Sashe 4
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tana da yalwar gassun gira da na ido bakake sidik masu taushi. Da gani ka ga fulanin Bauchi babu tambaya. Bacin rai ne kwance a kan kyakkyawar fuskar tata da wani irin yanayi da kallo daya ya yi mata ya karanto lalurarta. Su kansu sun yi mamakin ganin likitan dan Africa duk da fari ne amma ba can ba. Ga shi nan dai kamar Basudane, kamar kuma Maroccan. Ya nuna musu kujeru suka zazzauna bayan ya amsa sallamarsu. Dattijon zai fara bayani ya xaga masa hannu alamar dakatarwa idonsa a kan mara lafiyar. Mamarta na ta fama da ita a kan ta zauna a kujerar da ke fuskantar likita, amma ta ki. Kuma ta ki magana sai hawaye ta ke yi tana girgiza kai, tana tsane hawayen da gefen mayafinta. Uwar na fada cikin harshen Hausa. “Ko ki zauna, ko in sa su sa miki karfi, tunda ke ba a iya abu cikin kwanciyar hankali da ke”. Sai a wannan lokacin ta yi magana cikin kuka. “Wallahi ba zan zauna ba, don ban ga dalilin da za ku dinga yawo da ni asibitocin kwakwalwa ba, mahaukaciya ku ka dauke ni ko me? Ni lafiyata kalau, idan aka kara kai ni asibitin masu tabin hankali zan kashe kaina in huta…” Tana magana idanunta a warwaje babu alamun (respect) girmamawa ga matar, kwayar idanunta na wani irin juyawa kamar ba cikin idanunta suke ba. Yadda ta ke maganar da karfi bai jawo hankalin jama’ar da ke cikin asibitin ba, don sun saba da irinta. Dr. Dangi ya zuba mata ido babu ko kiftawa, bironsa a baki, kansa a karkace idanunsa a kaikace. Saurayin ya mike tsaye yana nade hannun riga. “ko ki zauna, ko na karya kafafunki SAFEENAH…” “Ba karaya ba, na ce maka zan kashe kaina ne wannan lokacin, ba kuma wanda ya isa ya hana ni, na gaji! Na gaji da abin da ku ke min…na gaji da rayuwar duniya”. “Ki kashe kan naki mana? Ke za ki mutu kafira. Amma kafin nan, sai kin dandana azabar karairayewar kasusuwa kin ji in da dadi maganin mai gardama”. Dattijon ya ce, “Khalil sa mata sarqa a kafafunta kawai in ta falle a guje ka sani sai dai jirgin zama”. Matar ta yi saurin fiddo mari a jakarta da kwado (padluck). Ganin haka ba shiri ta zauna tana wani irin kuka tun daga karkashin zuciyarta. DR. ABDUSSAMAD HARUNA DANGI wanda kowa ya sani da Dr. Dangi, ci gaba ya yi da kallon ‘patient’ dinsa da ta kifa kai a tebirinsa tana rusar kuka, wani irin abu na zagayawa a kwakwalwa da zuciyarsa, tsigar jikinsa na tashi a dalilin sautin wannan kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai imani. Har yanzu bai ce komai ba, amma tsigar jikinsa ci gaba ta ke da tashi, zuciyarsa na karbar wasu irin sakonni da ba ta taba karba ba ko a kan Suhaila in tana kuka. Wannan kukanta daban ne, yana fada cikin ransa duk wanda ya san lalurarki dole ya taya ki kuka, ‘Mental Health is totalhealth, you lose it and you lose all!!” Ya juya bangon ‘folder’ din yana duba sunanta, ‘SAFEENAT MAHMUD ALKALERI’. Ya lumshe ido a hankali yana maimaita kalmar ‘SAFEENAH’ cikin zuciyarsa, suna mai dadi da saukin fadi. Ta yi kuka, ta yi kuka bai ce komai ba, rubutu kawai yake a ‘folder’ dinta, ita kuma ba ta da alamar dainawa kamar za ta karar da dukkan hawayen da Ubangiji ya halicce ta da shi. Saurayin ya ce, “Likita, tunda muka sauka a kasar nan ta ki shan magani shi ya sa abubuwan ke ta’azzara, sannan tana yawan ‘attempting suicide’ don dai muna kula ne, kuma Allah yana karewa. Likitocinta na gida Nigeria sun ce a wannan ‘stage’ din komai na iya faruwa. Tunda mahaifinmu ya ki yarda su rike ta a ‘psychiatry’ sannan ba ta shan magani a gida a masai ta ke zubawa, shi kuma mahaifinmu ya ce sai bayan ransa,Safeena za ta kwanta a asibitin”. Sai yanzu ne Dr. Abdussamad ya yi magana. “Me ya sa ba zai bari ta zauna a asibitin ba (in such a critical situation)?” Sai da ya yi da gaske wajen boye mamakinsa jin likitan ya yi magana da harshen Hausa, cikin lafiyayyar Hausa mai taushi da dadin sauraro, bayan shi da Turanci ya yi masa magana. Bai bata lokaci ba ya amsa. “Sabida son da yake mata, har yau ya ki yarda Safeenah na da tabin hankali, cewa yake yi (aljanu) ne. Likitoci kuma sun ce babu aljani ko daya a jikinta. Haka Malaman addini sun yi ruqiyya ya fi sau a kirga babu aljanin da ya yi magana a jikinta”. “Shi ne wannan?” Ya nuna babban mutumin da suke tare, wanda a kalla ya yi shekaru hamsin a duniya. “A’ah ba shi ba ne, wannan abokin mahaifinmu ne da ke zaune a kasar nan. Ta hanyarsa muka san labarin asibitinku”. “Wannan kuma fa? Mahaifiyarta ce?” Saurayin ya sunkuyar da kai kasa. “Mamanmu ta rasu, step-mother dinta ce” (kishiyar uwa). Ya girgiza kai, ya koma nazarin takardar da suka zo da ita daga likitocin kwakwalwa na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, da ta GP din da suka gani a nan U.K yana tattare bayanan waje guda. Ya dago bayan mintuna biyu ya dubi saurayin da alamun bacin rai a kan kyakkyawar fuskarsa. “You are her biological brother, why are you treating her like this? (Kai dan uwanta ne na jini, me ya sa ka ke tafiyar da ita ta haka?) you are not soft on her (ba ka tausasa mata) har kuna threateningdinta da daura mata sarka, nunawa masu matsala irin ta Safeenah cewa su mahaukata ne shi ke kara ‘exaggerating anger’ dinsu ( shi ke kara ta’azzara bacin ransu). Safeenah ba mahaukaciya ba ce, ta san abin da ta ke yi, wani zubin bacin rai ne ya yi mata yawa ya maida ita haka. Lallashi da tausasawa ta ke bukata, shi kadai zai sanyaya mata zuciya”. Cikin nasa bacin ran shi ma saurayin ya mayar masa. “Ita ta ke kara tabbatarwa da duniya cewa ita mahaukaciya ce a kan SOYAYYAH! Don namiji daya a duniya ya ce ba zai zauna da ita ba sabida tana da ‘psychological problem’ sai aka ce shi ne karshen rayuwarta da za ta sanya wa ranta damuwa har ta taba kwakwalwar ta? Ilminta bai amfane ta da komai ba in haka ne, sai wulakanta kai da tozarta kai. Wallahi likita ba na tausayin Safeenah, kuma har abada ba zan ji ba, don ita ta siya wa kanta wannan halin da ta ke ciki da kudinta. Mahaifinmu kadai nake tausayawa wanda ya dauki soyayyar duniya ya dora a kanta, ya kuma damu da lafiyarta fiye da komai, shi ya sa nake karar da muhimmin lokacina, nake jinginar da muhimman ayyukana wajen nema mata lafiya don shi girma ya kama shi, ba zai iya ba, kuma ni ne babba. Sannan ga halin da yake ciki na rashin lafiya duk a dalilin lalurarta. Ban da haka Safeenah ba abar a tausaya wa ba ce, tunda ita ba ta san darajar kanta ba balle ta tausaya wa halin da masu kaunarta za su fada a dalilin shigarta cikin halin ha’u’la’i ba”. Dr. Dangi bai gane inda zantuttukansa suka dosa ba, abu daya ya fahimta shi ne, saurayin, wanda aka kira da suna Khalil zuciyarsa cike ta ke da bacin ran ‘yar uwar tasa, ta yadda har ba ya la’akari da cewa tana cikin lalurar da dole a tausaya mata. Ya mika masa hannu. “Ba ni magungunanta”. Matar ta sanya hannu cikin jakarta ta dauko su cikin kwalayensu, ta mika masa yana dubawa cikin nutsuwa, ya ga sun yi daidai da wadanda ‘consultant’ dinta na Nigeria ya rubuta a takardar tarihin ciwon nata, wato ‘tablets’ din (Artane, stelazine,carbamazapine, da kuma Aripipirazole). Ya dago ya dubi Khalil ya ce.