← Book details Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 24

Sashe 12

Kwarton Manya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932🤝🏻*

_*Wannan shafin naki ne Adda kuma Aminiya ta Rukyn Jalal (UMSAD INCENSE) Allah yaƙara kare ki Aduk inda kike ya shirya zuri'a ya rayasu mana su bisa tafarki madaidaiciya.....Ina maki Son So fisabillh😄🥰*_

*****

Ganin yanda Hajiya Raliya ke maganan cike da mamaki fuskar ta na fitar da annashuwa yasa Zainabu takowa inda take tana cewa " Ƙwarai kuwa Adda Raliya , wallahi mun gan ta , amma Habab bai da kirki". Dafe kai Raliya tayi tana cewa " Subhanah shiknnn Allah yasa bai yi mata tijarar nasa ba". Uhmm To Adda Raliya me zai fasa wannan, zuciyar shi ta dalma ce ,sam babu alamun tanƙwara ,abun da yace yayi masa kawai shine ,babu wanda ya isa ya hana shi , sai idan yaso". Shiru Adda Raliya tayi idon ta na kaɗawa , wannan wacce irin rayuwa ce Ammie ta jefa Habab? Taasa masa tsanar mahaifiyar sa ,baya marmari n ta irin na uwa da ɗa, anya Ammie abun da take tana kyautawa kuwa??". Duk Adda Raliya ke maganan a zuciyar ta ,kamin taji Muryar Zainabu ya katseta tana cewa " Adda Raliya na shirya mu tafi ko??? . Miƙewa Adda Raliya tayi jiki a sanyaye ba ƙwari suka nufi side ɗin Hajiya Luba". A falon suka tadda su kaman yanda suka bar su , sai dai a wannan karon ba Habab ba Sobreen. Zama Zainabu tayi tana gaishe dasu Hajiya Luba da Shema ,wanda dukan su a fuska sake suka amsa mata tamkar ba wani abu a tare dasu....Mmkin wannan sauyin Zainabu keyi kana ta tsinkayi muryar Hajiya Luba tana cewa " Zainab hau sama ki kira Habab da Sobreen ,su sauko haka nan".

Miƙewa Zainabu tayi a hankali su duka suna bin ta da kallo, a zuciyar su suna cewa " Shegiya ƴar matsiyata ta samu wuri ai dole ta buɗe ba abun da ya dameta, wato mu ta barmu ga ƴan iska , zaki san waye Hajiya Luba". Ita dai Zainabu dake juya jiki tamkar ɗawisu don ita kanta tana ɗan jin yanda jikin nata yayi mata nauyi. A hankali ta haye stairs ɗin falon tana nufan up don ta shaida masu kirar Hajiya Luba".

Wani irin dammm yaji ƙirjin ta ya buga mata , gani tayi Habab ƙawance a 3strr na falon da ya ƙawatu matuka , gyefe Sobreen ce zaune tana kissing ɗin bakin shi..... Shima yana nata , ji tayi tamkar ta juya ,amma kuma babu yanda ta iya , Cikin zazzaƙar Muryar ta tayi masu sallama, wanda babu wanda ya amsa mata , sai dai dakatawa da sukayi da yin komai ". Hajiya ce tace nayi kirar ku ƙasa". Kauda kai Sobreen tayi sai Habab ne yace " Okay! Ficewa tayi daga falon tana sauka don faɗa mawa Hajiya Luba , nan taga babu kowa a falon sai Adda Raliya.... Zama tayi gyefen Hjy Raliya tana cewa " Adda Raliya ina Ammie??. Tana ɓangaren Daddy jeki dubata can . Ita dai ji tayi kaman an cire mata laka , a haka ta nufi ɓangaren Alh Ahmadu , a falo ta tadda Shi da Hjy Luba ,wanda ganin haka yasa ta zubewa saman carpet ,kamin tayi magana yana murmushi don ita har mmkin fara'ar shi take , duka ƴaƴan shi babu wanda yayo sa. Mutanen Japan Zainab ɗiyata kinga dai gari ko? Bai rufe ki a gida ba don Nasan halin Habab sarai". Dariya Zainabu tasa har da ƙyaƙyatawa , kaman ba sirikin ta ba ta matsa kusa dashi tana cewa " Eiyee Daddy munje wallahi ƙasar tana da kyau gaskiya". Nan Zainabu ta hau Bama Daddy labrn japaan da yanda Suka yawuta da Habab. Fira sosai suke da Daddy har sun manta da Hajiya Luba dake zaune tamkar wacce aka dasata ji take tamkar ta kashe ɗayan cikin su ta huta.
Miƙewa tayi ne zata fita don baƙin ciki ya nata sukuni har ɗigar zufa take yi . Muryar Zainabu taji tana cewa " Daddy aiko na faɗa maka munga Mahaifiyar Habab a Japan!

Wani irin jiri ne ya ɗibeta , wanda yasata saurin dage bango tana shirin faɗi taimakon ta bangon da ta riƙe. Saurin aje jaridar hannun shi yayi yana kallon Zainabu jikin sa har rawa yake yana cewa " Zainab a ina kike ga Salma?? Ina take tare kuka zo?? A'a Daddy , Habab yaki.... inalillahi wa'inna ilaihir raji'un wannan wani irin yaro ne??? Bai taho mun da Salma ba ?? Daga can yasan inda zata tafi ! Ƙoƙarin miƙewa yakeyi yana dafe ƙirjin shi da yakejin tayi masa nauyi yana fara tari.....Saurin matsawa gareshi sukayi cikin sauri , wanda kamin ta isa Hjy Luba ta dafe shi tana zaunar dashi ,cikin wani irin murya mai kama da kuɗu tace " Zainab maza jeki falo ki ɗauko mun ruwa na basa.....Ruɗu da firgicin yasa Zainabu sam ta manta da wani fridge ,wannan yasata nufar falo da sauri don ta ɗauko ruwar".

Minti biyu ta dawo da ruwa a hannun ta , wanda hango Daddy tayi a kujerar babu alamun rai a tare dashi , kumfa mai kaman jini na fita ta bakin shi, sam ba Hajiya Luba a wurin....sakin ruwan tayi tsana nufan sa da sauri tana riƙo hannun da kirar sunan shi " Daddy ga Ruwan , daddyyyy!!

A bayan ta ne taji ihun Shema'u tana faɗin " Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un mun shiga uku ta kashe mana uba , Kuzo Safiya Adda Raliya shiknnn Zainabu ta kashe Daddy!!! ,Wani irin bugawa ƙirjin Zainabu yayi , wanda kamin kice kobo duka sukayo falon har da Habab da Sobreen da suka nufo inda Zainabu da Har a lokacin take riƙe da hannun Daddy". Girgiza Alh Ahmadu Habab keyi yana kirar sunan sa ,Sobreen ko ta ɗaura hannu aka tana tsala ihu....dai dai Hajiya Luba na sakkowa da gudu hannayen ta asaman kanta....kallon Zainabu tayi kamin tace " Zainabu me mukayi maki?? Me mukayi maki kike Son rusa duk wani farin cikin mu..mijina zaki kashe waye ke??? Habab ka ɗauko mana guba , kinyi yunƙurin kashe Habab bai yiwu maki ba shine zaki kashe mahaifin sa , kika sa da yaudara ??? Hawaye ne ya hau bin kuncin Zainabu sharrrr ³ ba ƙaƙƙautawa , buɗe baki tayi da ƙyar kanta yayi mata nauyi ,Hajiya wallahi bani ba....ji tayi tassss² Safiya tana wanke fuskar ta da wani irin gigitaccen mari, wanda yasa maganan nata ta ɗauke.....Baƙa mai baƙar aniya shiknnn lahaula walahhh Zainab me mukayi maki a rayuwa? Wayyo Daddy !!!! Safiya tayi maganan tana baya rigijajaaaa wai adole ta sume ..... Shema ne da Hajiya Luba suka hau ihu suna riƙe ta shiknnn za'ayi biyu......

Zee me Daddy yayi maki zaki kashe shi? Ta tsinkayi muryar Habab da yake takowa inda take kamar kumurci , a wannan lokaci n duk tsoran sa ta fice mata,tsayawa tayi ji take kawai ya kasheta itama ta huta da wannan rayuwar! Ka yarda kai ma Ni Zainabu xan iya kisa?? Kisan na wai na kashe Daddy??. Wani mari ya É—auketa dashi da sai da cikin ta ya murÉ—a mata tana ganin tartsatsin wuta..... Tun da kika ce kina Son na , Nasan da wata abun da kke kulawa , sai ki nemi kashe mun Mahaifi?? Wani marin ya É—auke ta dashi da sai da ta kira ,bakin ta na fashewa da jini ,fuskar ta shatin hannayen sun fito raÉ—a raÉ—a". Gaban sa Adda Raliya tayo tana cewa " Habab ka natsu tayaya Zainabu zata kashe Daddy??? .

Adda Raliya Daddy ne fa, sai kace ba mahaifin ki ba , to waye zai kashe shi anan gidan...kuma sawa aka same shi??? Shema'u tayi maganan cikin Muryar matsanancin kukan karya.....wanda jin haka n yasa Adda Raliya fashewa da kuka ,ita dai tana jin kokonto a zuciyar ta ,amma kuma waye zai kashe masu mahaifi?? ....yanda kika kashe mun Mahaifi wallahi kema yau sai na sa bindiga na harbeki ,ko na kasheki da duka. Habab yayi maganan fuskar da duk ta sauya ya koma Habab É—in É—an da a lokacin suma kansu tsoran sa sukeji ,don sun san zai iya komai.

A wannan karon sam Zainabu takasa kukan sai hawaye....Ina ai mu kira jami'ai su fita da ita...daga baya ayi bayani n komai ,Cewan Hajiya Luba tana goge hawayen fuskar ta".

Ina ne xa'a tafi da Zainab É—in ?? Sukaji wata Muryar da basu san ta wacece ba ya katse su daga bayan su". Cikin sauri su duka suka waigawa don ganin wacece ke faÉ—in wannan magana". Wani irin razana Hajiya Luba tayi kana cikin wata irin murya ta ce " Salma??".

Bata amsa ta ba sai cewa tayi " Ina a raye Sirikata matar Habab wai a yari? Abun da kikeso kenan ,to koda komai nawa da na mallaka xai ƙare sai dai ya ƙare ,baxan taɓa barin hakan ta faru ba. Aiko wallh ba'a isa ba ,ta kashe mana Daddy kice ba za'a ɗau mataki ba, dama ƙila ke kika saka ta! Shema ke maganan cike da ƙunar rai...ji take kaman ta haɗa su su duka ta kashe . Tsayawa Habab yayi cakkk yana kallon Zainabu da lokaci ɗaya kamanin ta sun sauya saboda marin da suka dingi zagba mata , jin tsanar ta yake a kowani sekan , Jinin yaga yana bin ƙafarta , wanda kamin yayi magana ne yaji Muryar Momy tana cewa" Ai mahaifin naku bai mutu ba , da kanshi xaiyi bayani in Zainabu ce take yunƙurin kashe shin zai faɗa.

DPO taji tayi kirar DPO wanda cikin gaggawa suka shigo da mutanen sa , kuɗauki Alh Ahmad akai shi asibiti mafi sauri kuma mai tsaro sosai....Ni xan tafi da Zainab ...Habab wallahi sai kayi nadama ,ko nace tun daga yau zaka fara nadama , Zee ce xata iya aikata wannan abun ,har kake marin ta , saboda tana ƙaunar ka a rayuwa , to Ni daga yau na rabaku da Zainab har abada babu kai babu ita....kaje kayi rayuwar ka da matar da kake so mai son ka da gaskiya.
Chapter 12 · 0% Book details