Sashe 7
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ya dubi mutumin da Yayanta ya kira Uncle Hassan, ya soma magana cikin turanci (British Accent).
“Za mu kwantar da Safeenah tare da mu tsawon KWANA SITTIN. Wato watanni biyu. Ba za mu ce ga hakikanin ciwon Safeenah ba, tsakanin cututtukan kwakwalwa guda uku, har sai ta yi wannan wa’adin tare da mu, mun ga abubuwan da takeyi da idon mu idan kuna da halin hakan. Insha Allah Safeenah za ta samu lafiya ta koma rayuwarta kamar kowa. I’m sorry to say abinda baban Safeena baya so. Cikin ukun nan dole Safeenah na fama da daya;Bipolar Disorder, Schizophrenia ko kuwa ‘Post Schizophrenic Depression’. Wanda da yardar Allah za mu shawo kanshi kafin cikar wannan wa’adi da na fada. Ta hanyoyi guda uku, karantar matsalolinta, sauraron damuwarta, bin kowanne motsinta, magance mata damuwar da sanya ta a kan hanya (counselling), shan magunguna (anti-depressants) da ba ta sabon ‘hope’ a rayuwa.
Ban ce muku Safeenah za ta warke ne har abada ba, domin har yanzu (Science) bai kawo maganin wadannan cututtukan kwakwalwar ba. Amma za ta ji sauki in har ta zauna a kan (treatment). Duk dabarunmu da karfin ‘anti-depressants’ idan ba ku bar Safeenah ta tafiyar da rayuwarta yadda ta ke so ba, to akwai matsala.
Akwai yiwuwar ta tabbata a haka, akwai kuma yiwuwar ta kashe kan nata kamar yadda ta ke ikirari. Muhimmancin kwanciyar Safeenah a asibiti tsayin kwana sittin shi ne, za mu yi (analysing) duba matsalolin rayuwarta ne filla-filla a yi mata maganin kowane daya-bayan-daya. Na biyu sai ta zauna da mu ne za mu san (abnormal characteristics) dinta (abubuwan da ta ke yi da suke bambanta da na sauran mutane) tunda za ta yi ‘attempting’ kowanne mu gani. Za mu karanta Safeenah da halayenta, matsalolinta da kawo hanyar magance su, sannan za mu koya mata shan magani.
Shan magani ya zama dole gare ta, tana so ko ba ta so, (counselling) kadai bazai wadatar ba, dole sai an hada da shan magani. Kai daga nan har shekaru ashirin a gaba Safeenah ba za ta zauna lafiya ba tare da shan magani ba.
Babban abin da ke jawo matsalolin kwakwalwa ya hada da bacin rai, damuwa, hada wa kwakwalwa abubuwan da suka fi karfinta a lokaci daya. Sanya karfi wajen ganin cewa, sai an sauyawa mutum dabi’un rayuwarsa daga wadanda ya taso a ciki, wato (takurawa), rashin fadar damuwa ko matsaloli ga wani wanda zai kwantar maka da hankali, sanya karfi wajen sauya wa mutum ra’ayi da akida ba ta hanyar dabara da dadin rai ba, ko ta hanyar nuna soyayya.
Mutum mai gudun bacin ran mutane a kan halayyarsa zai iya samun (depression), hadiye bakin ciki ba tare da amayar da shi ba, matsalolin rayuwa, tilasta wa kwakwalwa ta karbi canjin da ba za ta iya karba ba duk suna haifar da (psychological disorders).
Shi ya sa Bahaushe ba ma Bature ba ya ce, ‘in ka san halin mutum, to sai ka ci maganin zama da shi’ ya kuma sake cewa, ‘hali zanen dutse’ ne, wato ba ya kankaruwa.
Kowanne dan Adam yana da ‘hali’, wato dabi’a ta halitta da Allah ke halittarsa da shi, kuma a duniya ba kowa zai iya jure halin dan uwansa ba, in ka dauke iyaye. Iyaye ne kadai za su iya jure halin ‘ya’yansu. Ba kowanne miji ne zai jure halin matarsa ba, ba kowacce mace ce za ta iya jure halin mijinta ba. Shi ya sa ake son fahimtar juna kafin aure, da sanin hali da dabi’un juna, ba kawai don soyayya ta hada a yi (rushing) a shiga rayuwar aure ba.
Shi aure ibada ne da ake yi da sanya ran cewa, ‘till eternity’ (har abadan-abadan) cikin kowacce ibada kuwa sai an sa juriya da hakuri da yafiya. Duk auren da babu wannan a ciki, duk kauna da soyayyar da ke cikinsa sunansa rusasshe.
Dan abin da na fahimta kenan daga labarin ‘yar uwarka da ka bani. Sauran binciken kan al’amarinta wannan aikinmu ne. Babu bukatar mai jinya a (Spire-Little-Aston) muna da ma’aikatan jinyarmu da za su yi wa mara lafiya komai kamar yana gaban iyayensa. Ku aikunku shi ne biyan (bill), za kuma ku iya zuwa sau daya a kowanne sati in kuna so ku ganta, amma ba yanzu za ku fara zuwan ba sai ta samu a kalla sati biyu ta fara samun nutsuwar zuciya”.
Godiya sosai Khalil da Uncle Hassan suke yi, kai ka ce kyauta za a nema wa ‘yar tasu lafiya. Ba su bar asibitin ba sai da suka biya makudan kudaden da asibitin ya caje su na ‘treatment’ din Safeenah. Ma’aikatan jinya suka kai ta dakin ‘aminity’ ciki daya ne da bayan gida, babu abin da babu na jin dadin rayuwa, kai ka ce a dakin wata matar gwamna ka ke a Najeriya cike da matsanancin tsaro, da matsananciyar kulawa.