma ta amince da komawar Zainabu ga Habab ne , kwatsam a wannan dare akayo ƙirar su daga Lagos zuwa KD duba ga wasu miyagun da suka fara addaban mutanen Nigeria , wannan yasa akayi masu kirar gaggawa don ɓadda wannan ɓarakan". Da subahi bayan fitowar sa masallaci yake sanar mawa Daddy , haɗi da sanar masa da tafiyar tasa kamin gari yayi haske , duk da jirgi zai bi zuwa Kaduna". Nan Daddy sosai yayi masa Addu'a Allah ya kaishi lafiya ya cimma abun da ya tafi nema". Gari bai gama Haske ba ya nufi Gidan Mom Salma da fitowan ta kenan falo daga bedroom ta ganshi zaune cikin shigar sa ta kaki , komai nasa a ready yake ,alamun tafiya ". Wani sanyi taji a ƙirjin ta ganin sa cikin shigar da tafi So tun yana yaro take da burin ganin shi a hakan ,kuma gashi yanzu Allah ya cika mata burin ta .. ɓangare ɗaya ne na kuma zuciyar ta ke mata fargaba da tambayan ina Habab zai tafi da wannan sanyin safiyan??". Sojana kai ne da wannan safiyar lafiya dai ko? Ko kazo ɗaukar Zee ne ,don Nasan ka da naci da axuza. Murmushi Habab yayi yana gaishe da Mom da mata bark da safy , kana yake sanar mata da tafiyar da ta taso masa ta gaggawa". Tsammmm Momy tayi kana tace " To Allah ya dawo dakai lafy Habab ,kaje ka duba matan naka , ina tunanin ta koma bacci gaskiya ,amma kaje ka duba ta". Murmushi yayi mawa Momy kana ya miƙe don ganin Zainabu n da dama hakan yake buƙata". Koda ya shiga bedroom ɗin ta can tsakiyar gadon ya hangota ta rufa da bargo da alamun tana jin daɗin baccin a wannan lokacin. Ƙarasawa yayi yana takawa zuwa inda take kwance yana sa gwiwowin sa ƙasa. Hannun ta ya riƙe a hankali yana matsa mata su ,ko zata buɗe idanun ta ,amma sai ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara sauke numfashi a hankali , murmushi yayi don ya lura baccin yayi mata nisa sosai...wannan yasa shi kai bakin shi yana kissing ɗin saman goshin ta , yana shafa fuskar ta ....kusan minti goma yana a haka kamin ya miƙe da ga tsaye yana gyara mata abun rufa yana fitowa falon Momy don bai son tashin Zainabu n a yanda take jin daɗin baccin nata". Momy taso ya tsaya yayi breakfast amma sai yace " Lokaci zai ƙure masa ,wannan yasa ta bin sa har wurin da yy parking tana masa addu'oi ,kana ya fice daga gidan cike da farin cikin ganin yanda Komai na rayuwar sa ya koma masa tamkar da baya cike da jin daɗi ya nufi airport. Ita ko Momy har ya fice ta kasa komawa ,kawai sai jin ƙwallah tayi na bin kuncin ta , kewan Habab da tausayin sa suka rufe ta , falon ta juya tana komawa , don haɗa masu break fast ,tasan jiya Zainabu kwana tayi tana zazzaɓi ,sai da ta taimaka mata da magunguna sannan taji dai dai , wannan yasata koda ta farka da asuba tana sallah ta koma baccin ta....haka dai Momy tayi ta aikin ta ,tana murmushi haɗi da cewa a zuciyar ta" Allah yasa abun da nake hasashe ya zama gaskiya".
*****
Tafiya sukeyi idon su rufe basa ko ganin gaban su...kashe mun ke zaiyi?? Ina bazai yiwu ba ,ga tukwicin saki ga kuma shi yana shirin kashe mun ke Sobreen?? Tabbas sai na kaisa kotu ,kotun ƙoliii kuwa, muje sobreen ,nemo mana keke mu hau yanxu zamu tafi kotun ƙoli....Ammin Sobreen ke tafe tana sambatu na mahaukata , wanda nesa na hango Sobreen tana gudu haɗi da ƙwala kirar sunan ta Ummma!! Amma ina gaba tayi tana shiga titi wannan abun hawa ya kauce mata ,wancenn ya kauce mata". Isowan Sobreen yasata saurin jan hannun ta tana kauda ita daga titin ,kana tace " Umma sati nawa da barin mu gidan Abba , muyi hakuri komai ya faru damu mu muka jah mawa kanmu". Tayi maganan tana goge hawayen fuskar ta , da tayi baƙi wannan farin fatan da ake ƙafulle dashi ya jeme ta lalace tamkar ba ita ba. Sobreen!! Taji an kirata cike da mmki ta juya ganin su Shema'u da Hjy Luba suma a wulaƙance ". Kunya ne ya kama Sobreen wanda yasata kasa haɗa ido da su sai sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana cigaba da zuban hawaye". Mai ya sameta ??? Hjy Luba tayi maganan tana nufar inda Mahaifiyar Sobreen take ta duƙa tana ta tsintar ledoji . Cike da Muryar kuka Sobreen take basu labarin sakin da mahaifin ta yayi mawa Umman nata , da kuma dukan da yayi mata tamkar zai kashe ta ....wanda ruɗun rabuwar su yasata haukacewa...... Salati Hjy Luba tasa tana rushewa da kuka , wanda suna tsaka da hakan ne Suka ga Umman Sobreen ta razana tana jah baya da cewa " Ni ne Alh nafi'u zai saki?? Bazai yiwu ba sai na kai sa kotun ƙoli tana maganan haɗi da fallawa da gudu tana nufar titi , bin ta sukayi suna cewa " Taimako a kamata a riƙe , amma ina tuni ta shige ma titin , wani babban moto ne yayo kan babban titin ,wanda jah baya su Hjy Luba sukayi suna sakin wani gigitaccen ihu ganin moton yabi takan Umman Sobreen.... Sobreen kuwa ganin hakan yasata zubewa wurin gwiwowin ta ƙasa tana tsaga ihu.... Mutane ne suka rufe wurin ciki harda Alh nafi'u mahaifin ta da dama yake neman ta ta bashi ƴar sa . Da ita kenan masa wato Sobreen ya ɗauki alƙawarin aura mawa koma waye koda kuturu ne".
[7/3, 16:01] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*

****
[7/3, 16:44] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
Chapter 16 · 0% Book details