← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ASALIN ABDUSSAMAD HARUNA DANGI

“Na dawo Nanna, Na dawo Nanna, Nannata kina ina???”

Dan karamin yaron dan shekaru bakwai, sanye da farin yadin kofilin riga da wando da hula na makarantar firamaren gwamnati ta yaran garin Dambam yake fadi, yana shigowa cikin gidan nasu wanda ke zagaye da dangar kara da zangarniyar dabino.
Ta fito daga inda suka kira ‘mazagayi’ wato bandaki rike da buta da alama ta kama ruwa ne za ta yi sallar azahar.
“Oyoyo da dan-Nanna, maza a cire kayan makaranta ga ruwan wanka na dumama maka cikin tukunyar tuwo ka juye, duk ka yi futu-futu kamar ba Dan-Nanna ba’.
Ya yi dariya ya ce.
“Nanna Idi ne ya bula min yashi, ni kuma na shako shi sai da na tabbatar ya ji kamshin mutuwa sannan. Yanzun nan za ki ga Baffansa ya zo nemana”.
Cikin takaici Maman ta ce.
“Wato ba za ka daina gwada wa yara karfi ba ko Abdul? Na hana ka a tsokane ka ka rama da duka, na ce duk wanda ya tsokane ka ka zo ka gaya min ko wane ne zan je gidansu in gaya wa iyayensu su fita sabgarka, amma ba ka ji magana ba ko?”
Ba ta kai ga rufe bakinta ba suka ji gyaran muryar Baban Idi a bayan dangarsu yana fadin.
“Kina ina uwar shegen yaron nan mai cin zalin ‘ya’yan mutane? Fito da shi nan in ramawa Idi shakar da ya yi masa tunda dai Da bai fi Da ba”.
Idanunta suka yi rau-rau ta kai dubanta ga Abdussamad ta ce.
“Ka ji dadi yanzu ko? Tunda ka jawo min tijara”.
Ta janyo mayafinta jikin kyaure ta yafa ta fita ta tadda Malam Garba Baban Idi a waje. Ya kare mata tanadi tas! Kanta na sunkuye ba ta dago ba balle ta tanka, amma hawaye ta ke yi. A karshe ya ce.
“Wa ya ke son danki ya zo kusa da dansa ma balle har ya kai kazamin hannunsa ya taba shi? Dan shege da ba a san ubansa ba, ban da arzikin zaman lafiya da muka yi da marigayan iyayenki kina tunanin za mu barki ki zauna mana a gari ki yi goyon shege, har ki haife ki yi rainonsa cikin yaran karkararmu? To kin ci darajar Gyartai Hodijo da Landiya bayin Allah na gari da ba su taba barin abin kunya ba, shi ya sa muka kyale ki ki ke zaune da ke da shegen dan naki. Don haka ki gargade shi ya kiyayi kai kazamin hannunshi jikin ‘ya’yanmu tsarkaka ko da da gaisuwa ne ba duka ba”.
Tana durkushe har Baban Idi ya yi sababinsa ya gama, sannan ta mike ta share hawaye ta dawo cikin gida. Sai ta ji ta yi karo da abu. Dubawar nan da za ta yi Abdussamad ne ya labe yake jinsu.
Ya yi gumi kashirban jikinsa yana ta rawa.
“Nanna ki ce masa ya daina ce min shege, duka yara a makaranta ma shege suke ce min… Nanna ba na son sunan nan, Nanna ki ce su daina”.
Ta jawo shi jikinta ta rungume shi tana kuka yana yi. Aka rasa mai lallashin wani, amma sai ta tuna ita ce UWA dole ta bude zuciyarta ta karbi duk wani kalubale a kan danta, in dai za su rayu tare.
Ta ce, “Abdul?”
Ya dago ya dube ta idanunshi sharkaf da hawaye.
“Ka yarda da abin da zan gaya maka ka ji? Kai ba shege ba ne da ubanka. Ya mutu ne”.
“To ina danginsa Nanna?”
“Ba shi da dangi Abdul, don haka ba ka da DANGI!”
Ya sake rushewa da kuka.
“Ni dai ki kai ni wajen Babana Nanna in ba haka ba ba za su daina ce min SHEGE ba”.
“Zan kai ka babu Abdul? Na ce BABU! BA KA DA DANGI!! Ni ce uwarka, ni ce ubanka, kuma ni ce DANGINKA. In ba ka sona ne to ka je duk inda za ka, ni zan zauna ni kadai”.
Ya rungume ta da karfi, yana fada cikin kuka, don kukan da ta ke yi ya bashi tsoro.
“Na yarda Nanna, ni ba shege ba ne, Babana ya mutu, ke ce dangi na, ba zan sake tambayarki ba”.
Ta yi ajiyar zuciya a hankali, ta kama shi suka shiga daki.
A haka yaro Abdussamad ya girma, ga kyau, ga haiba da kamala. Ga son UWA da hidimta mata. Abdussamad shi ne wankin kayansa da na mahaifiyarsa, shi ne shara da wanke-wanke, har girki watarana shi yake musu. Ya je jeji ya yo mata itace, ya yi dako ya yi karen mota a tasha duk don ya taimaki mahaifiyarsa da karatunsa na sakandire.
Lokacin da ya zana jarrabawar gama karamar sakandire ya ci ‘science college D/Tofa’, makarantar na garin Dawakin Tofa ta jihar Kano. Nanna ta yi fadi-tashinta iri-iri har Abdussamad ya samu tafiya wannan makaranta, ya kammala a shekara ta (1990).
Sanda Abdul yake Dawakin Tofa kowa ya sanshi ya sanshi ne tare da Ishaq Barkindo, wani yaro dan wani babban dan siyasa, abotarsu ta zo daya ne ba don ajin rayuwarsu daya ba, sai don kwakwalwarsu da ta ke iri daya. Kowanne ‘quiz’ da kowanne ‘debate’ za ka ji daliban D/Tofa na fadin ‘Dangi’ da ‘Barkindo’ ne za su dauko mana kofin, haka kowanne ‘athlet’.
Lokacin da suka kusa gama makaranta Barkindo ya gaya wa Abdul cewa, mahaifinsa ya ce idan ya fiddo (9 credits) da ‘English’ da ‘Maths’ zai kai shi kasar Ingila ne ya karanci likitanci. Wannan magana ta dade tana yawo a zuciya da kwanyar Abdussamad.
Bayan sun kare makaranta ba su rabu ba, sukan ziyarci juna. Har Dambam Ishaq ke zuwa. Amma kullum Ishaq ya dubi rayuwar Abdul da mahaifiyarsa ya kuma dube shi shi kansa, sai ya ce, kana da karama. You didn’t look the way you are!’.
Rannan ya ce masa an fara shirye-shiryen tafiyarsa England, nan da watanni uku masu zuwa.
Hankalin Abdussamad ya tashi, ya kasa ci, ya kasa sha, ya kasa bacci a kwanakin har Nanna ta gane. Ta bi duk ta damu ta kuma aza a ranta kewar Ishaq da zai yi ne kawai.
A wani dare ta iske shi ya hada kai da gwiwa a bayan danga yana gursheken kuka. Ta isa har inda yake ta dafa shi, ta ce.
“Kukan me ka ke yi Abdul?”
Ya yi saurin share hawaye, yana boyewa bai so Nanna ta ganshi ba don ko kadan ba ya son tashin hankalinta. Ya kuma san tashin hankalin Nanna bai wuce ta ganshi cikin damuwa ba.
“Za ka gaya min Abdul ko ba za ka gaya min ba?”
Muryarsa na rawa hawaye na zuba, ya ce.
“Nanna, kin hana ni fada”.
Ta ce, “Me na hana ka fada?”
“Kin ce kada na kara yin zancen Babana”.
Nanna ta yi ajiyar zuciya, ta ce.
“Ba zancen Babanka na hana ka yi min ba, zancen DANGIN SA ne, shi ne wanda na hana ka, ba nasa ba. Tambaye ni duk abin da ka ke son ji a kansa zan gaya maka”.
Abdussamad ya sunkuyar da kai cikin in’ina yake magana da muryar da ta sha kuka ta koshi.
“…cewa na yi da ni ma ina da Baba…”
Ta yi saurin gyara masa.
“…kana da shi, ce ne da Babana na raye…”
Ya gyada kai cikin jin dadi.
“Da babana na raye, ni ma da ya kai ni karatu England”.
“Mene ne England?” Nanna ta tambaye shi.
Bai bata lokaci ba ya soma yi mata bayani.
“Wata kasa ce Nanna, mai tarin ci gaba, zaman lafiya, mutunta dan Adam, ilmin kimiyya da fasaha da ilmin zamantakewa makil a cikinta”.
Nanna ta yi shiru tana sauraren Abdul. Ta nisa a hankali can kuma ta ce.
“Ka sa a ranka ubanka irin uban kowa ne, ko in ce ya fi uban kowa. Shi ma ya yi maka wannan tanadin kamar ya san haka za ta faru, kamar ya san irin wannan ranar na zuwa. Tashi mu tafi wurin Ishaq ya kai ni wurin mahaifinsa”.
Nanna ta shiga dakinta da ke cikin gidansu na gado. Ta gaji dakin ne daga mahaifiyarta wanda aka yi rufinsa da azara da zangarniyar dabino. Ta daga gadon bonon mahaifiyarta wanda a yanzu ya zama nata ta janyo wata tsohuwar akwatin karfe ta sa dutse ta balle kwadon. Ta dauko wani kunshin zani ta kunce, sai ga jaka irin ta sojoji wadda suke daurawa a kwibinsu, tana nan sabuwa dal dinta yadda ta ajiye ta kusan shekaru ashirin da biyar ba ta canza ba, sai kura da ta yi. Ta daura ta a kwibinta, ta dora zani a kai ta yafa mayafi, ta ce.
“Mu je gidan su Ishaq Abdul”.
Daga tashar Dambam suka hau motar Kano, aka sauke su a tashar Na’ibawa, suka yi shatar mota zuwa Sokoto Road gidan su Ishaq karkashin jagorancin Abdussamad.
Chapter 12 · 0% Book details