← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mutane kuwa daga masu kama kai sai masu ihu ganin irin daga dagan da Umman Sobreen tayi ta haɗe da kwalta , inalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine kaɗai abun da Hjy Luba ke cewa " ruɗu iya ruɗu tashi ga a wannan rana .. Alh Nafi'u ne ya kama hannun Sobreen da take ihu kaman ranta zai fita ,yana jefa ta a moto yana jahh haɗi da barin wurin , don ko a jikin sa ganin wannan haɗari , cewa ma yake hakkin mahaifiyar sa ne , da ta raɓasu tsawon shekaru. Don haka can zai kai Sobreen garin Adamawa ta koya mata tarbiya kaman sauran ƴaƴan da ya saba gani.
Zainabu kuwa sam bata farka ba sai wuraren 9:00am ,wanda da addu'a a bakin ta ta miƙe , tana kirar sunan Habab , sai da idon ta yaƙara buɗe wa ne ta tabbatar da mafarki tayi". Dafe ƙirjin ta tayi da yake harba mata da ƙarfi tana cewa " Meke shirin faruwa da Habab ?? Allah kasa mafarki ne ba gaskiya bane . Kasa nufar toilet tayi sai kawai nufan falon tayi don ganin Momy a wani hali take ciki don tasan jiya a kanta ta kwana". Cike da murmushi Momy take bin Zainabu da kallo da tayi wani dama² tayi kyau ta murje sai ƙiban ta take mai sukuni da natsuwa. Cike da harka Zainabu ta ke yin mata an tashi lfy? Kana ta nufi kitchen don taimaka mata aiki. A'a Zainab koma kije ki huta , na kammala komai ai , yanxu ke nake jira ki shirya kizo kiyi breakfast sai kisha maganin ki". Nisawa Zainabu tayi tana murmushi da mata sannu da aiki ,kana ta juya don ta watsa Ruwa ta sauya kayan jikin ta daga na barcin zuwa na zaman gida". Cike da jin ƙaunar Zainabu n Mom Salma kebin ta da kallo , tabbas abun da take hasashe hakan yake , juna biyun jikin ta na nan bai fita ba ,Allah kenan! Allah ya raba lafiya". Mom Salma tayi maganan tana cigaba da shirya dirnng area n. Motsin Zainabu ne yasata ce mata " Bismillah zauna dai da lura! To Momy". Zainabu tayi maganan tana zama a hankali duk jikin ta nauyin shi take ji a kwana biyu sai tana rinƙa jin ba daɗi a harshen ta ,kome xata ci bata jin daɗin shi....nan tafara break cike da gode mawa Mom Salma don iya girki da karamci ba baya ba". Gaskiya Mom Komai yayi daɗi". Zainabu tayi magana tana dariya. Dariya itama Momy tayi tana cewa " mashaallh to tun da Zee ta yaba saura ɗan ƙaƙƙwafi Habab! Ohhh!! Ɗazu fa Habab yazo gidan nan kina bacci tfy aiki ya kamasa a yau ɗin nan yanxu ma ina tunanin jirgin su ya ɗaga gasky". Wani irin bugawa ƙirjin Zainabu yayi , wanda sakin cup ɗin tea tayi tana cewa " Momy meyasa kika bar sa ya tafi?? Wallh tsoro nakeji nayi mafarki Momy ki kirasa ya dawo!!!. Ganin Zainabu ta ruɗe lokaci ɗaya yasa Mom Salma saurin dafata tana ɗan bubbaga kafaɗan ta da cewa " Shiiii... Ya isa ai zai dawo yace baifi 1 mount zaiyi ba , kuma mafarki Zainab ba gaskiya bane ba kinji ,Allah zai dawo maki da Habab lafiya inshaallh". Nisawa Zainabu tayi ji tayi komai ya fice mata a rai. A hankali ta ce " To Momy Allah yasa". Amin abun da Mom Salma tace kenan tana cigaba da matsar mata da irish gaban ta.
****
Kwana uku da tafiyar Habab Daddy da Kanshi yazo bikon Mom Salma ,wanda iyaye sun shiga cikin maganan sosai da ƴan uwa da suke ta zuruntu garuruwa kuwa ,wannan yasa don dole Mom Salma ta kuma amincewa , a satin a ka maida auren su da Daddy ,duk da ba wani taro akayi ba,manya ne a dangi suka taru...a kuma ranan Mom Salma da Zainabu da baki yaƙi rufuwa saboda farin ciki suka koma gidan Daddy. Da komai na gidan sai da aka sake , niko nace sabon gwamnati kenan shi aka kafa". A ɓangaren Zainabu ke zaune ,kula da gata iri iri take gani a wurin Momy da Daddy kowann su na ƙoƙarin ganin sun faran ta mata ,sun kawar mata da dukkan wani damuwa . Wanda a yanxu kusan wata ɗaya kenan da tafiyar Habab . A yau ne Zainabu ta shirya don zuwa gidan Umman ta ,wanda a yanxu idan kaga Zainabu komai na alamun masu ɗauke da juna biyu ya bayyana mata , gashi bai fara girma ba ,amma ya sata tayi kyau matuƙa ,duk da da hutu da kula irin na Mom Salma da take bata".

Farin ciki da taje gidan ba'a magana wurin mutan gidan da su Abba ,bana har da Sama'ila anan nan da ita ,wanda sosai taji daɗin hakan , Zainabu fah anyi hankali don har da tsaraba takai mawa su Umma da sauran yaran gida. Anan take jin ashe Habab sai da yazo sukayi sallama sannan ya wuce. Wurare n yammaci ta tattara tana komawa gidan Daddy. A falo ne take jin kukan mutane da magiya na ban haƙuri ,wanda yasata kutsa kanta cikin sauri , idon ta ne ya sauka akan Hjy Luba da Shema safiya dukan su a falon gaban daddyy ,gyefe guda kuma Mom Salma ce itama fuskar ta ɗauke da damuwa.........

*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
[7/4, 16:55] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*

Jiki a sanyaye Zainabu ta isa tsakiyar falon tana zama gyefen Adda Raliya da itama ke share ƙwallah ganin yanda Uwar tasu duk ta mozan ta ,duk da da halin ta amma kuma uwa uwace ! Zama Zainabu tayi a ƙasa a hankali tana jin yanda Safiya da Shema'u keba ma Alh Ahmadu Haƙuri harda Hjy Luba , wanda cike da Muryar girma Alh Ahmadu ke cewa " Ya yafe masu Allah shi yafe mana baki ɗaya". Jin hakan yasa Su Hjy Luba juyowa ga Momy da Zainabu da kanta ke a ƙasa suna bata haƙuri akan abubuwan da suka ai ƙata da yanda ta kori Momy da hannun ta duk don kishi da masifa". Cike da nuna komai ya wuce suka ce Allah ya yafema na baki ɗaya". Wani irin Zainabu taji ganin wai Hjy Luba ce take yi masu sallama zata bar gidan ita da su Safiya. , Wanda ganin hakan yasa Momy kallon Daddy tana cewa " Ya kuma zaka barsu su tafi? Don Allah dai kayi haƙuri akan komai mu ɗauke shi muƙaddari dama rubuta ce ne Allah ya tsara xaya faru. Maganganun Momy ne yayi tasiri a zuciyar Daddy , wanda sai da suka fita ne yake ce mawa Adda Raliya ta kai su ɗaya daga cikin gidajen sa na High low cost , ya bama Hjy Luba har muddan rai , su Safiya su zauna can , har Allah ya basu bazajen aure ,idan kuma auren nasu ya dai daita Alhmdullh". Ba Adda Raliya ce kaɗai tayi godiya ba , har da Zainabu da farin ciki yaki ɓoyiwu a fuskar ta , don ganin Hjy Luba a wannan hali ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba". Godiya sukayi ta mawa Daddy har ya shige side ɗin shi ,kana Adda Raliya ta fice da sauri don sanar mawa su Hjy Luba da kyautar da karamcin da Daddy yayi mata... Momy ne ta kalli Zainabu tana murmushi kana tace " Har kin dawo yasu umma?? Suna lafiya Momy sunce a gaishe ki". Cike da jin daɗi Mom Salma tace " to mashaallh ina gdy. Tun daga nan shiru ne ya biyo bayan su tsawon lokaci ,kamin Zainabu ta katse shirun da cewa " Momy wai don Allah nayi maki wata tambaya ,Allah yasa bazai ɓata maki ba , don a kan rayuwar ki ne Momy da na Habab!
Chapter 17 · 0% Book details