← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

“Tablets din da ta ke karba are special) wato na musamman ne, kuma likitocin da ke duba ta sun san aikinsu. Abu kadan za mu kara a kan wanda suke yi. I wonder (na yi mamakin) dalilin da ya sa ba sa aiki a jikinta har ta ke ‘attempting suicide”.
Ya ce, “Likita ba ta yarda ta sha maganin ai, zubawa ta ke a masai, don ita ba ta yarda fa ba ta da lafiya ba, mu ne ma ta ke kalla a marasa lafiyan”.
Bai san sanda ya yi murmushi ba, har hakoransa suka fito, kalaman Khalil sun ba shi dariya. Khalil ya kirne fuska ya ci gaba da cewa.
“Shi ya sa likitocinta suka ce, in har ba za ta zauna tare da su ba (kwanciya a psychiatric) ba kuma ta shan magani a gida, to fa ba abin da za su iya yi a kanta, tunda (condition) dinta (is critical).
Na yi kokarin mahaifinmu ya amince ta kwanta ya ki, tunda asibiti ne mai kyau ba ‘asylum’ ba ne, amma wallahi Maimartaba sai ya fadi, faduwar da ta janyo masa hawan jini da yake fama da shi a halin yanzu. Ya ce, ‘da ya ga Safeenah a asibitin mahaukata wai ana mata ‘treating’ mata hauka gara ya ga ajalinsa’.
Wani irin so Daddy ke yi wa Safeenah da ban san irinsa ba, da ya rufe masa ido ya hana shi karbar kaddarar da ta same ta. Cewa ya yi a kyale masa ita tunda malamai da likitoci sun kasa. Ka ga da a ce a asibiti ta ke, su sun san yadda za su takura mata ta sha magani su yi mata duk abin da ya dace, amma mu kallonmu ta ke tababbu, ba mu isa mu sa ta ta yi abu ta yi shi cikin dadin rai ba, ga shegen karfi ko katti biyar za ta iya watsar da su sai mun sa mata sarka a kafa muke samun saukinta, ko mu kulle ta a daki.
Na rasa yadda zan yi da tsohonmu likita ya yarda Safeenah ba ta da lafiyar kwakwalwa, ga shi dai ya yi karatun boko amma bai yarda da duk abin da likitoci suka fada a kan Safeenah ba, wai jifa ne da turen aljanu aka yi mata. Ka ganmu mu ne har Maradi ta Nijar neman magani, amma babu malamin da ya ce akwai aljani a jikin Safeenah, ni na yarda da likitoci tana da wata cutar kwakwalwa ta daban da Allah ya halitta kashi – kashi iri daban-daban kamar yadda likitocin mu na gida suka ce.
Ko zuwanmu kasar nan Daddy bai san asibiti muka kawo Safeenah ba, da ba zai bari ba. Cewa zai yi a kyale masa ‘yarsa shi zai iya zama da ita a haka idan kowannenmu ba zai iya ba. Da gaske ba za mu iya zama da ita a haka ba, ba dare ba rana muna kanta. Kullum abin da za ta yi daban yake da na gobe. Yanzu ma cewa na yi za mu zo hutu ne wurin Uncle Hassan (ya nuna mutimin da suke tare) da ba zai bari ba.
Ni kuma ba don komai ba na tsaya tsayin daka wajen nema wa Safeenah lafiya ba, wallahi sai don kwanciyar hankalin Daddy. Na kudiri aniyar nema mata lafiya ko da duk abin da muka mallaka zai kare ba tare da sanin Daddy ba. Don haka, ka taimaka mana Dacta, da kwarewar da Allah ya ba ku, kada ku damu da kudi, daga miliyan daya har goma zan biya in dai zan ga ‘previous charming Safeenah’, ta kuma manta da KABEER DAMBATTA. Ka taimake mu likita, Safeenah is Daddy’s hope. Idan ta kashe kanta ta kashe mana Daddy. Wanda ke daidai da yi wa al’ummar da ba za ta kidayu ba da ke shan inuwa a karkashin Daddy asara, sabida ita kadai ranta.
Mutuwar Daddy a daidai wannan lokacin daidai ta ke da fitar Sarautar Alkaleri daga gidanmu, ta koma hannun makiyanmu. Domin daga ni sai Safeenah Allah ya bai wa Daddy, duk da nake namiji kuma babba, ba zan iya sarauta ba likita. Ni mutum ne mai son (simple life) da sha’awa a kan aikina matuka.
I’m a computer scientist (ni masanin ilimin kimiyar na’ura mai kwakwalwa ne. ina aiki da (Minting company) a gida Najeriya, ba zan iya hatsaniyar sarauta ba, amma ina matukar sonta ga tsohonmu wanda shi, ya gaje ta ne daga iyaye da kakanni gaba da baya, kuma shi kadai ne yake mulkar Alkaleri da gaskiya. Talakawansa na matukar kaunarsa, amma yana zagaye da adawar makiya.
Likita ina son sanin mene ne matsalar Safeenah a rayuwa. Don mu dai in banda dan iskan yaron nan ba mu san mene ne matsalarta ba. Kuma ya barta tun lokacin da lalurar nan ta fara samunta, ta soma bayyana a tare da ita. Wannan ya kara tuburar da Safeenah, kowa ya yi amanna da cewa Safeenah ta samu matsalar kwakwalwa ne a dalilinsa, domin kafin ya shigo cikin rayuwarta ba haka rayuwarta ta ke ba.
Safeenah rayuwa ta ke yi mai ban sha’awa ga kowa, yarinya ce da Allah ya yi mata baiwar fikira da hazaka tun tana kankanuwa. Daga firamare har sakandire Safeenah bata taba daukar na biyu ba, sai na daya. Haka abin yake har jami’a.
Tunda Kabeer Dambatta ya shigo rayuwar Safeenah, shi ke nan Safeenah ta koma tamkar wata tababbiya-tababbiya, mai-hankali-mai-hankali. Yau cikin nutsuwa da hankali, gobe cikin wasu abnormal abubuwa kamar surutai, juyewar idanu, sai ta kwana tana magana ba ta gaji ba”.
Ya yi shiru yana share hawaye da gefen rigarsa.
Idon Dr. Dangi a kan Safeenah, wadda har zuwa lokacin ba ta daina gursheken kuka ba da wasu maganganu cikin Turanci. Wani lokacin da Hausa, wani lokacin da Filatanci. A ciki za ka iya tsintar sunan KABEER DAMBATTA, cikin wata irin kakkausar murya mai nuna tsananin fushin da ta ke yi da shi.
Chapter 5 · 0% Book details