← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ya tambaya. “Wane ne Habibu Sodangi?” ‘Wanda ka sani dai”. “The popular investor of solar powered laptops?” Da karsashi ta amsa. “Yes! He is the one!”. Sai Dr. Dangi ya saki baki yana kallonta cike da tausayi da wani irin kishi da ya soma cin zuciyarsa, ya ce. “To yana ina yanzu?” Ta ce, “Ya je England, gobe zai dawo”. “A ina za ku hadu?” “Na masa waya ya biyo ta nan ya dauke ni mu tafi”. “nan ina ke nan?” Ta ce, “Ba Lagos ba ne?” Ya ce, “A’ah Birmingham ne, England”. Sai ta yi shiru tana tunani, daga bisani ta ce. “Amma jiya da muka yi waya ya gaya min in jira shi a nan Lagos zai biyo mu wuce gida Katsina inda iyayensa suke. Ka san dan Katsina ne”. Ya gyada kai. “Kwarai dan Katsina ne. Ba ni wayar in dauki lambarsa in gaya masa kina nan Birmingham ya biyo ta nan ku tafi”. Ta ce, “Dadina da kai akwai kirki Doctor”. Ta shiga laluben wayar (alhalin fa ba ta da ita) lalube ta ke har da su karkashin filo, ta diro daga gadon ta duba kasansa babu waya babu dalilinta, sai hannunta ya fada bisa ‘remote’ din T.V, ta dauka ta mika masa, “Ga ta!” Ya yi murmushi ya karba ya latsa ya kunna T.V da shi, T.V ta kama aiki cikin raye-raye da wakokin larabawa. Ya dube ta, ta shiga mamaki. “Do you believe this is not a phone?” Ta yi shiru tana kallonsa. Ya mike yana mata kallon tausayi. “Zan wuce gida Safeenah, mamana tana jirana. Gobe litinin ba zan zo ba, jibi ma haka, gata ma haka, sai alhamis in Allah ya kai mu. Ki yi hakuri ki dinga karbar abinci daga hannun ‘nurses’ in na dawo zan ci gaba da ba ki da kaina”. Jikinta a sanyaye ta ce. “Ba komai, zan dinga karba”. Ya ce, “Alkawari?” Ta ce, “Eh, I promised you”. Can kuma ta ce, “Amma har kwana uku Doctor?” Idonta ya ciko da kwalla, amma ba ta kai ga zubowa ba, fuskarta ta nuna ta shiga damuwa sosai. Ya yi fatan ina ma a cikin hayyacinta ne ta yi wannan damuwar da shi? Da wane irin farin ciki zai samu kansa a ciki? “Kada ki damu Princess kamar yau ne. Ina yi wa babban asibitin kasa aiki ne a kwanakin. In zan dawo zan kawo miki tsaraba, amma sai kin min alkawarin za ki ba ni labarin rayuwarki da mijinki Kabeer daga farko har karshe, da kuma na shi ‘solar-powered’ don ni sunanshi kawai nake ji, amma ban sanshi ba. Ina kuma sha’awar ayyukansa ban taba ganinsa ba. Inda ku ka hadu, sanda ku ka yi aure, da ‘ya’ya in kawai. Da abin da ya sa babu wanda ya san kin aure shi sai ke kadai”. Ta ce, “Lah! Duk dangi an sani fa, ka taba jin inda aka yi aure babu sanin iyaye? Ai tun kafin rabuwata da Kabeer muka yi aure, yaya Khalil shi ya daura auren”. Abdussamad ya yi dan taku zai fice, don ya ga cewa ba zai iya ci gaba da jin wannan kwamacalar ta Safeenah ba. Ya kira ‘nurse’ daya ta kawo masa allura ya hada ya juyo ya dube ta. “Dan gyara ko? Allura za mu yi”. Ba ta yi musu ba, don ta ga babu alamun wasa a kan fuskarsa, ya yi mata allurai guda biyu, dama da hagu. Kafin ya fita ya ba ta ‘remote’ dinta. “In kun yi waya da daddaren, ki gaishe shi, kada kuma ki manta da alkawarin da ki ka yi min in na dawo zaki ba ni labarin kowannensu”. Ta ce, “Na yi maka alkawari Doctor Kirki”. Ta bashi dariya, “Sunana ke nan?” “Yeah, kuma allurarka ba zafi”. “Thank you Princess”. Ya ja mata kofar ya fita.
Chapter 15 · 0% Book details