Sashe 6
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Dr. Abdussamad ya dauke ido daga kanta, ya tambayi Khalil.
“Wadanne irin abubuwa Safeenah ke yi wadanda suka tabbatar muku tana da matsala a kwakwalwarta?”
Ya fada da murya mai rauni, sanyin amo da na zuciya bakidaya, wadanda bai taba ji a kan kowanne ‘patient’ dinsa ba.
Zuciyarsa wani irin bugawa ta ke yi a duk lokacin da ya dora ido a kan ‘Safeenah’. Ji yake ba shi da wani sauran buri yanzu a duniya kamar na samun lafiyar Safeenah. Wani al’amari ne mai girma yake faruwa da shi a kanta, da bazai ce mene ne shi ba. Abdussamad ba ya taba sanya sha’anin mata a gabansa, balle ya dame shi. Tun kafin ya samu Suhaila da kuma bayan da ya rasata, amma a yau ga Safeenah ta zo masa da wani al’amari mai girma, da bai taba ji ko da a kan Suhaila ba. Bai gama kiyasce-kiyascensa ba ya tsinkayi muryar Khalil a cikin kansa yana ba shi amsa da cewa.
“Ga shi nan kana gani? Surutai, ta yi ta magana ita kadai ba kai ba gindi, ba wanda ya san a kan me ta ke maganar. Ta kamo nan ta kamo can babu daya kwakkwara cikin maganganun nata. Sai ta kwana tana magana ba ta yi shiru ba ko ta yi ta kuka babu gaira babu dalili, sannan ba ta bacci, ko ta kama hanyar Gombe a kafa tun daga Bauchi. Sai an yi sa’a ake samo ta, duk abubuwan da ta ke yi a da ta daina, wato karance-karance da rubuce-rubucen aikin jaridarta, wadanda a da ba ta iya rayuwa babu su.
Sai kuma abu na tsakanin miji da mata. Ni dai ba gida daya nake da Safeenah ba, ban da wannan lalurar da ta same ta sai in yi watanni biyar ban sa Safeenah a idanuna ba, sai dai mu gaisa ta waya.
Sai dai tunda ta fara abubuwa nake jin wai-wai daga bakin ‘yan uwa, duk da ana boye min, babu wanda ya taba tara ta ido-da-ido ya gaya min kai tsaye, don kowa yana shayin fushin Maimartaba da bacin ransa, don Safeenah ‘yar lelensa ce. Mata biyar ya saki a kan Safeenah a kan kuskure kalilan, wa ka ke tunanin zai tare shi da wannan al’amari da ya samu Safeenah bai shiga cikin littafin makiyansa ba? Ashe ana ta rade-radin da kumbiya-kumbiyar tun shekarar da ta wuce cewa Safeenah ta tabu.
Shi kuma mijinta Kabeer din, a nasa bangaren ya ce, Safeenah soyayya ta ke da waninsa ta ‘internet’ shi ya sa ya sake ta ba don abin da mutane suke fadi ba.
A takardar sakinta da ya rubuta, ya ce, bai saki Safeenah don tabin hankalinta ba sai don ba ta ba shi hakkinsa na aure, waninsa ta ke nema… kai maganganu marasa dadi, wanda mu mun yi amanna wannan ba tarbiyyar da muka yi wa Safeenah ba ce ta yi soyayya da wani alhalin da aurenta. Lamarin is mysterious (wanda ya gagara fahimta).
Sannan ya ce Safeenah ba ta ba shi hakkinsa na aure ne sabida shi wancan da ta ke nema, don haka ya kasa zama da ita. Domin dai shi ba jahili ba ne, amma Safeenah jahili ta ke kallonsa bayan ba ta fi shi ilimi ba, karewa ma, makarantar da ta samo ilimin shi ma a nan ya samo (ATBU) balle ta ce ta fi shi. Ya ce, tunda ya auri Safeenah tsayin shekara biyu zai iya kirga sau nawa ta bari ya kusance ta a matsayinsa na mijinta, shi ma kuma ba cikin dadin rai ba.
Kuma abinda zai ba ka mamaki likita da mu’amalarsu, Safeenah da Kabeer auren soyayya suka yi, ita ta kawo mana shi don tana sonsa. Mun rasa gane dalilin da ya janyo auren ya koma na kiyayya mai tsanani, domin Safeenah na da zurfin ciki. Ita ta kawo shi ga mahaifinmu ta ce nan duniya shi ta ke so.
Dukkanmu ba ma so saboda nasaba irin ta sarauta da ta talaka, banbancin a bayyane yake. Muna ganin Kabeer bai kai matsayin da zai auri Safeenah ba, domin iyayensa talakawa ne. Ganin ta dage, kuma Daddy ba ya son bacin ranta muka yarda da auren a bisa sharudda. Sharuddan su ne, ba yaji, babu korafi, babu kawo kara, ko ba komai yana da ilmin zamani za mu iya gina shi.
Tun bayan auren Safeenah ni ina Lagos inda nake aiki, na kan je gida kowanne karshen wata amma bama haduwa, farkon auren ta kan neme ni a waya mu gaisa daga baya ta daina, nikuma bana kiranta saboda har zuwa lokacin bacin ranta na auren wannan yaron bai sake ni ba, a ma sarautar mu faduwa ce mai girma dan sarki ya auri talakan sa, ban san me suke ciki ba.
Shekaru biyu bayan nan wani abokina ya yi min waya, wai ga Safeenah ya tsinta a garin Suleja kan hanyar shiga Abuja. Ya yi-ya yi ta yi masa magana ta ki yi. Na ce, don Allah ya rike ta kada ya bari ta bar hannunsa ga ni nan zan baro Lagos a jirgi mu hadu a gidansa da ke Kaduna. Na kira mijinta a waya na ce, ina Safeenah? Dan iskan yaron nan ko kunyar idanuna ba ji ba sai ce min ya yi, ya sake ta!!! Baisan a duniyar da ta ke ba.
A take na tafi Kaduna, ni da Sa’id muka sako Safeenah a mota sai Bauchi. Na gaya wa mahaifinmu duk yadda aka yi. In banda takardar sakin Kabeer da ke dunkule cikin hannunta har zuwa wannan lokacin babu komai a tare da ita. Ta iska ta bi ta tafi Suleja? A kafa ko a mota? Babu wanda ya sani sai Allah.
Sau uku Safeenah na fakar ido ta fice daga gidan mahaifinmu, na farko an samo ta a hanyar Gombe, na biyu aka samo ta a Kano, na uku a garin Shira.
Tun daga lokacin abubuwa suka ci gaba da habaka ga Safeenah daidai da tabarbarewar lafiyar mahaifinmu. Magani na gargajiya ba irin wanda ba a yi ba, kullum abubuwa maimakon su ragu sai kara gaba suke, abin da za ta yi yau daban da na gobe. The higher the ciwon Safeenah, the morekwanciyar Daddy a gadon asibiti. Shi bai yarda Safeenah ciwon hauka ta ke ba, jifa aka yi mata. Kuma ya sa an yi duk wani maganin sammun duniya da ruqiyyar duniya babu aljanin da ya yi magana a jikin Safeenah. Na yarda da ilimin likitanci… na yarda da likitocin Aminu Kano Teaching Hospital… kwakwalwar Safeenah ta tabu!!!”
Dacta Dangi ya yi wani dan juyi cikin kujerarsa, ya wurga ido ga Safeenah, sannan ya yi ajiyar zuciya. Zuwa wannan loakcin ta gaji da kukan ta yi shiru ta yi bacci mai nauyi a kan tebirinsa. Tana sauke numfashi a hankali, yarinya kamar ita ta yi kanta don kyau, haiba da kamala. Ko inda yake zaune (UK) inda ya hada al’ummatai kala-kala daga shiyya daban-daban of the global world (na daukacin duniya bakidayanta) ba ya jin ya taba katari da mace mai kyawu da ilhamar Safeenah!
Sai dai kash!It’s a pity!!Idan har ciwon da yake zato bayan wasu gwaje-gwaje da zai yi ya tabbata gaskiya a kan yarinyar za ta kare sauran rayuwarta cikin wahala, da zaryar asibiti. Don ma Allah ya tarfa wa garinta nono (she’s born with a silver spoon) wato ( ta fito daga inda za a iya daukar nauyin lalurar tata), ba don haka ba, dole abin da mahaifinta ke guje mata ya faru da ita (zama a psychiatric) ko kebance ta daga cikin al’umma don samun lafiyarta.