← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmushi Adda Raliya keyi cike da jin daɗin yanke shawarar da Habab yayi ,kinga dole idan suka ganshi a cikin gidan ya nasu sukuni ,Momy zata bashi matar sa ,kuma itama zata koma gidan mijin ta. To ina zai zauna anan? Taɓ Momy zama da wai xaiyi anan gidan?? Zainabu tace tana kallon Mom Salma da ta tsaya tunanin ya zata ɓullo mawa lamarin Habab". Jin shirun nata yasa Adda Raliya amsan takardan da yaba Zainabu ,tana buɗewa murmushi suka ga tanayi kamin ta sa dariya tana cewa " ZeeHabab kenan! Wani irin dammm yaji ƙirjin ta ya buga ,wanda yasa Zainabu saurin shigewa falon tana nufar inda Habab ya shiga". Tsaye ta taddashi jikin window ɗin falon ,idon sa na akan ƴan tsirarun ma'aikatan dake ƙular mawa Mom Salma da gidan nata.... Tsayawa tayi bayan sa tana bin sa da wani kallo , haushi n sa takeji na mamaye ta ,musamman tuno da kala kalan ixiyan da yayi ta mata , hannun ta ta kalla da yanxu bakace da karaya a hannun ba , sai shafa gyefen fuskar ta da tayi tana tuno da marin da tasha marar adadi a hannun shi....ɗan tsaki tajah mai sauti , wanda kamin yayi magana yaji muryar ta tana cewa" Malam mai kuma kazo yi mana anan? Gaskiya ka koma inda ka fito ,don bana ƙaunar buɗe idanuwan na ga fuskar ka ,bana Son ka bana Son ganin ka Habab". Tayi maganan tana zubda hawaye dake sakko mata. Duk maganan da take masa ko motsawa baiyi ba , sai ma haɗe hannayen sa da yayi wuri biyu". Ganin yana shirin maida ta zauwatacciyya yasa ta ƙara matsawa garesa tana cewa " kaji mai dai nace maka ko?? , To ka sakennn.....Juyowa yayi yana bin ta da wani irin kallo da yasa ta yin shiru sai bin sa da harara take yi .... Me kike cewa ? Na rabu dake ,bakya sona ?? To Naji ,amma Ni ba zan rabu dake ba Zainab , Saboda ina Sonki , idan kuma kika matsa zaki rabu dani , wallahi da ƙafar ki sai kin dawo ,saboda Ni ɗin nan da kika ganni mugu ne ,xanyi maku mugun tan da dole ki dawo gareni ,idan kuma kika sa kafiya kika ƙi to sai dai mu ƙare rayuwar mu a haka ,ke ba miji Ni ba mata. Sakin baki Zainabu tayi tana kallon sa da mamakin ƙiƙirarin da yake mawa kansa na shi mugu ne , zai yi mata mugun tan kenan?? Na shiga uku ,abun da Zainabu ke faɗi kenan tana bin sa da kallo da cigaba da sauraren sa. Ki zaɓi ɗaya ko rabuwa dani ko cigaba da zama dani?....yayi maganan fuskar sa ba wasa a ciki? Yana matsowa dab da ita". Haɗe rai Zainabu tayi kaman bata tsorata da maganganun sa ba tace " Mai ya kawo ka ? Ka fice Habab don Allah ka bani... Ji tayi ya rungume ta yana haɗe bakin shi da nata mutsu² take tana Son ƙwatar kan ta ,amma ina sam ta kasa sakamakon wani riƙo da yayi mata... Mom Salma ce ta shigo don itama tayi masa nata faɗan ,nan taga ya riƙe Zainabu da take son ƙwatar kanta ,amma ta kasa". Kirar Sunan sa Tayi da ƙarfi " Habab! Wanda anan ne ya tsagaita badon ya soba yana cika ta daga jikin shi . Saurin baya Zainabu tayi tana goge ƙwallahn da ya taru mata tana cuno baki gaba da cewa " Wallahi Allah ya isa! Dariya taga yasa mata sam bai damu da ganin Mom Salma ba da itama ta tsaya tana ganin rashin kunya irin na Habab . Kice mawa Mom ta tabani ke,idan ba haka ba kene da kunya , don inaaaa.... Nufo sa Mom tayi nan yayi baya da sauri yana tsagaitawa da maganan tasa yana dariya".

Habab fice mun daga gida! Mom tayi maganan fuskar ta ba wasa . Murmushi yake yana cewa " To ai Mom Ni É—an ki ne , kuma nan gidan Momy na ne anan zan kwana". Ehhhh ka kwana a ina? Allah shi kyauta ,ka hanani sukuni da Zainab kenan fita!!

Murmushi yayi yana tuno da inama momy ta barshi ya kwana a gidan da tabbas cikin dare sai ya turmushe Zeee don ya gaji da haƙuri ,ƙwartancin dai ya daina yi ,tun da ya samu Zee ya kuma ɗan ɗani zuman ta". Momy na tuba don Allah ki barni na zauna ,zan ƙoƙari na kauda kai na akan Zainab indai wannan ne tunanin ki . Kai baka isa ba ,ai ka girma nemi gidan ka ,nan gida na ne nida Bby na".

Tom Momy ki tambayi Zainab inda bata So na ,ta faɗa maki sai in tafi . Ban gane ba? Mom Salma tayi maganan tana kallon shi ,itako Zainabu sunkuyar da kanta tayi ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannunta. Ehh Momy ki bari ki tambayi Zainab in tace " Bata so na sai ki rabamu in kuma tace tana Sona to sai ki barni na zauna anan tare da Matata".

Humm numfasawa Mom tayi tana cewa Ok shikenan". Zainab kina Son Habab ? . Ƙirjin Zainabu ne ya buga , shiru tayi tana sauke kanta ƙasa ta kasa ce mawa Momy komai". Kar kiji nauyi na Zainab , kar kuma ya baki tsoro faɗa mun kina Son komawa gidan shi??? Ƙasa bata amsa tayi sai hawaye n da ya fara zuba mata. Shikam Habab Murmushi yake don yasan ya riga ya gama tsorata Zainabu da maganganun burgar da yagama yi mata , wanda a yanda yake jin kansa yake zai iya aikata komai akan duk wanda yayi yunƙurin Rabashi da Zainabu. Zainab baki ce komai ba?? Yaji Muryar Momy yana katse ta. Dariya yasa yana cewa " Mom tana jin kunyar ki ne bazata yi maki magana ba ,amma ina mahaukacin Son Zee itama kuma haka take So n Habab.

Shiru Momy tayi sai kawai ta saki murmushi tana rungume Habab shima Rungume ta yayi , fuskar su su duka na fidda Annuri ....hannu takai tana matso da Zainabu da tayi shiru har lokacin kanta na a ƙasa , haɗa su tayi su duka tana Rungume su tana tsakiyar su.... murmushi Zainabu tayi tana ƙara riƙe hannun Momy. Ɗago da fuskar ta tayi ,nan taga idon Habab na akan ta , kashe mata 1 eye yayi wanda yasa ta saurin ƙasa danata idon". Momy ne ta goge ƙwallahn dake zubowa daga idon ta , tana ƙara godiya ma Allah". Ganin haka yasa Habab kai hannun sa yana sa hankie yana goge mata hawayen....kallon sa tayi tana murmushi ,nan suka ƙara Rungume junan su...tana riƙe da hannun Zainabu dake bin su da murmushi sosai suka burgeta , A wannan yanayin Adda Raliya ta shigo ta tadda su... Kissing ɗin Momyn nasa yayi yana Rarrashin ta... Murmushi Momy tayi tana waigawa ga Adda Raliya kana tace " Na amince Zainab zata koma ,amma ba ayau ba ,shi kuma ya koma ba bu wurin kwanan sa anan!

Rintse ido Habab yayi don ya fahimci Momy ta gane shi sosai tasan akwai abun da yake nufi. Dariya Adda Raliya tasa tana cewa " Ai ko a hakan muna godiya'.

A tare suka nufi falo ,ban da Zainabu da tayi bedroom ɗin ta ,ji tayi duk jikin ta yayi mata sanyi , gaba ɗaya Habab ya sauya , tabbas ba yaudara a tare dashi duk abun da ya faɗa xaiyi hakan ne har a zuciyar shi..............zama tayi a gyefen ƙayataccen bed ɗin nata tana sa hannun tana....

*Littafin ƙwrtn mny na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932 "Tncuuu".🤝🏻*

Mmn teddy🧸
[7/3, 15:58] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
Chapter 15 · 0% Book details