Sashe 9
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ni kaina, tunda Kabeer ya nuna min babu tausayi, yarda da aminci a tsakanin ma’aurata na taho daga rakiyarsa, da ma kowanne Da namiji. Ina so in rayu ni kadai, a inda babu kowa”. “An gama Safeenah” Ya fada cike da karramawa da bin umarni. “Nan dakin ya yi miki? Za ki iya rayuwa ke daya a cikinsa?” Ta yi walai da manyan magananta, sai da zuciyar Abdussamad ta buga ta ba da wani dan sauti yadda ta harba idanun cikin dakin kamar a zuciyarsa ta harba. Ta gyada kai alamar ‘eh’ ba tare da tana dubansa ba. “Amma sai in kun yi min alkawarin ba za ku dinga ba ni magani ba irin na Aminu Kano, shan maganin yana takura min, ba na son hadiyar kwayar magani tunda ni dai na gaya muku lafiyata kalau, kadaicewa nake bukata”. Ya mike yana gyara ‘tie’ dinsa, yadda zai ji dadin tafiya. “Rabu da likitocin Aminu Kano, haka kawai su dubi zukekiyar yarinya haka irin Safeenah su dinga ba ta magani suna cewa ba ta da lafiya? Duk ba su san aikinsu ba. Nan ba mai ba ki wani magani, ba mai takura miki. Ko su Yaya Khalil ba zan bari su shigo ba balle su takura miki, don na lura Yaya Khalil din nan ba shi da tausayi”. Ya russuna a gabanta cikin sigar roko. “Zan ke iya zuwa ina taya ki hira? Ranki ya dade GimbiyaSafeenah?” Ta girgiza kai. “me ye hadina da kai da za ka dinga zuwa taya ni hirar? Ina maganar ‘isolation’ kana maganar hira, ina ruwana da wata hira?” Ya mike ya daga hannayensa sama alamar ya yi saranda. “Shi ke nan Aunty Safeenah. Amma ai dole za ki ci abinci ko? Ko shi ma namiji ne an yi fushi da shi?” Ta dago da sauri ta dube shi suka hada ido. Sosai yake kallonta cikin idonta yana murmushi. Wasu kibiyoyi na sukar zuciyarsa wadanda ke fitowa daga idon Safeenah, ita kuma cewa ta ke cikin ranta, ‘he is talking nicely, ba irin Yaya Khalil ba’. Ta dauke kanta daga kallon kurillar da suke wa juna. “A dinga miko min ta taga, in ba haka ba na hakura, yadda na hakura da Kabeer ko shi ne autan maza zan iya hakura da komai. Ba abin da ya zame min dole a rayuwa…!” Ta fada cikin karkarwar murya mara amo, wadda ta taba zuciyar likita Dangi, ya kasa dauke ido a kanta. A hankali ya saki gefen gadon da ya dafa ya fita. Yana zaune a kujerar ofishinsa yana rubutu cikin ‘file’ din Safeenah. Yana fadi cikin ransa, ‘insha Allah kafin kwana sittin zai shawo kan matsalar Safeenah. Aka kwankwasakofa ya ba da umarnin shigowa. Katheryn ce, (nurse on duty) kuma mai kula da abincin da Safeenah za ta dinga ci. Ya rubuta mata magungunan da za ta dinga narkawa Safeenah cikin lemo guda uku sau biyu a rana, ko a ruwan shanta. Ta kuma maida robar ta like babu alamar an bude daidai yadda ta zo daga company. Ta karbi umarnin da kyau ta fita, shi ma ya tattaro komatsansa ya watsa a bayan mota ya nufo gida. Kamar kullum, ba ya taba shiga gida hannu Rabbana ba tare da ya rike wa Suhail ko Nanna wani abu ba. Yau ma hakan ya saya wa Suhail dirkekiyar (pampers) a kantin alkawari kamar yadda yake kiran kantin, wato (ASDA). Yana son kantin cikinshi kadai yake iya siyayyar kayan masarufi, yana son shagon kamar ko ma fiye da yadda marigayiya Suhaila ke sonsa. Ya kusa kaiwa gida wayar Nanna ta shigo wayarsa, ya amsa cikin russunawa, duk da ba ta ganinsa. “Ina bisa hanya Nanna dear, (10 minutes drive) ya rage min na iso gare ku”. Nanna na bude kofa Suhail ya rugo da gudu har yana faduwa don kafarshi ba ta yi kwari ba. Shekarunsa biyu. Ya kwashe tsahonsa gabadaya ya zubar a kasa ya ware hannuwansa ya yi wa yaron kyakkyawan matsuguni a kirjinsa. Kira yake. “Daddy… Daddy…” Ya ce, “Suhail dan Daddy, kun wuni lafiya?” Nan ya yi ta masa gwalantu yana biye wa shirmensa, tuni Nanna ta wuce kicin. Kicin din suka bi ta shi da Suhail dauke a kafadunsa, Suhail din na kwance masa madaurin wuyansa. Ya tsaya a bayan Nanna tana tuyar masa irin tasu ta ‘yan Bauchi. Ya ce, “Nanna, ko in sanya Suhail a crechene (wajen rainon yara) mu dinga fita tare don ki samu ki dinga yin baccin safe da kyau? Na lura in kin tashi tun asuba shi ke nan sai wata goben duk a hidimarsa da ta abinci ki ke karewa, ni kuma ina tausaya miki”. Ba tare da ta juyo ba ta ce. “Mene ne creche?” “Makarantar rainon kananan yara Nanna”. Tsaki ta saki, sannan ta juyo ta harare shi. “Ina ruwanka da rashin baccina? Ni na ce da kai Suhail ke hana ni bacci? Wai kana jin tausayina ai kai ne abin tausayi, kuma bari in gaya maka ba Suhail ne yake hana ni bacci ba, kai ne da kanka”. “Ni Nanna?” Ya fada cikin rarraunar murya. “Eh, kai. Domin farin cikina da kwanciyar hankalina shi ne cikar naka farin cikin. To ka hana wa kanka farin cikin a kan wadda har abada ba za ta dawo ba, tata ta riga ta kare. Addu’a kawai ta ke bukata kuma na san kana mata”. Ya yi shiru yana sauraron mahaifiyarsa, wadda ke magana cikin fushi, amma amon muryarta tafe yake da lallashi da nasiha. Bai san me zai ce mata ta fahimce shi ba, illa; “Idanuna sun mutu Nanna da kyawun Suhaila, zuciyata ta rufe kofarta da cikar nagartarta, ta yadda ba na iya kallon kowacce diya mace. Zuciyar ba ta iya soka kauna da soyayyar kowa bayan naki da na dan Suhaila. Amma a yanzu a hankali zuciyar tana karbar wani CANJI da ban gama yarda da shi ba balle na gaya miki”. A hankali ya ce, “Ki bar ni Nanna… ki bar ni Nanna da wannan maganar… don Allah ki bar ni”. Abin da ya ce da ita ke nan. Da sauri ya aje Suhail. Da sassarfa ya fita daga madafin ya bi matattakala ya yi sama.