← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** *** *** Abdussamad ya nisa a hankali, ya aje wata gwauruwar ajiyar zuciya lokacin da tunaninsa ya zo nan. Lokacin ya duba agogon motarsa ya ga cewa, ba karamin lattin tuki ya yi ba, kasancewar tafiya yake sannu-sannu, yana tunanin rayuwarsa daga kuruciya har girma. A daidai lokacin da ya hau titin ‘Oxford Circus’ don isa wajen aikinsa wayarsa ta yi kara, ya amsa da ‘earpiece’, Nanna ce. “Ya ya, ka isa lafiya dai?” “Na isa lafiya Nanna, yanzun nan zan karasa office. Ba za ku ji ni ba sai dare, ku wuni lafiya, ku yi min addu’a”. Nanna ta amsa, “Allah ya karemana kai a duk inda ka shiga, ka zo ka same mu lafiya kamar yadda ka barmu”. *** *** *** Yana shiga office ‘case’ na farko da ya fara samu na yaro ne dan shekaru goma, mai fama da lalurar ‘depression’. Wadannan matsaloli sun zamo gama-gari, ba ga manya ba, ba ga yara ba, kuma suna sanya Abdussamad cikin damuwa mai yawa a duk lokacin da ya yi katari da mai su, musamman ga kananan yara, uwar yaron ta ke gaya masa sai ya yi kwana uku bai yi magana ba, bai yi rubutu a cikin aji ba, duk yadda yara ke son haduwa da junansu su yi wasa shi ware kansa yake a gefe ya kalle su kawai. Wannan abu yana damunta, domin ba ta san me ya nema ya rasa ba a rayuwarsa. Kallon farko da Abdussamad ya yi wa yaron ya gano matsalarsa. Amma an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi. Don haka ya tambaye shi. “Azeez, where is your dad (ina babanka?)” Ga mamakin su duka a take ya bude baki yana magana. “Doctor I don’t have Dad. All my friends have Daddies. I want two parents, not only Mummy…”(likita banida uba, iyaye biyu nake so ba mummy kadai ba. Duk abokai na suna da uba). Abdussamad sai da ya ji tashi zuciyar ta motsa, ya tuna sanda yake damun Nanna a Dambun ina Babansa? Ya tuna irin damuwar da yake shiga har yau in ya tuna mahaifinsa da rashin danginsa. Wato shi Allah ne yake kare shi bai kamu da ‘depression’ din ba har yau. Zuciyarsa ta kara motsawa, motsawa mai ciwo! Shi ma yana son dangi tunda ya yarda Babansa ya mutu, amma dole ai yana da dangi duk da ba abin da Nanna bata yi masa ba a rayuwa. Atleast dai ya gansu, ya ji duminsu a kusa da shi ko da sau daya ne a rayuwarsa. Koda bazan bashi komai ba. Maman Azeez ta ce, “Doctor ba abin da ba na yi masa fiye ma da abin da kowanne uba zai yi wa dansa. Am I not enough for him?” Murmushi Abdussamad ya yi, domin sai ya ji kamar Nanna ce ta ke gaya masa hakan, ya kawar da tunanin tasa rayuwar daga cikin aikinsa, ya ce. “Yanzu ina Baban nasa?” “Na sake shi ne. tun ranar da na kama shi da ‘house girl’ dina na kai shi kotu aka raba mu”. Abdussamad ya ce, “Yana da kyau ki yi hakuri ku yi sulhu ko don lafiyar yaronku. Yana so ya kasance tare da ku ku biyu. Yafiyar laifin juna a aure dole ne ba don kanmu ba (iyaye) sai don yaranmu, rayuwarsu, walwalarsu da kwanciyar hankalinsu. Mu za mu iya samun sababbin abokan rayuwa mu manta da junanmu, amma su mun hada su da tawaya ta har abada. Kin fahimce ni Maman Azeez?” Ta gyada kai, cikin sanyin jiki. Ya rubuta wa yaron magani da zai sha kullum, ya kuma yi mishi albishir da cewa, Mummy za ta dawo da Daddy, a take ya fara dariya. Haka ya yi ta fama da marasa lafiya iri-iri masu matsaloli masu kamanceceniya da juna har zuwa ranar laraba da ya baro London zuwa gida Birmingham. Inda alhamis da juma’a suka kasance ranar aiki da ‘Spire-Little-Aston-Hospital’ da ke Birmigham. Washegari alhamis tun takwas yana office yana nazarin ‘folder’ din Safeenah yana karanta bayanan da ‘nurses’ din da ke kula da ita suka rurrubuta a kanta. Alhamdu lillahi akwai ci gaba. Ta sha magani na kwana bakwai cif ba tare da ta sani ba. Don haka da kwarin gwiwarsa yau ya tunkare ta. Ya kwankwasa kofar da yatsunsa biyu, sannan ya tura kadan yana fadin, “Assalamu alaikum”. Ta amsa “Amin wa’alaikumusssalam”. Sosai ya yi murmushi, don bai zaci za ta amsa ba. Ya idasa shiga cikin dakin. “Yi hakuri Aunty Safeenah, kin ce ni ma ba kya bukatata, to kawai sai na yi tunanin yau dai kwana bakwai ban zo ba, ko za ki bukaci abinci irin na gida, don su in kin fada musu ba sa iya fada daidai yadda zan gane, ko sun gaya wa mai dafawa ba ta ganewa”. Ta ce, “Gara da ka zo kuwa, ina son dan waken fulawa da mai da yaji, kuma ina so in yi wanka, duk jikina tsami yake min, amma duka famfon babu ruwan zafi sai na sanyi, ga shi ina jin sanyi sosai ba zan iya wanka da ruwan sanyi ba”. Ya yi hamdala a zuciyarsa, domin alamu sun nuna ta fara dawowa cikin hayyacinta. A fili kuma ya ce. “To me ya sa ba ki yi wa nurses magana su kunno miki ba?” Kai tsaye ta amsa. “Sabida ba na son yi wa kowa magana”. “Da suka yi miki wane laifin?” “Duk mutanen duniya munafukai ne”. Safeenah ki ji tsoron Allah, ba a taru duka aka zama daya ba”. “Humm, kada ka bata bakinka a banza, ba zan sake yi wa kowa magana a rayuwata ba. Ba zan sake yarda da kowa ba”. Ya mirgina kai. “Eh, na ji abin da ki ka ce tun rannan, amma ai a kan ‘maza’ kadai ki ka ce, shi ya sa na hada ki da mata su hidimta miki, su kuma munafuncin me suka yi?” Ta yi tsaki, saboda ya fara ba ta haushi. “Ba na so ana raina min hankali, su kuma wadannan halinsu kenan, ina kallonsu fa kullum suna kafa min ido suna rubutu, ina ruwansu da ni?” Ya yi dan murmushi. “Allah ya ba ki hakuri Princess Safeenah, daga yau ba za su kara ba, zan sallame su, amma fa (on only one condition” (a bisa sharadi guda). Ta dan bude masa fararen idanunta irin ina jinka din nan. Ya sake yin murmushi don ya lura har da jinin mulkin ke tasiri a dabi’unta. “Ni zan dinga zuwa ina kawo miki abincin da kaina da hannuna, daga yau har zuwa ranar lahadi, in kin amince to duk zan sallame su, kuma zan kunno miki ruwan zafi”. Ta ce, “Na amince”. “Yauwa Safeenah. To bari in je gida in sa Mamana ta yi miki dan waken, a hado da kunun gyada?” Da sauri ta gyada kai. Ya yi murmushi ya daga mata hannu ya fita. Ta muskuta ta gyara rufar bargonta ta kwanta. Yana fita ya kira Nanna, ya gaya mata cewa, ta yi dan wake ga shi nan zai zo ya dauka yanzu. Nanna ta dade cikin shiru da tsoron wannan al’amari na wannan maras lafiya, ‘yar masu sarautar Alkaleri, mutanen da ba ta da makiya ya su a duniya da lahira, yau ita ta zama mai dafa abincin da ‘yarsu za ta ci. Haka ta daure ta yi, fatanta a rabu lafiya. Ya zo ya dauka har yana tsokanarta wai ta yi ‘dying’ ne bayan ya fita? Bai ga furfura a kanta ba? Ba ta ba shi amsa ba sakamakon ta yi zurfi a tunani. Cikin kunun ya zuba magungunanta, wannan karon masu karfin gaske ‘stelazine, Artane’ da ‘carbamazapine’. Haka aka dibi kwana uku, wato alhamis, juma’a, asabar nanna na dafa wa Safeenah abinci kala-kala ba da son ranta ba. Ranar lahadi ya shigo asibitin da wuri, ya samu ta yi wanka ta yi fes! Amma fa kayan jikintan nan ta maida. Yana murda kofar yana shigowa ta yi wata ajiyar zuciya. “Yauwa Doctor, tun dazu nake jiranka, don Allah ka kira Yaya Khalil ya kawo min jakar kayana, doctor na jikina sun yi datti, they smell bad! A ce mutum ya yi ta zama da riga guda?” Ya yi murmushi, a fili ya ce. “Alhamdu lillahi”. Ya dube ta da murmushin kauna wanda bai san ta ina yake fitowa daga gare shi ba, a duk lokacin da ya dubi kyakkyawar fuskar Safeenah. Zuwa yanzu ya amince, bayan so na soyayyah zuciyarsa na yi wa Safeenah wata irin kauna da ta yi shige da ta ‘yan uwantaka. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta cikin taushin murya ya ce. “To Safeenah, ke fa ki ka ce su tafi ba kya bukatarsu, ni kuma a bisa umarninki nake”. Ta ce a hankali. “Raina ne kawai a bace a lokacin”. Ya yi murmushi, “Kin huce ke nan yanzu?” “Na huce. Ai Yaya Khalil na hannun damana ne, ban da Kabeer da ya zo ya shiga tsakaninmu, ya raba mu”. Cikin kulawa ya ce. “Safeenah, waye Kabeer?” Ta ciji lebe kafin ta ce. “He is my Ex”. “Ex-boy friend?” ya tambaya. “Ex-husband”. “Ashe kin taba aure?” Idanunta ya wani irin kada, ban da su likitocin kwakwalwa babu wanda ya san me kadawar idon Safeenah ke nufi, ya yi jajawur ya juye. A duk lokacin da aka tuna wa mai ‘schizophrenia’ wani abu da ya taba zuciyarsa yakan samu kansa cikin wannan juyewar idanun, wato ‘delusion’ ta fara karkacewa ke nan daga saitin da kwakwalwarta ta samu za ta soma amfani da (false beliefs). Muryarta ma canzawa ta yi, ta ce da shi cikin ‘delusion’. “Aure na biyu”. Zuciyarsa ta buga, domin dai shi dai ‘yan uwanta ba su gaya masa haka ba, ba shakka a yanzu tana cikin juyewar unani, wato (delusion da hallucination). Aure daya suka ce masa Safeenah ta yi. Ya ce, “To ajiye daya mijin a gefe, mu fara yin maganar na farkon, wato Kabeer Dambatta, don ina so na sasanta ku, ku koma wa aurenku…” Kai ta ke girgizawa cikin juyewar idanu. “Har abada ka daina wannan hasashen, mun rabu, rabuwa ta har abada kuwa, tuni muka rabu, na auri HABIBU SODANGI”. Ya yamutsa fuska, amma dole ya bi ta da yadda ta ke so, har a samu ta dawo cikin hayyacinta. “Who is that?”
Chapter 14 · 0% Book details