← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sanata Hashim Barkindo, Sanata ne da ke wakiltar Kano ta tsakiya. Tun a ‘gate’ Ishaq ya hango su ya sheqa da gudu suka rungume juna shi da Abdul, ya shigar da su har dakin mahaifiyarsa hajiya murja. Aka bawa Nanna daki guda don ta huta, ga abinci kala-kala, ruwa da lemuka. Shi kuma tuni Ishaq ya janye shi sun shige nasa dakin.
Sai washegari Hajiya Murja ta yi mata iso wajen Baban Ishaq da ta ce shi ta zo gani. Mutum mai fara’a da faram-faram da jama’a kamar kowanne dan siyasa. Ya gaida Nanna cikin mutunci da girmamawa, sannan ya ba ta damar ta fadi abin da ke tafe da ita.
“Na zo in ba ka amanar maraya kamar yadda Allah ya sanya amanar talakawa a hannunku. Duka abin da za ka gani cikin jakar nan mallakinsa ne, marigayin mahaifinsa ya ba ni amana domin in hidimta wa ilminsa ko bayan ransa.
Kwanaki ya shiga cikin damuwa, da na matsa da tambaya ya ce, dan wajenka abokinsa Ishaq ne zai tafi karatun digiri kasar Ingila, shi ma da yana da uba da ya yi masa. Na ce masa ubansa kamar uban kowa ne, mutuwa ce ta yi masa yankan kauna, amma ya san watarana wannan hidimar na zuwa, kuma baka da mai yi maka, don haka shi ma ya yi maka tanadinta, ka duba duk abin da ke ciki in har za su isa to, don Allah ka hada shi da Ishaqa ka yi musu komai tare, idan fa har ka yarda, Da na kowa ne, kuma amana a hannunku shuwagabanni”.

Sanata Barkindo ya dade yana maimaita sunan da ya gani, da sa hannun da ya gani da aka yi da bankin ‘firstbank’ tun shekara ta (1980).‘Manjo Janar Haruna Wakili Alkaleri’. Ya ambaci sunan tare da mikewa tsaye yana karewa Nanna kallo. Ba tsohuwa ba ce, wahalar rayuwa ce kawai ta tsofe ta. Kyakkyawar bafulatana ce ta kin karawa, me ye hadinta da ‘Late Prince Haruna Wakili’? Tambayar da ya yi a zuciyarsa ke nan, bai san cewa a fili ya yi ta ba.
“Mijina ne”.
Ta ba shi amsa a takaice, hawaye na ambaliya daga idanunta.
“Ya rasu wajen kare kasarsa da al’ummarsa, ya rasu da kyakkyawan kuduri a kan dansa, ya ba ni amanar dansa shi ya sa na sarayar da kuruciyata a bayan da na rasa shi, na kular masa da dansa wanda ba shi da kowa sai ni.
A wannan lokacin na zo wani geji da dole sai an taimaka min tunda ban san yadda zan yi na kai shi karatun inda yake so ba”.
“Baiwar Allah, ina ki ka kai dangin Prince ki ke wannan wahalar alhalin danki dan gata ne?”
“Ba abin da ya gama mu da su, Haruna ne da ma kuma babu shi. Ka yi wa Allah kada ka tambaye ni wani abu da ya shafe su, ka tambaye ni wanda ya shafe ni ko Da na zan fada maka, amma ban san komai game da su ba, kuma ba na so in sani, su ma ba na so su san da ni ko Dana har yanzu muna raye a doron kasa. Na roke ka ka taimake ni Sanata”.
Ta durkushe a gabansa tana kuka kamar na fitar rai.
Sanata Barkindo ya ce, “Yi shirunki, kwantar da hankalinki baiwar Allah, ya isa. Na fahimta, na fahimci komai ko ba ki min bayani ba. Kamar na so in san labarinku domin ni din nan da ki ke gani kafin in shiga siyasa tsohon soja ne, kuma mun yi zaman ‘barrack’ daya da ‘Late Prince’ a BukavuBarrack na shekaru biyu. Na sanshi, ya san ni. Don haka ki sa a ranki Abdul dana ne, yadda zan dauki nauyin karatun Ishaq haka zan dauki nasa.
Wannan dukiyar tasa kuwa hadata zan yi wuri guda in saya muku gida a kasar Ingilan ku tafi tare. Ba uwa irinki ake raba wa da danta a zauna lafiya ba. Abin da ya yi saura zan bude muku asusu a can don wasu bukatun, amma ban da na karatu, wannan na dauke su har in koma ga Ubangijina”.
******
Mafarin zaman Nanna ke nan da danta Abdussamad a garin Birmingham bayan da suka samu gurbin karatu shi da Ishaq, shi ya samu nasarar shiga ASTON UNIVERSITY, jami’a mai tsohon tarihi a kasar England. Ba sa tare da Ishaq don shi yana garin ‘Leeds’ sai dai suna ziyartar juna akai-akai.
Yana shekara ta biyar a jami’a Daddy, kamar yadda suke kiran Sanata Hashim Barkindo ya ba shi auren diyarsa SUHAILA BARKINDO. Bai yi musu ba, bai nemi ganinta ba ya ce ya amince, domin ba ya jin ko kuturwa ce in dai daga jikin Daddy ta fito zai kasa karbarta matsayin matar aurensa.
Suhaila wankan tarwada, mai matsakaicin tsawo, kyakkyawa daidai misali. Ta zo cikin rayuwar su shi da Nanna ta canza ta, ta kyautatata, ta armasata, ta kawatata da kyawawan halayenta. Shi da kansa ya samar wa Suhaila gurbi a jami’ar Aston fannin ‘Pastry- Art’ wato girke-girke, wanda shi ne sha’awarta, kuma shi ke dauke da nauyin karatun ba mahaifinta ba. Tsakaninsu da Daddy sai shawarwari a kan yadda za su inganta rayuwarsu.
Ranar da ya kammala MBBS, ranar Suhaila ta shiga shekarar karshe a jami’a.
Watanni biyu bayan nan ta samu cikin da ya zamto abin riritawa, ba ga ma’auratan ba, ba ga kakannin cikin ba, kowanne ya dauki so da buri ya dora a kan abin da Suhaila za ta haifa. A lokacin Yaya Ishaq (yadda Suhaila ke kiransa) ya kammala nasa karatun tuni ya koma gida Najeriya, ya yi aure, su kuwa da ma sun samu (resident permit).
Rayuwar Suhaila da Abdussamad rayuwa ce ta soyayya zallah, wadda aka gina saboda Allah da girman iyaye. Kullum suna bakin ruwa (beaches) daban-daban na kasar Ingila. Musamman ‘morecambe’ na ‘Lancashire, North Cornwal, Water gate Bay, Newquay, Weymouth beach’ da ire-irensu, suna karatu ko hutawa.
Sanda cikin Suhaila ya shiga watanni shidda ne ta soma yi ma Abdussamad ire-iren hannunka mai sanda da ya fada a baya, wanda ke nuni da cewa, ba za ta dade cikin rayuwarsa ba. Allah ya nuna mata hakan. Ta zo ne zuwa na wucin gadi, amma ‘memory’ na farin cikin da ta haifar cikin rayuwarsu ba zai taba gushewa daga zukatansu ba.
Suhaila ta rasu a ‘labour room’ na babban asibiti (Queen Elizabeth Hospital Birmingham) a yayin da kanta ke bisa cinyar Abdussamad mintuna goma bayan ta haifo danta namiji mai kama da ita, amma duk wasu ‘attributes’ dinsa nasa ne. mutuwar da ta gigita hankali da tunani da zukata na miji, iyaye, ‘yan uwa da suruka na wannan baiwar Allah. Ta tafi da ruhin Abdussamad da duk wata soyayya da yake jin yana da ita a kan diya mace. Sai dai kamar yadda ya ce a baya, yana godiya ga Allah da ya sa Suhaila ba ta barshi haka ba, ta barshi da sanyin idaniya mai sanyaya zuciya, wato (Hashim) Suhail.
To kuma ga shi a yau zuciyarshi na farfadowa daga magagin rashin Suhaila, har tana darsa masa wani sabon abin da ya jima da binnewa, wato soyayyar mace. Tun dai daga ranar da ya dora ido a kan Safeenah ya kasa tantance halin da zuciyarsa ke ciki. Tausayi ne ko so? Bai sani ba.
Abin da ya sani shine, ya damu da ‘patient’ din tasa, damuwa mai yawa da bai taba yi a kan mace ba bayan Suhaila, Safeenah ba ta san yana yi ba, hankalin nata gefe da gefe ne duk da yana da tabbacin kafin kwana sittin din da ya diba za ta koma daidai, cikin hankali da nutsuwarta. To shin, za ta karbi al’amarin da zai zo mata da shi, ko za ta tankwabar? Ya farantawa kansa ya farantawa Nanna? Allah shi ne masanin gaibu.
Chapter 13 · 0% Book details