Sashe 17
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
“Sunana Abdussamad Haruna Dangi. Likita ne ni daga asibitin ‘Spire-Little-Aston’ na kasar Ingila, kuma ni ne wanda ‘case’ din tsohuwar matarka ke hannuna, muna nema mata lafiya, zan so ka ba ni hadin kai in samu wani dan ‘information’ a kan zamanku don zai taimaka min kwarai a kan ‘treatment’ din da nake yi a kanta don ganin ta koma ‘normal life’ dinta”.
Tsaki Kabeer din ya ja, wani irin mikakken tsaki, ji ka ke, ‘tsuuuuw!’ sannan ya dora.
“Wallahi na dauka wani abin arziki ne a yadda na ji muryarka ta mutumin da ya san abin da yake yi, shi ya sa har na tsaya na saurare ka. Allah wadaran naka ya lalace, tunda na sake ta me ye gamin katar dina da ita? Matsiyaciyar yarinya wadda ba ta san darajar aure ba, da aurenta tana soyayyar waya da wani Da namiji? Ta ina na rage ta? Auren Safeenah ko mummunar kaddara? Don ina neman mata hujja ce a gare ta da za ta ce za ta rama a matsayinta na matar aure?
Don Allah don Annabi Malam kada ka kuma kirana, in dai a kan wannan matsiyaciyar yarinyar ne. Wadda ba ta san darajar aure ba, me ake da wata Safeenah kayan haushi kwancen hauka? Ba ciwon hauka ba har ciwon zuciya sai sun taru sun hallakata. Yadda kuma ta karya zuciyata sai wani ya ba ta ninkin ba ninkin wanda ta yi min. Da yardar Allah tarihi zai maimaita kansa. Ni ko Safeenah za a ga wane ne dan halak, wane ne butulu?
Yesss! Na yarda Safeenah da mahaifinta sun yi min hanyar samun abinci amma basu suka azurta ni ba Allah ne, ba mai azurta wani sai Allah balle ace na yi mata butulci. Ban yi musu butulci ba ko kankani, in dai a zamana da Safeenah ne. Wanda ake tunanin ya zalunci wani tsakanin ni da ita Allah ya bi masa hakkinsa!”
Kirif! Ya kashe wayar.
Abdussamad bai yi fushi ba, don tuni ya gano inda matsalar ta ke. Ya sake kiran Kabeer din. Ta jima tana ‘ringing’ kafin ya daga a matukar fusace.
“Bawan Allah, in ba so ka ke in ci ta uwa da ubanka ba, to don Allah ka saurara min!”
Abdussamad ya kwantar da murya.
“Na yi maka alkawarin idan ka amsa min wannan tambayar ko da a takaice ne, ba zan sake kiranka ba”.
Sai ya yi shiru, da alama ya yarda ke nan zai amsa.
“Me ya hada ka da Safeenah? Ina nufin me ta yi maka ka sake ta?”
“Ban saki Safeenah don tana da tabin hankali ba kamar yadda iyayenta ke zargi. Ina zarginta ne da yin soyayya da wanina da igiyar aurena. Ke nan na yi daidai da na haramta wa kaina Safeenah duk da tarin alkhairan da ta yi min? Kamar yadda iyayenta da Yayanta ke tsammanin butulci ne na yi mata?”
Kan Dr. Dangi ya sara. A fili ya ce, “Wa’iyazu billahi… Kabeer ka yi amfani da ilminka mana? Ka gani da idonka akwai wanda ta ke soyayyar da shi?”
Ya ce, “Ban gani ba, amma na ji da kunnena, ba sau daya ba, ba sau biyu ba in suna magana a waya da wasu abubuwa da yawa. Don haka yadda ake shafe matacce a doron kasa a mance da shi, haka na shafe Safeenah da al’amarinta daga rayuwata. Ina fatan wannan ya zama kira na karshe da zan samu daga gare ka in dai a kan Safeenah ne, don Allah abokina”.
Abdussamad ya yi murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinsa. Daga Safeenah har Kabeer din tausayi suka ba shi. Magana yake da sauti mai nuna tsananin kiyayya, amma amon muryarsa wanda ke fitowa daga zuciya yana jaddada soyayyarsa gare ta. Wannan cuta ba ta yi ba, ta addabi al’umma, ta farraka masoya da dama, sai wadanda suka kai zuciya nesa ko ma’abota sani a kanta. Ya Allah ka ba mu ikon kawar da ita daga doron kasa alfarmar Nabiyullahi”. Ya yi addu’ar a zuciyarsa.
“Na gode Kabeer da wannan din ma, ‘atleast’ na samu abin da nake son samu bakidaya daga gare ka. Na gode (once more), kuma na yi maka alkawarin ba zan sake kiranka a kan Safeenah ba. Sai dai ka daina amfani da GAIBU, domin saninsa sai LILLAHI in ba haka ba kana tare da hakki da nadama a rayuwarka.
Kuma ina ba ka shawara ka yi bincike a kan cutar ‘schizophrenia’ zai taimaka maka watarana in ka hada rayuwa da mai ita”.
Ya ajiye wayar a gefe ya dafa goshinsa. Ya lumshe ido a hankali. Abin mamaki sai ga fuskar Safeenat Mahmoud na yi masa gizo, tana gilmawa a idanunsa. ‘A very innocent face’. Wasu irin ‘emotions’ suka ci gaba da zagaye illahirin jikinsa na tausayi, so da matsananciyar kauna. Wannan shi ne wani ya ki ka da wuni, wani ya so ka da kwana. Kabeer na yi mata wani zargi bisa abin da ita kanta ba ta da masaniya a gare shi, kuma ba ta san tana aikatawa ba. Wasu sassa na zuciyarsa ya ji suna rera masa sunanta, “SAFEENAH… SAFEENAH… SAFEENAH”. Cikin kunnuwansa. Suna wawaso mata muhalli mai girma cikin zuciyarsa. Wani matsanancin tausayi ya zo ya lullube shi da ya tuna cewa, duk fa wani kokari da zai yi ko yake yi Safeenah sai dai ta ji sauki, amma waraka na wurin Allah”.
“Ina sonki a haka Safeenah zan rayu da ke a haka har abada, in har za ki ba ni wannan damar”.
Idan Safeenah ta ji sauki ta ce tsohon mijinta za ta komawama, Abdussamad ya ya za ka yi? Kawai sai ya ji hawaye sun tarar masa a kwarmin ido.
“Allah kada ka nuna min wannan ranar”.
Ya mika hannu zai dauki hankici ya tsane idanunsa, hannunsa ya fada kan laptop dinsa. A take wanda aka saki Safeenah domin shi ya fado mishi a rai. Ya tabbata abin da yake tsammani haka ne, amma duk da haka yana son kore wa kansa zargi, yana son samarwa kansa zargi, yana son samar wa kansa ‘confidence’ a kan aikinsa da ita kanta Safeenahr. A take ya shiga ‘google’ ya sanya sunan Habibu Sodangi, minti biyu ta yi yawa bayanin mamallakin sunan da hotunanshi suka cika ‘screen’ din lafiyayyar ‘laptop’ dinsa.
“Habibu Sodangi is a solar power designer…” bayanin da aka fara a kanshi ke nan, sai tarihin rayuwarsa, kuruciya, karatu da girma, aure da ‘professionality’. Matashi ne da bai cika shekaru arba’in ba. Mai kyau da aji na misali da kwatance. Abin mamaki sai ya ji wani abu mara dadi da bai taba ji ba a kan mutum dan uwansa ya darsu a zuciyarsa da ya tuna cewa, wai fa a kansa Safeenah ke ‘delusion of love’. Shi bai santa ba, bai san ma tana yi ba. To kai me ye naka na damuwa da hakan tunda kai ma ba ta san kana yi ba? Wani bangare na zuciyarsa ya yi masa wannan tambayar.
Me ye tsakaninka da ita ban da likita mai ba da magani da mara lafiyansa? Zuciyar tasa dai ta yi saurin cewa, “A’ah, matsayin Safeenah ya zarta haka a gare shi har ya kai wani ‘limit’ da zai kasa boyewa kamar yadda yake ta kokari. Fatansa Allah ya bai wa Safeenah lafiya ya fallasa mata sirrin zuciyarsa’.
Ya janye wannan tunanin ya fuskanci abin da ya sa a gaba, wato bude ‘contact us’ cikin ‘website’ din. A nan kuwa ya ci karo da (email address) dinsa kamar yadda ya yi tsammani. Ya rubuta gajeren sako ya tura. Gabadaya ya kashe na’urar ya mike don gabatar da sallar magriba.
Abin mamaki, washegari yana shiga ofis da ya kunna na’urarsa sai ga amsa daga Habibu Sodangi. A gurguje ya karanta, “Ina zaune a garin Rumah ta jihar Katsina, asali na ke nan. Amma a yanzu haka ina kasar Japan ina yi wa ‘solar company’ aiki. Za mu iya haduwa duk sanda ka shirya a duk inda ka ke so, tsakanin Nigeria da Japan”.
Abdussamad ya nisa. Wani shaukin kasar haihuwarshi ya kama shi. Da a ce Nanna za ta barshi zai zabi su hadu a kasar Nigeria ne. yana son Najeriya fiye da kowacce kasa a duniya. Amma shi ma ya san hakan ba mai yiwuwa ba ne. In yana son ganin bacin ran Nanna, to ya ce su koma kasarsu. Ya rasa abin da ke binne shekaru kusan talatin a zuciyar wannan baiwar Allah, da ta kasa yafewa ta kasa mantawa game da wasu mutane can da bai sani ba. Dole ya zabi su hadu a Japan. Da ya yi ‘booking’ sai ya sanar da shi ya tabbatar masa zai dauke shi a babban filin jirgin saman ‘Hiroshima’.
Laraba da daddare ya shiga gida Birmingham, ya tadda Nanna da Suhail dinsa. Suka yi ta shaukin ganin juna kwana uku ba sa tare yakan zame musu ne kamar shekara uku ba su ga juna ba saboda soyayya da shakuwar da ke tsakaninsu. A nan yake gayawa Nanna gobe zai je kasar Japan duk dai a kan matsalar yarinyar nan ‘yar Sarkin Alkaleri. Amma kwana daya kacal zai yi.
Wani bakin ciki ya taso wa dattijuwar, ta dube shi cikin fushi.
“Ni yarinyar nan kanwar tsohonka ce ne? Tunda ka fara aikin asibiti ban taba ganin ranar da ka ce za ka je ko da garin ‘Reading Berkshire’ a kan mara lafiya ba, ba ka taba shiga damuwa a kan mara lafiya ba sai a kanta, ba ka taba zama na minti talatin a cikin gidan nan ba tun zuwanta saboda ita, sannan yanzu za ta fitar da kai daga kasar da tunda ka shigo cikinta shekaru ashirin ba ka taba fita ba. Duk ana me? A kan kwabon su? To ban amince ba”.
“Wallahi Nanna ba don kwabonsu ba ne, hasali ma ko sisinsu bazan karba ba”.
Ya samu kansa da fada ba tare da ya shirya hakan ba.
Nanna ta bi shi da kallon mamaki da tsoro, saboda ba ta taba fada ya mayar mata ba a rayuwarsu. Amma ko me ta tuna? Sai ta sassauta tata zuciyar jikinta kuma ya yi la’asar. Ba ta so ya zarge ta wani abu a kan yarinyar, sai ta ce.
“Allah Ya kiyaye hanya”.
Durkusawa ya yi a gabanta, kwayar idanunsa cike da nadamar musun da ya yi mata.
“Nanna, idan ranki ya baci da abin da na ce, ina rokon Allah Ya baki hakuri. Sannan ina rokonki ki ci gaba da karfafa min gwiwa a kan kowanne mara lafiya na. Nanna ba haka ki ke a kan kowa ba, why are you so harsh on Safeenah???”
Kamar ta ce da shi, “Kai ma da ka san wace ce da ba ta ishe ka duba ba, balle ka yi asarar muhimmin lokacinka haka a kanta, ka yi tsayuwar tsayin daka a kan lafiyarta. Mutanen da suka yi mana tozarcin da ko kare ba za a yi wa cikin al’umma ba. Amma a fili sai ta tausasa muryarta.
“Babu komai Baban Suhail. Kawai na ga aikinta na wahalar da kai ne, ka sani kuma ba na so ka wahala ko ya ya a rayuwa muddin ina raye”.
Wasu kwalla suka tarar mishi, na kauna da tausayin mahaifiyarsa. Mai sonsa da yawan tausayi a gare shi. Wadda ta zamo masa UWA, ta zame masa UBA, ta zame masa DANGi duk ita daya, kuma babu inda ta kasa. Ya daura hannu a kan tafin kafarta, ya ce.
“Nanna na, ho! Ai ba a nasara a rayuwa sai an wahala, duk wanda ki ka ga ya zama wani a rayuwa, kuma abin kwatance tambaye shi tsawon wane lokaci ya dauka yana yi, amma kada ki tambaye shi ko ya sha wahala ko bai sha ba, domin zai ce miki ne ya sha!”
Nanna ta ce, “Ai kai da ma ba a yi maka gwaninta, yanzun nan sai ka fi mutum baki. Ni matsa na tashi Allah ya ba da sa’a. Na daina magana a kan ‘yar gaban goshin likita daga yau insha-Allahu”.
Dariya ya yi yana hawa matattakalar da za ta sada shi da dakin barcinsa, amma bai tanka wannan zance na Nanna ba. Yes! ‘yar gaban goshinsa ce ya yarda, sai dai ‘it’s a pity’ tunda ba ta san ma yana yi ba.
Karfe biyar na asubahin ranar ya tashi zuwa kasar Japan daga ‘Heathrow Airport’ don saduwa da Habibu Sodangi, mijin kwakwalwar Safeenah.
****