Sashe 8
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dr. Dangi ne da Tiara (nurse on duty) a kan Safeenah. Da kanshi ya yi mata allurar da za ta kara nauyaya baccin nata, daga yau har zuwa gobe. Sannan suka sanya sinadarin narkakken abinci cikin cikinta ta hanyar amfani da wata siririyar roba (tube) ta hancinta, duk ba tare da ta san ana yi ba. A sannan ne ya samu ya baro asibitin a matukar gajiye.Ya tsaya ya yi (take away) na (KFC) da (McDonald) ya karasa gidansa. Nanna da Suhail suka bude masa kofa, kowannensu bakinsa ya ki rufo, don yau ya dade, dadewar da ya jima bai yi irinta ba. Nanna ta ce. “Lafiya dai ko Baban Suhail?” Ya zauna cikin kujerun ‘leather’ da suka yi wa falon kawanya cikin gajiya, ya ce. “Nanna, yau wata mara lafiya na samu daga Nigeria. Kuma in Allah ya taimake ni a kanta zan hada ‘project’ dina, don tana fama ne da cutar da na ke rubutun a kai da na dade ina neman wani muhimmin bayani a kansa”. Nanna ta ce, “To Allah ya ba da sa’a, ita kuma Allah ya ba ta lafiya. Ga can abincinka can bisa tebir”. Ya yamutsa fuska. “Bar ni yau Nanna, ba na jin cin mai nauyi, na yo guzuri (take away). Ku ma ga naku a sanya min abincin a firji zan yi sahur da shi in ya so sai na dumama da kaina cikin (microwave) in na tashi sahur din. Insha Allah gobe da azumi zan tashi musamman a kan Allah ya dora ni a kan matsalar yarinyar nan”. Daga haka ya mike ya bi matattakala zuwa samansa da ledar (take away) din nasa. Nanna na fadin. “To Allah ya ida nufi, mu kwana lafiya”. Ta dauki Suhail suka yi ‘toilet’ don ta yi masa wanka ya samu ya yi bacci. Da asubahin washegari yana bisa sallaya bayan ya idar da raka’atainil fajri kafin ya ba da faralin asubahi ya jero bukatunsa ga Allah Subhana, ya roke shi Ya dafa masa a kan aikin Safeenah da ya shigo hannunsa wanda yake jin dari-bisa-dari yake son taimaka mata ita da iyayenta ba don abin da zai samu kan aikin ba. Ya roka wa Maman Suhail rahma, ya kuma roki Allah da sanya masa danganar rashinta, Ya kawo sauyi na farin ciki a rayuwarsa kamar yadda Nanna ke buri. Sannan ya ba da faralin asubahi, ya kuma kara da wata nafilar raka’a hudu, ya karanta fatiha ya shafa. Daga nan kan na’ura mai kwakwalwa ya koma, ya ci gaba da bincike a kan matsalar Safeenah, wadda da ma a kanta yake yin ‘project’ din da ya gagara gamawa tuntuni. Yana da bukatar bincike mai zurfi da ‘experiment’ wato (gwaji) na zahiri a kanta, don tabbatar da cewa is she a schezophrenic kamar yadda yake tsammani? Duk wasu alamomin ‘schezophrenia’ dai ga su nan baro-baro a tare da ita. Zuwa karfe bakwai da rabi, Abdussamad Haruna Dangi na cikin motarsa kirar ‘Kia Picanto’. Mahaifiyarsa Nanna (Aisha) ta biyo bayansa ta sanya masa ‘basket’ din kayan abinci a bayan mota na karin kumallon da ya kasa tsayawa ya yi. Kai ka ce karamin yaro ne da zai tafi makaranta. Shi kansa ya rasa dokin fitar yau din na mene ne? Sai da ya yi tsam da ransa ya gane dokin ganin Safeenah ne. Wata kwayar mutum guda daya da ta yi wa zuciyarsa karan tsaye daga safiyar jiya zuwa wayewar garin yau. Ya rasa abin da ke jan zuciyarsa ga son yin tozali da ita. Nanna ta dago idanunta cike da kauna irin ta UWA ta dube shi, yana kokarin kunna motar, ta yi masa wata addu’a wadda rabon da ta yi masa irin ta in bai manta ba tun yana aji uku a jami’ar ASTON. “Allah ya sa wannan daukar wankan,wannan gayun, wannan kwalliyar da ka ci a yau ya sa ba za su fadi kasa a banza ba, za ka gano mahadin rayuwa wadda za ta dinga yaba su ba ni ba”. Ya yi hanzarin dagowa ya dubi Nanna, don sai ya tuna ranar da ta yi masa wannan addu’ar, ranar ne surukinsa Sanata Barkindo ya yi masa maganar Suhaila. Ya yi hanzarin sunkuyar da kansa daga kallon Nanna, cikin sanyin jiki ya yi ribos ya fita daga ‘compound’ din, Nanna bata kara ganin kwayar idanunsa ba. Dattijuwa Nanna, ta yi murmushi ta koma cikin gida, tana zance cikin zuciyarta. “Yaushe ne Abdussamad zai manta da Suhaila? Yaushe ne zai saki ransa ya samu madadin Suhaila? Yaushe ne zai amince wa ransa cewa Suhaila ta tafi ke nan ba za ta dawo ba? Wannan ita ce SOYAYYA BAYAN RAI! Ita kam Suhaila ta dace da miji mai sonta. Ban taba ganin mutum mai son matarsa har bayan ranta irin Abdussamad ba. Kodayake watakila hakan gado ne, ni ma har gobe haka nake son mahaifinsa tun daga shekarun kuruciya har yau da furfura ta mamaye gashin kaina ina begensa. Bayan rabuwar shekaru talatin ban kara kara sha’awar yin aure ba, kuma ba abin da ya canza har yau cikin raina. Sai dai ai ni tawa ta kare, me nake jira banda kyakkyawan karshe? Shi kuwa Abdussamad fa? Yanzu ne yake kan ganiyar kuruciyarsa, yanzu ne ya fara dandana rayuwa, ya kuma yi auren ya san dadinsa, rana daya mai rabawa ta raba ba tare da an shirya ba. Ina rokon Ka ya Ubangiji ka sanyaya zuciyarsa hakan nan a kan matarsa, Ka kawo wata cikin rayuwarsa wadda za ta sabunta farin cikinsa da walwalarsa. Ta kawo murmushi a kan fatar bakinsa…” ****** Cikin nutsuwa ya murda kofar dakin ya shiga. A cikin cikinsa ya yi sallama bai fito da ita fili ba, kamar yadda ya zata allurar baccin ta sake ta, tana kallonsa yana nufo gadonta, amma ba ta ce da shi komai ba, kar! Idonta a kansa. Tana zaune ne a tsakiyar gadon ta yi tagumi da hannayenta bibbiyu. Hawaye na ta ambaliya daga kyawawan idanunta. Dr. Abdussamad ya ja kujerar da ke gefen gadon ya zauna yana fuskantarta. A hankali ya soma magana cikin lallashi da taushin murya. “Sunana Dr. Abdussamad, likitan da zai kula da al’amarinki. In tambaye ki Safeenah… Safeenah ke musulma ce?” Ta dago jikakkun idanunta ta dube shi, amma ba ta ba shi amsa ba. Bai damu ba ya ci gaba da cewa. “Kin yarda ke musulma ce Safeenah?” Yadda ya yi maganar cikin tsananin kwantar da sauti sai ya sassauta mata zuciya. Ta daga masa kai wato ‘eh’. “Kin yarda da haka Safeenah ki ke ikirarin kashe kanki? Alhalin kina da masaniyar cewar, makomar kowanne musulmi da ya aikata hakan ko da ya shekara dari cikin musulunci ya mutu kafiri? Abin konawa a wutar jahannama? Safeenah don kin ga Babanki yana sonki ki ke son yin amfani da son ki hallaka shi?” Kukanta ya karu sosai, hawayenta suka kara gudu a kan kuncinta, ta ce. “Ka daina gaya min haka, ni ma ina son Daddy…” “...Ban ga alama ba”. Ya katse ta, “Da kina sonsa da baki dinga yin abubuwan da ki ka san za ki tayar masa da hankali ba. Da ba ki sa shi cikin halin hauhawar jini ba, da ba ki sa dan uwanki mai sonki Khalil ya yi fushi da ke ba…” “Yaya Khalil ba ya sona…” Ta katse shi cikin wani rurin kuka. “Zan yarda da abin da ka ce a kan Daddy, amma ban yarda kowa a duniya yana sona ba banda shi. Kowa munafiki ne. Kai I hardly believe if something like that (love) exist a duniya (ban yarda wani abu wai soyayya akwai shi a duniya ba). Sai yaudara da butulci kadai maza ku ka sani. Har shi Yaya Khalil din tunda ai shi ma NAMIJI ne. yanzun ma ai yaudarata ya yi ya kawo ni asibiti bayan cewa ya yi gidan Uncle Hassan kawai za mu je”. Murmushi Abdussamad ya yi, cikin nuna kansa da dan alinsa, cikin kwantaccen sauti ya ce. “Har da ni Safeenah?” Ta tattaro wata uwar harara ta manna masa irin ta (sannu wanda ya fado daga sama ba wanda aka haifa kamar sauran maza ba), a fili kuma ta ce. “Na ce Yaya Khalil ma, wa ka ke zaton zan cire a cikinku?” Ya yi dariyar da bai shirya ba, wadda rabonsa da yin irinta shi kansa ba zai ce ba. Domin ya jima bai yi irinta ba. Ya ce. “Yanzu Safeenah duk dadin da rayuwa ke da shi sai ki hakura da ita?Ki shige kabari saboda Kabeer Dambatta, wanda bai san kina yi ba? Bai san duniyar da ki ke ba?” Ta russunar da kwayar idonta kasa, cikin sanyi ta ce. “Ni ba saboda shi kadai nake so in kashe kaina ba. Amma har da shi a cikin matsalolin da suka taru suka yi min katutu, suka gadar da bakin ciki mai tsanani a cikin raina. Ya yi min butulci, sannan ko kadan bai yi min adalci ba a tsayin zaman shekaru biyu kacal da na yi da shi”. “Sai kuma su wa cikin wadanda suke sanya ki wannan tunanin na suicide? Saboda mene? Haka kawai ana zaune kalau, babu rashin ci, babu rashin sha sai mutum ya rataye, ya harbe ko ya gille kansa? Haba Safeenah?” Ta soma sheshshekar kuka tana fadin. “Su Yaya Khalil sun takura min ne, kowa ya tsane ni, kowannensu kallona yake MAHAUKACIYA. Kana ganin yadda suke danne ni suna daure ni da sarka, suna dura min magani, bayan na gaya musu ni lafiyata kalau. I need peace Doctor… ba dama in kama hanya in tafi inda nake tunanin zan samu peace din sai su bi ni su kamo kamar wata kaza…?” Ta sanya kuka mai amo sosai, ta kifa kanta a cikin kafafunta. Tausayi da wata matsananciyar kauna da bai san ta mecece ba suka shigi likita Dangi. Kodayake dama ta’adarsa ce (tausayin). Amma na yau na daban ne dana duk wasu marasa lafiyar kwakwalwa da ya duba a rayuwarsa. Ya kada kansa cikin girgiza shi. “Shi ke nan Safeenah cool down. You are now under my custody. Babu su Yaya Khalil masu sa miki damuwar nan. Yanzu me ki ke so a yi miki?” Da sauri ta café. “Kowa ya rabu da ni, kowa ya daina shiga rayuwata. Na tsani kowa, na tsani komai harda