Sashe 3
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana tafe a kawatattun titunan birnin Birmigham, birni na biyu mafi girma da kayatuwa a kasar Ingila, daga London sai shi a girma. Tituna kwance sumul marassa tudu balle gargada. Cikin nutsuwar tuki da nutsuwar zuciya wadda tsare ibada ke gadarwa mai su. Ta wani bangaren yana son kawar da tunanin da ke son yin fatali da nutsuwar tasa ne ko ta halin kaka. A lokacin da ya soma hango dogon ginin daga cikin ‘lenses’ dinsa masu karfi, ba na kara karfin ido ba kadai har ma da wanke rubutu ya fito tartar! Komai nisansa. Daidai lokacin da danja ta tsayar da shi a shataletalen da zai sada shi da ‘New-Street’ a dole so yake ya kawar da kai daga ganin dogon ginin da ke gabansa mai dauke da manyan rubutun da aka yi da ruwan gwala a kan dogon ginin da ke son tariyo masa rayuwarsa ta baya da ta riga ta shude. A like jikin ginin kafcecen agogo ne na azurfa wanda tsawonsa da fadinsa ya kai mita saba’in wanda aka gina tun shekara ta (1980). Rubutun da yake kauce wa ganin shi ne ‘ASTON UNIVERSITY’, amma bai iya kauce wa ganin nasa ba duk da kokarin da ya yi na kawar da kai daga ginin. Hakan bai hanakwayar idanunsa da ke cikin ‘medicated lenses’ din kasa karanto rubutun ba. Tuni fuskarsa ta yi kaca-kaca da hawaye a lokacin da danja ta basu hannu. Bai damu da ya share ba, haka hawayen basu daina shatata a kan kyakkyawar fuskarsa ba. Kuka yake sosai na baka da zuci, har da gunji da sheshsheka. Suhaila na gilamawa a idanunsa ta fito daga daukar lacca rungume da ‘folder’ tana murmushin nan nata, ‘dimple’ din da ‘cleft’ sun lotsa, tutsiyar karen ta dan fito waje. Kamshin ‘carolina herrera’ na tashi a hankali daga jikinta. Siririn bakin nan ya sha ‘AVON lipstick’. “…Duk duniya babu jami’ar da na ke so na ke alfahari da ita irin ASTON Dr. Dangi, insha Allahu, duka ‘ya’yanmu (would be Aston university Alumnae)”.Ta fadi a lokacin da ta ke shafar matashin cikinta. “…Zan cika miki burinki Suhaila… Insha Allahu Suhail zai halarci Aston, ko da wannan shi ne abu na karshe da zan gabatar a rayuwata”. Kalaman da yake maimaitawa ke nan har ya yi (parking) a inda aka tanada don adana motoci ga maziyarta shagon na ASDA. Ya fito ya rufe kofar motar da mukulli, ya shiga cikin dankareren shagon, bayan ya dauke hawayen fuskarsa da tafukan hannayensa guda biyu. Ya fito daga shagon rike da farar leda mai matsakaicin girma. A jikinta koren rubutu ne da manyan haruffa (ASDA). Cikin sassarfa da matsanancin hanzari, idanunsa sun rufe zuciyarsa ta yi duhu ta yadda har ba ya ganin abin da yake gabansa face ‘image’ na marigayiyar matar sa Suhaila. A sanda ta ke raye? Ina ya san zuwa kanti siyayya? Ya ya za a yi ya shiga (super market) shi kadai? Tukin motar ma ba kullum yake yinsa ba, shi dan gatan miji ne a wurin matarsa Suhaila. A kusa da ASDA shagon sayar da tufafi na MATALAN ne, inda Suhaila ke sayen kayan sanyawarta.Tabaron idanunsa (eye-lensess) ya hango masa wata rigar bacci ta mata cikin MATALAN a jikin mutum-mutuma da ake sanya wa riguna kamar mutum, sak! Irin ta Suhaila! Ya tuna ranar da ya zaba mata rigar ya ce da ita. “Wannan will suit my darling wife. Duba ki ga”. Ta bude dukkan fararen hakoranta masu kama da kankara don haske, tana dariya ta ce. “Allah angon Suhaila? Ni kuma sai na ga gara na sanya ta a cikin lefen da nake hada maka”. “Lefe?” Ya tambaya cike da mamaki da rashin fahinta. Dariya ta yi, tana mai kawar da kai daga gare shi. Ta jefa rigar cikin siyayyar da ta ke yi cikin kwando, ta yi gaba ta barshi a baya baki a bude, tana ci gaba da yi masa dariya. Bayan sun dawo gida, tana kici-kicin dora sanwar abin da za su ci ya dube ta. “Wai Suhaila abin da ki ka fadadazu a MATALAN, ni fa ban gane ba?” “Me na fada?” “Wai ki ka ce kina hada min lefe, lefen me? Lefan lafiya?” Dariya ta shake Suhaila ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska kamar ta yaba masa kashin shanu a fuskar. Cikin yanayin dariyarta mai shagaltarwa da gabunta na ‘ya’yan gata, ta ce. “Na rantse lefe nake hada maka, jiya ma na je ‘Liverpool’ na zabo atamfofi da ‘swiss laces’ duk na zuba a lefen. Yanzu haka takalma da jakunkuna suka rage min, su ma kuma ina jira a fara ‘sales’ ne don yanzu sun yi tsada”. Cikin sanyin murya ya ce. “Me ki ke nufi Suhaila?” “Aure zan yi maka”. Ta fada kanta tsaye, muryarta na bada amon iya gaskiyarta ta ke fadi. “In ke uwata ce ai sai ki yi min auren”. “Ba uwarka ba ce, matarka ce mai sonka da kaunarka”. Ta fada da wata irin murya da ya kasa bambance tata ce ko ba tata ba ce? Domin akwai wani abu cikin muryar tata mai kama da ba da ‘umarni’ wanda bai taba ji a muryar Suhaila ba. Tsaye yake a jikin bangon madafin ya harde hannuwansa a kirji, amma bai san sanda ya sulale ya zauna a daya daga cikin kujerun ‘dining’ din yana kallonta duk da ta bashi baya ne tana kwashe abincin da ta kammala dafawa. “Suhaila, wani abu ya shiga kanki, ina jin…” “Ai ku dama ‘psychiatrists’ ko magana mutum ya yi wadda ba ta gamsar da ku ba sunanshi mai rashin lafiyar kwakwalwa”. Abin nata sai ya koma ba shi dariya, ganin yadda ta ke ciccin magani kai ka rantse da Allah ita ce za ta daura masa auren wanda sam-sam hakan ba dabi’arta ba ne ba (cin magani). Kullum ‘pretty face’ din ta cikin yalwa take.Ya mike ya isa har inda ta ke ya daura hannu bisa kafadunta ya juyo ta suka fuskanci juna, suka yi wa juna kallon sakanni. A cikin kwayoyin idanunsu so da kaunar juna ne fal! Cikin nutsuwa ya kamo hannayenta biyu ya rike cikin nasa. “Gaya min dai, kin daina sona ne Suhaila? Ta yadda har ba kya kishina ki ke fatan kawo wata cikin rayuwarmu mai nagarta da fahimtar juna. Fata nagari lamiri Suhaila! Ko a aljannah ina addu’ar kada Allah ya hada ni da wata mace ba Suhaila ba!” Ga mamakinsa da ta dago idonta da ta sunkuyar hawaye ne share-share a kan fuskarta. “Wallahi za ka yi aure Dr. Dangi, na rantse da Allah za ka yi aure. Kuma za ka so matar kamar, ko ma fiye da yadda ka ke sona. Mafarkaina ba karya ba ne. Abinda ban sani ba shine ina raye ko bana rsye zakayi auren. I’m sure wani shafi na rayuwarka ta gaba da ke lullube Ubangiji yake nuna mini. Tana nan zuwa cikin rayuwarka ba da jimawa ba, kai dai ka yi shirin tarbarta a duk yadda tazo, kamar yadda na soma shiri ni ma. Muna namu ne Allah yana nashi, kuma naShin shi ne gaskiya, amma mutum bai isa ya tsara wa kanshi rayuwa ba, kaddarorin gobe yawa gare su. Son da muke wa juna bai zama hujja na lallai tare za mu karasa rayuwarmu ba. Don haka wannan gudunmuwata ce na ba ka Dangi, nake fatan ka karba da godiya”. A wancan lokacin ‘he is speechless, wordless, voiceless, wato ya ma rasa abin da zai ce ko kalmar da zai fada. Amma a wannan lokacin da ya fito daga ASDA ya hango MATALAN da wannan rigar ‘he is teary (hawaye yake yi). Abubuwa da yawa sun faru bayan nan, wadanda ke nuna Suhaila ba za ta dade cikin rayuwarsa ba. Kuma Allah ya nuna mata, sannan ta dade tana yi masa hannunka mai sanda da kukan kurciya iri-iri bai ankara ba, bai yarda ba sai a ranar da yake wanke gawar Suhaila!!! Da wannan tunanin ya dauke kai daga shagon ya kara har da gudu-gudu zuwa ga motarsa, sabida kukan da ya ci karfinsa. (Door-bell) ya dannawa Nanna ta zo ta bude. Bai shiga ba ya mika mata ledar hannunsa, ba tare da ya yi magana ba. Fuskarsa kawai ta kalla ta san abin ya motsa, ita ma ba ta yi magana ba ta mika hannu ta karba kawai, ya juya ya shiga mota ta maida kofar ta rufe ta koma ciki. Sha biyu da mintuna biyar ya shiga cikin ‘Spire-Little-Aston’ don haka sauri yake kamar ya tashi sama, don a ka’idar Bature bai san saba lokacin alkawari ba. Ya karbi mukullinsa a hannun sakatariyarsa. Yana zama ta shigo da ‘folder’ din ‘patient’ din da zai duba. Tana fadin. “Suna nan tun mintuna talatin da suka shige”. Karba ya yi yana dubawa kadan, ya mike ya fito ya shigo da su da kansa. Bayan da aka ba su takarda mai dauke da yarjejeniyar ganin ‘physician’ din, sun karanta sun amince da dukkan ka’idojin, sun kuma biya kudin da aka caje su (consultation fee) sun sanya hannu a kan amincewa da yarjejeniya. Mutum uku ne a zaune a kujerar ‘reception’ din, da alama sune masu ‘appointment’ din da shi. Bakar fata ne ‘yan asalin kasarshi Nageria, daga kallo daya ya fahimci hakan, ga sunan mara lafiyar kuma rubuce jikin ‘folder’ din, maza biyu da mace daya, sai wata babbar mace kuma a can gefensu da alama tana waya ne, amma ga dukkan alamu tare suke, tana sanye da riga da zani na atamfa ta yi lullubi da mayafi mai girma, daga gani ka ga cikakkiyar Hausa-Fulanin ‘Northern Nigeria’. Da ganinsu ko a Nigeria din manyan mutane ne, ko daga kamalarsu da kwarjini da irin sittirun da ke jikinsu. Hannu ya sa ya kira su suka mike da sauri suka biyo shi cikin ofishin har babbar macen bayan ta gama wayar. Da gani babban mutumin mahaifin ‘patient’ din ne, ko da ba su yi kama ba, saurayin kuma Yayanta, macen kuma mahaifiyarta ko da dai ita ma ba su yi kama ba da saurayin kadai ta yi kama. Yarinya kyakkyawa son kowa, mai cikar zati da kamala, ga ta a nutse ko’ina a jikinta hutu ke magana, kamar da ka taba jini zai yi tsartuwa, amma ba fara ba ce sosai (choculate in complexion), wato wankan tarwada.