Sashe 18
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
HABIBU SODANGI RUMAH!
Yana sauka daga matattakalar jirgin ya hango wannan sardidin fasihin matashi. Yana sanye cikin kaftan na shadda ‘hilton’ idanunsa saye cikin bakin gilashi, yana ganinsa ya gane shi. Ya idasa saukowa daga matattakalar jirgin. Habibun ya nufe shi yana duba agogon hannunsa yana dube-dube alamar bai san wanda ya zo tara ba. Ya karasa a hankali ya dafa kafadarsa. Da yake ya bashi baya.
Matashin ya juyo da fara’a mai yawa akan fuskarsa. Ya bashi hannu suka yi musabiha.Akwai tabon sujjadah a goshinsa radau! Ya turu ya yi baki alamun cewa Sajidi ne. Ga kuma wayewar zamani mai yawan gaske da alamun hutu a tattare da shi.
Ya kama hannun Abdussamad ya rike sosai cikin nasa ya ja shi zuwa inda ya adana motarsa, wata irin bakar ‘ferrari one door’ da Abdussamad ya tabbata ta fito ne daga ‘general motors’ din Amurka. Cikin sukuni yake tuki yana jan Doctor da bakatsiniyar hirarsa.
Ya ce, “Doctor Abdussamad ni ma ba ni da lafiya, kwanan nan na fito daga asibiti. Na kan yi fama da ciwon kai na barin kai guda mai tsananin zafi, yanzu haka na yi hoton kwakwalwa, gobe zan karbo. Ka taya ni addu’a kada ya kasance babban lamari ne”.
Abdussamad ya dube shi cikin tausayi, ya ja sunan Allah a zuciyarsa kada abin da ya hasaso ya zam tabbatacce.
Ya ce, “Insha-Allah you will be alright my friend. Kaffara insha-Allahu. Ya ya iyali fa? Akwai ko babu?”
Ya yi murmushi yana murza sitiyari.
“At my age idan na ce maka babu iyali ai sai ka yi min fada. Domin a kalla za mu yi ‘age-mates’ ni da kai. Akwai mace daya da yara biyu sun je hutu gida Katsina”
Ya kai hannu jikin wani dan kyakkyawan ‘frame’ da ke jikin motar ya juyo masa da shi. Mace mai kyau da gogewa ‘yar kimanin shekaru ashirin da biyar ita ma da tsagin rumawa irin nasa a gefen fuskarta da yara mace da namiji, kyawawa har ma fiye da iyayen.
“Masha Allah, tabarakarrahman, you have a wonderful family”.
Daidai lokacin da ya kashe motar a ‘parking space’ na ‘flat’ dinsa, a wata kebantacciyar unguwa ma’abociyar korayen ganyayyaki masu kyawun gani da kamshi mai sanyaya zuciya.
Ya sa mukulli ya bude ‘flat’ din. Wani kayataccen falo ya zahhara a idanun Abdussamad. Ba wai zai ce falon ya burge shi kadai ba, har ma da jinjinawa tsarin rayuwar mamallakansa. Maza irinsa ‘are rare’ a duniyar nan wadanda Allah ya yi wa baiwar komai na rayuwa.
Habibu ya katse masa tunani ta hanyar ba shi izinin zama cikin kayatattun kujerun. Kawo wannan, kawo wancan daga kicin da firinji. Habibu ke nan da ke kokarin ‘entertaining’ bakon nasa ko ta ya ya. Idan ya dauko sai ya aza a ‘dinning’, fadi yake.
“Gidan gwauro sai dai ‘yan dabarun kama ciki abokina likita, amma babu kwakkwaran abinci, ‘this lady’ ta gama sangarta ni da girkinta, ba na iya cin na ‘restaurant’ haka nake fama da ‘yan dabaru har sai ta dawo”.
Abdussamad ya lumshe ido a hankali. Tashi ‘lady’ din ta dawo ‘fresh in his memory’. Wadda shigowar Safeenah cikin rayuwarsa ya sa shi fara mantawa da ita, sai ya kwana ya wuni bai tuna ta ba. A yau shi ma ya tuna ta, ya tuna kala-kalar girkinta masu dadi ya tabbata shi da irinsu sai a aljanna idan Allah ya hada su, domin ya san ko ya yi nasarar auren Safeenah ‘yar Sarki ce ba ta san wannan wahalar ba.
Shi kadai ya yi murmushi, ya ce da Habibu.
“Kada ka damu, ni ma ba ma’abocin cin mai nauyin ba ne a tun bayan da na rasa ta. Gara kai za ta dawo ta ci gaba da yi maka, ni kuwa sai a Darussalam”.
“Oh dear!” In ji Habibu.
“Ban so na kawo wannan batu ba. Allah ya yi mata rahma da madaukakiyar gafara, Ya bakamafiyinta. Yara fa? Akwai ko babu?”
“Suhail yana nan, ‘a very healthy toddler”.
“To masha-Allah, ‘since we’ve him’. Allah ya raya shi, Ya albarkace shi. Ina da Aminu da Amani. Maman su ‘first cousins’ muke, sunanta Ruqayya”.
Ya fada yana zuba mishi ‘fresh milk’ a kofi.
Abdussamad ya dubi hoton ‘window size’ da ke kafe a falon, ya ce.
“Daga duba na farko za a san kun hada jini da ita. Dukkanku rumawa ne”. Habibu yayi dariya.
Daga haka ba su kara magana ba sai da suka kintsa cikinsu. Suka yi sallar la’asar da lokacinta ya yi a lokacin. Abdussamad ya nemi da ya kai shi ‘hotel’ mafi kusa ya sauka ya huta zuwa anjima kafin su yi maganar da ta kawo shi. Atabau ya ce shi ‘already’ ya yi masa masauki a ‘guest room’ dinsa.
Karamcin Habibun ya sha kansa, ta yadda ya kasa musawa ya karbi tayinsa.
Ya yi wanka ya kwanta ya huta wahalar zaman jirgi, zuwa karfe shida na yamma ‘alarm’ din da ya saita shi ya tashe shi. Ya fada ‘toilet’ ya dauro alwalar sallar magriba duk da lokacinta bai karasa ba a kasar Japan, mukhtarin ya bambanta da wanda ya baro. Ya canza kaya ya zauna bakin gado ya kira Nanna, ya gaya mata ya sauka lafiya, ya kuma kusa gama abin da ya kawo shi, ta yi mishi addu’a.
Daga nan (Spire-Little-Aston) ya kira ya ji halin da Safeenah ke ciki. Duk ‘report’ din da suka dauka suka gaya masa, tana karbar kowanne abinci aka ba ta tana ci yanzu, ba sai na kasarta ba. Sannan babu wata waya a tare da ita, amma hakan bai hana ta hira ita kadai ba, tana ‘assuming’ tana yi da wani.
Suka gaya mishi cikin hirar tana yawan ambaton wani suna ‘Habibu’, wani lokacin kuma ‘Kabeer Dambatta’. Ya kara ‘adjusting’ magungununta ya gaya musu. Aka kara ‘dose’ din.
Ya ce da su su daina bari tana gane akwai ido a kanta, a yi komai ta CCTV.
Habibu ya dan buga masa kofa.
“Friend, magrib time”.
Ya mike, da ma a kintse yake, ya bude suka jera, ya ce.
“Akwai masallaci babu nisa daga unguwar nan, can za mu je”.
Suna tafe cikin motar Habibun suna hirar kasarmu Najeriya. Da yadda aka barta a baya cikin abubuwa na ci gaba, musamman (infrastructure and good governance) yaushe ne kasarmu Nigeria za ta samu wadannan abubuwa?
Habibu ya ce, “Sai ranar da muka cire son kai, hadama da zalama, muka taimakawa shuwagabanninmu masu kudiri na alkhairi”.
Abdussamad ya ce, “Kuma ‘ya’yanta irinku da Allah ya yi wa baiwar ilmin da fasaha ku ka bar kasashen Turai ku ka dawo ku ka rungume ta ba?”
Ya kyalkyale da dariya, ya ce, “And you?” Ya na nuna shi da dan alinsa cikin dariya.
Abdussamad ya ce, “Ni abin da ya raba ni da gida har nake wa ‘western’ aiki ba rashin kishin kasata ba ne. Matsala ce daga mahaifiyata, ba ta so in san dangin mahaifina. Amma in don ta ni ne, ba abin da zai sa in dinga ciyar da wanda dama gaba yake damu gaba, ba ya bukatar sai da ni zai ci gaba. Kuma ina fatan watarana in koma kasata in tallafa wa al’ummata”.
Habibu ya ce, “Na yarda da hujjarka, don mahaifiya gaba ta ke da komai. Amma ni din ka san tawa?”
Ya ce, “Ban sani ba”.
“Yauwa, to akwai masu dumbin ilmi ‘yan kasarmu a kasashe daban-daban wadanda zurfin ilimin da fadinsa da suka samu ya zarta mahaifarmu ta amfana da shi ita kadai. Ko kuma ince, bata bukatar bangaren sa saboda cigaban nata bai zo nan ba. Zan baka misali da Almustapha Zubair Dankasa (Babban Goro), automobile engineer ne, har yanzu banji ta inda ilminsa zai amfani kasarmu mai albarka ba. Ga kuma ni Habibu Rumah. (I design a Solar Power from Japan). Amma gara ni,sabida su wa ke amfana da ‘solar at 80% rate’ a wannan zamanin da muke ciki in ba ‘yan kasata Nigeria ba?”
Cike da gamsuwa da bayanansa Abdussamad ke gyada kai.
“Allah ya kawo wa kasarmu Nigeria mafita daga halin da take ciki, domin matsalolin sun wuce tunanin mai tunani, ya wuce dabarar mai dabara, ya wuce azancin mai azanci, ya wuce hikimar mai hikima. Amma muna da tabbacin matsalar bata gagari Allah ba, muna rokonsa kuma muna da tabbacin zai mana maganin matsalolin. Muna da tabbacin ya san daga inda matsalar ta ke zai mana maganinta bakidayanta alfarmar Sayyidis-Sadati Nabiyullahi…”
Daidai sanda suka iso masallacin har an fara kiran sallah. Da sassarfa suka karasa, ba laifi akwai wadatar musulmi daga ‘ethnicity’ daban-daban a kasar. Suka bi jam’i, suka zauna har aka yi isha’i da su sannan suka dawo gida.
A kan hanyarsu ta komawa gida ya tsaya a wani ‘restaurant’ ya yi musu ‘takeaway’ na ‘dinner’ mai zafi suka karasa gida.
Bayan sun ci abincin sun goge baki da hannu. Abdussamad ya dauko gundarin muhimmin abin da ya kawo shi.
“Habibu ka san Safeenah?”
“Safeenah? Wace ce haka?”
“Diyar Sarkin Alkaleri”.
“Ko sunanta ban taba ji ba”.
“Ko cikin abokan karatu? Kawaye na makaranta? Tsofaffin ‘yammata? Ba ka taba alaka da wata mai suna Safeenah Mahmoud Alkaleri ba?”
“Gaskiya ban taba yi ba”.
“Ko cikin ‘fans’ na yanar gizo?”
Ya yi shiru yana tunani tsawon lokaci, kamin ya ce.
“Ban taba yin ‘fans’ mata ba, duk masu yaba ayyukana maza ne ‘yan uwana, sannan ko cikin kawayen matata ban taba jin mai irin wannan sunan ba”.
Abdussamad ya nisa, yanzu komai ya bayyana gare shi babu kokwanto, Safeenah na fama da ‘delusion’ cikin ‘schizophrenia’ dinta, a kan mutumin da bai santa ba, ba ta sanshi ba, ‘yet he’s in existence (wato akwai shi raye a duniya). Wani matsanancin kishi ya kama shi, amma bai bari ya fito a idanunsa ba.
Ya gyara zamansa tare da gyara kwalar rigarsa ya fuskanci Habibun, sannan ya dauko (I.D Card) din sa ya nuna masa, ya kara da wannan bayanin.
“Sunan ta Safeenah, diyar sarki Mahmoud Hamza Wakili Alkaleri. Na yi mamaki da ba ka san masarautar Alkaleri ta Bauchi ba. Domin babbar masarauta ce mai tsohon tarihi da karfin arziki a Najeriya. Ko ni da ke wajen Najeriya na santa a kafafen yada labarai. Iyayenta sun yi mata aure da wani matashi da na lura ita ke sonsa tun kafin auren su ba su so, sakamakon cewa shi din ba dan sarauta ba ne. Na fahimci wannan ne daga labarin da Yayanta ya bani. Bayan auren a cewarsu ta hadu da ‘psychological problem’ sai mijin ya sake ta. A cewar iyayen ke nan fa. Amma daga ita Safeenahr da shi Kabeer din kowanne na tuntuba mafarin ciwonta sai na fahimci matsalar tasu ta fi gaban nan. Wato wani sirrin sai aure. Iyayen su su suke ta hargagin su da alakanta ciwon da butulcin mijinta kadai, amma Safeenah da Kabeer ba ‘psychological problem’ din ta ne kadai ya yi wa auren su kisan gilla ba, kai ne Habibu Sodangi Rumah…”.
Zaro idanu Habibun ya yi na alamun tsoro, kamar za su fado cikin mai a soya su.
“Ta ina na shiga cikin matsalar ma’auratan da ban sani ba? Ba su san ni ba?? Har na kashe musu aure???”
Mu karasa a littafi na 2. Tare suke. Taku; Sumayyah Abdulkadir.