Sashe 2
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Lokacin da karfe biyar na safiya ta buga tuni gari ya yi haske, ya ratso ta farin ‘curtains’ dindakin(labulaye). Ya kashe na’urarsa ya tura kujerarsa mai tayoyi baya, ya miqe tare da yin mika, sannan ya miqe sosai. Mintuna ashirin ya kwashe yana motsa jikinsa a kan injinan motsa jiki, amma fa yana jin sanyi mai ratsa kashi da bargo, duk da kakkaurar rigar sanyin (sweater) da ke jikinsa ruwan makuba da kakkauran wandon ‘jeans’ shudi, ga kuma (room heater) da ke ta aiki ba kakkautawa a dakin, sannan ya fada ‘toilet’ ya yi ‘brush’ yadda ya saba,yayi wanka da ruwa mai zafi har tururi yake daga shaya (shower) da ruwan sabulun ‘cien’ mai tsananin kumfa da kamshi, wato (liquid soap). Ya dauro shawul ya kuma dauki karami yana tsane kansa ya fito.
Yana iya jiyo kukan Suhail da muryar Nanna daga kasan bene, tana ta faman yi masa wakar lallashi, kai ka ce da babba ta ke magana. Ya yi murmushi shi kadai ya ce,
“Nanna amaryar Suhail”.
A gurguje ya yi shiri ya fesa turarensa kadan (Boss Intense), ya daura farar rigarsa ta likitoci a kan ‘suit’ din ta sauko har gwiwarsa. Sannan ya dauki ‘medicated lenses’ dinsa fari kar ya sanya kwayar idanunshi a ciki. Ya dauko komatsansa cikin bakar jakar goyawa ya fito, ya janyo kofar dakin, sannan ya gangara kasa cikin nutsuwa.
Nanna na goye da Suhail a bayanta ta juya baya tana tuyar kosai cikin mai a (gass- cooker), ta jiyo kamshin turarensa tabbacin ya shigo madafin. Ganinsa ke da wuya Suhail ya soma zillo daga bayan Nanna yana ta gwalantu yana mika wa Babansa hannu. Daga bakin kofa ya tsaya yana dariya, yana fadin.
“Suhail angon Nanna….”
Ba tare da ta juyo ba ta ce.
“Ba na auren, na sake shi. Jiya ko na minti daya bai bar ni na runtsa ba sabida abincinsa ya kare. Na dama masa kunu, amma yaron nan fafur ya ki sha, ya riqa furzo shi waje”.
Dariyarsa ta karu, ya shigo har inda suke, ta sunto masa shi daga bayanta ya karbi yaron yana fadin.
“Zan fito daga office karfe goma sha biyu, zan je ASDA in dauko masa ‘cereal’ dinsa, ke ma dai Nanna ta ya ya za ki ba wa bature irin Suhail kunu?”
Nanna ta ce, “Ko ba’indiye ne shi sai ya sha kunu. Ni ba na son kalan dangi. Ta ina ya zama baturen? Me ye hadin bafillace da bature in ba son sauya wa tuwo suna ba da kalan dangi?”
Shi dai Suhail tunda ya samu ya shiga hannun da ya fi so yake kyalkyatar dariya, ya manta da Nanna. Shi kuma Baban yana kissingdinsa waje-waje a fuskarsa yana manna shi a kirjinsa, yana lumshe ido.
Nanna ta karasa tsame kosanta ta kashe ‘cooker’ din. Ta dauki ‘plate’ ta zuba mai dadan dama daidai yadda ya saba ci. Ta dauko masa ‘flask’ din da ta cika da lafiyayyen kunun gyada mara sukari, sai lemon tsami kadan kasancewar ba ya shan sukari. Ta hada da kofi duka ta ajiye masa a kan tebir. Ya ja kujera daya ya zauna ya dora Suhail a kan cinyoyinsa suna ta hira cike da nishadi, yana biyewa gwalantunsa suna cin kosai.
Nanna ta koma gefe tana kallonsu cike da tausayi fal cikin kwayar idanunsa idanunta. Ta lura bai da niyyar maida hankali ya ci abincin hankalinsa duka yana kan Suhail, kuma zai makara, sai ta sa hannu ta dauke yaron daga cinyarsa ta yi falo da shi tana fadin.
“Ka hanzarta, ka makara fa”.
Ya girgiza kai yana murmushi ya bude ‘flask’ din kunun ya tsiyaya a kofin tangaran mai kauri (mug), kunun fari kal da shi, abin sha’awa kamar kunun madara ba na farar shinkafa ba.
Ya kai bakinsa ya kurba a hankali, gardin kunun ya ratsa bakinsa, ya wuce makogaronsa ya isa cikinsa,cikin ransa yana shiwa Nanna albarka, yana addu’ar Allah ya barshi da Nannarsa, Ya kuma kara mata lafiya da tsawon rai.
*** *** ***
Duk da ‘appointment’ din da yake da shi karfe biyu na rana daidai na duba wata yarinya da aka kawo daga kasarshi Nageria da babban likitan, kuma mamallakin asibitinda yake wa aiki(part time) wato ‘Spire-Little-Aston’ bakidayanta Dr. Trotter ya turo masa mara lafiyar domin ya duba ta kasancewar bangaren rashin lafiyanta yake, bayan da ya karbi takarda daga G.P din da ta gani. ya yarda ya karbi ‘case’ din zai duba ta a yau da karfe biyu na rana, amma tunanin ‘cereal’ din Suhail yana manne cikin ransa, ya kasa barinsa kwanciyar hankali. Rubutun da yake yi cikin ‘file’ din yarinyar ya tura gefe, ya duba agogon hannunsa karfe sha biyu daidai na rana.
Akalla yana da sauran awanni biyu kwarara kafin lokacin ‘appointment’ din, ya kintata ya ga cewa zai iya fita ya je ASDA ya sayi ‘cereal’ din Suhail ya kai wa Nanna, ya san tana can tana fama don Suhail ba sauki in dai yana jin yunwa. Ya miqe tsaye, makullin motarsa da wayarsa kawai ya zara ya fita, ya janyo kofar ofishinsa ya rufe da mukulli ya ba da mukullin ga sakatariyarsa ya fita.