Sashe 10
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Nanna (Aisha) ta saki baki tana kallonsa har ya bace wa ganinta. Bai kara fitowa ba sai washegari. Abincin daren jiya bai ci shi ba. Ko duk haushinta ne, ko ba ya jin yunwa ba ta sani ba. Ta san ba zai wuce ya cika cikinsa da kayan marmarin firinjinsa ba ne, ya sha madara ya kwanta abin da kullum ta ke masa korafin ba ya rike ciki.
Wayewar garin ranar ta kasance asabar ba ya zuwa asibiti. Amma sai ga shi ya fito ma Nanna cikin shiri na cikakken Bahaushensa. Shadda Wagambari mai launin sararin samaniya. Ta sha guga ta sha turaren ‘Boss Intense’. Ya karkata hula kalar kayan mai cizawa. Abinki da mutum mai launin fata mai kyau irin na mutanen Sudan, sai ya yi wani irin kwarjini, ya yi ‘fresh’ da shi.
Suhail ta ke bai wa (nutriend) amma sai ta dakata ta zuba masa ido. Ya karaso inda suke ya tsuguna a kan gwiwoyinsa yana gaishe ta da safiya. Ta amsa cikin rashin walwala, sannan ta ce.
“Sai ina kuma? Na ga yau ranar hutunka ce?”
Ya gyada kai, “Lancaster za ni Nanna”.
“Lancaster?”
Nanna ta tambaya cikin sanyin murya. Don tuni ta dago abin da zai kai shi.
“Me za ka je ka yi?”
Ta sake jefo tambayar ba tare da ta karbi amsar waccan ba.
“Kawai zan motsa jini ne Nanna. Na gama ‘project’ dina jiya”.
“Za ka je motsa jiki daga Birmingham har Lancashire bayan tarin kayan motsa jikin da ka cika a daki? Fadi gaskiya dai. Zan je makokin soyayyarmu ni da Maman Suhail a morecambe beach…”
Duk dauriyarsa a wannan karon sai da hawayensa suka diga a kan tafin kafarsa. Ya tsurawa mahaifiyarsa jan idonsa. Yana mamakin tarin kulawarta a kansa da rayuwarsa gabadaya. Ta yadda duk halin da yake ciki, duk wani motsinsa ta san inda ya dosa, kuma ta san me yake nufi, ko bai bude baki ya fada mata ba. Nanna ta kara kallonshi sosai.
“In dai don maganar da na yi maka jiya ne, na cewa ka hakura da Maman Suhail ka nemo abokiyar rayuwa haka ya janyo duk wannan, to Allah Ya ba ka hakuri. Amma ka koma ba za ka je bakin ruwan nan ba”.
Ya dago a mamakance ya dube ta, domin wani abu ne da ba ta taba yi masa ba, wato hana shi fita, tamkar wani yaron goye? Nanna ta yi kamar ba ta gane abin da yake fadi a ran nasa ba, ta ce.
“Gara ka zaga gari, kantina da makarantun jami’a, ko za ka gano wadda za ta maye maka gurbinta, ta hana ka TUNA BAYA. Abin da ya wuce ya riga ya wuce Abdussamadu, na gaba ake tara a fuskanta. Wannan shi ne cikar imani”.
A sanyaye ya mike ya koma saman nasa, madadin ya yi yadda Nanna ta ce, wato zaga birnin Birmingham zaben matar da za ta maye masa gurbin Suhaila, sai ya ga gara ya nutsa cikin binciken ciwon Safeenah wanda zai dauke masa hankali. Yana so ya kara fahimtar cutar sosai, don ya kara fahimtar ta sosai, shin itace ko Bipolar Disorder? Domin suna kamanceceniya da juna duk da bai fara gwajin da zai wa Safeenah ba.
Tuni ya fara fahimtar alamomin cutar a tare da ita. Ya dauko manya-manyan littattafan ‘psychiatry’ yana kara nazarin cutar ‘schizophrenia’ wadda ya tabbata ita ke damun yarinya Safeenah, kuma wadda yake cikin likitocin kwakwalwa na duniya da WHO ta nada suke yin bincike don kawo maganinta na fau-fau, wato na har abada a duniya.
‘Schizophrenia is a chronic psychotic disorder’ wato ciwo ne mai tsanani na kwakwalwa. Kalmar ta samo asali ne a shekara ta (1908) daga ‘Psychiatrist Eugen Bleuler’. Alamominta sune tsananin tunani, shauki a kan wani, rashin iya zabi tsakanin abu biyu, rashin hayyaci wanda ke janyo wa mai ita kebancewa daga cakuduwa da al’umma.
‘Schizophrenia’ cuta ce da ke faruwa akai-akai ga mai ita, wataran ta zo, wataran ta tafi. Mugun ciwo ne mara dadi. Tana hana mai ita yin wasu abubuwa, kamar wasu bangarori na ayyukan da ya saba yi a rayuwarsa. Eugen Bleuler ya ce, “It deprive the physical, moral, or intellectual strength of an individual”.
Masu fama da ‘schizophrenia’ sukan ji muryoyi wadanda sauran mutanen da suke tare da su ba sa ji. Za su amince cewa mutane suna karantar abin da ke zuciyoyinsu, suna da son su sa sauran mutane su bi ra’ayoyinsu. Suna yin zargin wasu mutane suna shirya musu muguntar da za ta cutar da su. Wannan zai firgita su ya sa su yi baya da wadannan mutane, alhali a zahirance ba haka ba ne.
Masu ‘schizophrenia’ ba sa amfani da hankali da tunani a yayin da suke magana. Za su iya zama wuni guda ba tare da sun yi motsi ko magana da kowa ba. A wasu lokutan kuma, ‘schizophrenic patients’ za ka gansu lami lafiya. Garau da su, amma fa sai sun fadi abin da ke zuciyoyinsu ko tunaninsu hankalinsu ke kwanciya. Wasu lokutan kuma ka gansu ‘very disturbed’ (wato cikin tsananin damuwa).
A wasu lokutan, masu ‘schizophrenia’ za ka gansu daidai cikin nutsuwarsu da hankalinsu in har sun amayar da hakikanin abin da suke tunani, ko yake damunsu.
Schizophrenia ta rabu kashi-kashi.
Simple Schizophrenia.
Residual type schizophrenia da kuma Catatonic Schizophrenia.
‘Catatonic schizophrenia’ ita ce wacce ta kunshi dabi’u masu tsanani irin su ‘catatonic excitement’ da kuma ‘catatonic stupor’. Wanda ke ragewa mutum ayyukan da ya saba yi, ya zama ba ya motsi, ya zama ba ya magana. Duk wasu al’amuran rayuwarsa da na ci gabansa sai ya katse su babu gaira babu dalili.
Akwai kuma ‘paranoid schizophrenia, schizo-affective disorder, schizophrenia form’ da lokaci ba zai barni in yi bayaninsu daya bayan daya ba. Duka rabe-raben cutar ‘schizophrenia’ ne.
Mai saukin ciki shi ne ‘post schizophrenic depression’. An fi samunsa ga mutane masu ‘schizophrenia’, wanda ya faru a baya mutum ya warke, ya koma (normal life) dinsa. Daga baya zai fahimci cewa (he’s attimes a mental patient) musamman in yana shan magani bisa ka’ida.
Abin da suke bincike a kai yanzu shi ne, ya ya za a yi a kawar da wannan cuta, ko a samu maganinta na har abada? Bayanin da ya bayar a nasa ra’ayin shi ne.
“Schizophrenia is not curable, wato cutar ba za a iya magance ta kwata-kwata ba, amma za a iya magance alamominta (delusion da Hallucination, etc) ta hanyar ‘social and vocational training’ ga mai matsalar.
By vocational training Dr. Abdussamad Haruna Dangi, yana nufin, a barsu a kan sana’ar da suke so, ko ilmin da suke so, ko kuma duk wani abu da suke da (experience) a kansa. Kada a hana su.
‘Social training’ kuma yana nufin koya musu cudanya da al’umma. Wasu daga cikin masu matsalar ba sa yarda su karbi ‘training’ din da ake son nasu da shi, musamman hulda da jama’a, shiga cikin mutane ‘yan uwansu da sauransu. Idan har za su karbi wadannan ‘training’ din zai taimaka ‘80%’ su samu lafiya, su yi rayuwarsu kamar sauran mutane. Zai taimaka musu su tuna al’amuran rayuwarsu masu muhimmanci su dawo cikin hankalinsu, kuma zai gyara musu kimarsu da kwazonsu.