← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*** *** ***
Ya kammala tattara bayanan ya dora a yanar gizo, yana jiran wani experiment na zahiri da zaiyiwa Safeenaya rufe babi na karshe da su a ‘project’ din da yake yi, wanda ya kira da suna ‘LIVING WITH SCHIZOPHRENIA’.
Da ya duba agogo sai ya ga azahar ta yi, zai iya zuwa masallaci tunda akwai sauran lokaci, kasancewar garin na Birmingham gari wanda ya fi kowanne yalwar musulmai da yawan masallatai a Birtaniya.
Cikin sujjadarsa yake rokon Allah ya taimake shi ya zamo daya daga cikin wadanda za su rage yaduwarta a duniya, ko da ba su yi nasarar (eradicating) share ta daga doron kasa ba. Domin hakika masu dauke da ita suna wahala. Iyayensu da mazajensu har ma da ‘ya’yansu na yi. Idan mata ne ba kowane namiji ne zai iya zama da su ba, daga mai ilmin zamantakewa (sociologist) sai mai ilimin dabi’a da tunanin bil adama (psychologist), ko mai ilmin lafiyar kwakwalwar dan adam (psychiatrist).
Yana fitowa daga masallaci wayarsa ta yi kara, yana mai ci gaba da tafiya don isa ga abin hawarsa ya daga wayar. Katheryn ce, wato ‘nurse’ din da ke kula da Safeenah.
Tun ba su gaisa ba yake tambayarta.
“Ya ya dai Katheryn, ba matsala tana karbar abincin ta ci?”
Da karsashi Katheryn ta amsa.
“Eh, tana karba. Amma yau da safe ta ki cin duk abin da aka ba ta, wai sai wani abinci ta ke fada, wai shi ‘kumbubus’, shi kawai ta ke so, in ba haka ba na sake zuro mata abincina za ta fasa min kai”.
Dariya ta kama Dr. Dangi, yana kokarin cankar me harshen baturiya Katheryn yake nufi da ‘kumbubus’ a karshe ya gane Safeenah na nufin ‘Alkubus’ ne watakila.
Ya ce, “Ki ce mata za ki yi mata kumbubus din zuwa biyar na yamma. Ta yi hakuri ta ci wanda ki ka ba ta. In ta ki ki kyale ta har na kawo. Ke dai ki kula da narka magungunan cikin abin shanta”.
Ta amsa, suka yi sallama.
Ya iso gida ya tadda Nanna da Suhail dinta sun sha wanka. Cikin fara’a yake sosai, irin wadda bawa ke kasancewa a cikinta duk lokacin da ya gana da Ubangijinsa.
“Nanna amaryar Suhail, inyee! Kun sha gayu”.
Nanna ta harare shi, ya yi dariya ya mika wa Suhail hannu ya dane shi da hanzari suka yi saman bene yana fadin.
“Mu je mu kulle kofarmu mu sha sweet Suhail mu koshi kada Nanna ta hana mu saboda ita ba ta san dadi ba”.
Nanna na jinsu sai ta yi murmushi, cikin ranta ta ce.
“Ku fara zawayi kuma ku tafi asibiti ku kadai, wannan karon ba rakiyar tsohuwa Nanna, tunda ba kwa jin magana”.
Bai jima da hawa ba sai ga shi ya sauko da sauri, lokacin Nanna tana madafi. Daga bakin kofa ya tsaya bai shiga ba.
“Nanna alkubus za ki yi min yanzu, daidai cikin mutum guda”.
Nanna ta juyo ta dube shi.
“Me za ka yi da alkubus kai da ba ka sonshi?”
“Ba ni zan ci ba Nanna, mara lafiyata ce da na ke gaya miki ‘yar Najeriya”.
Ta ce, “Au Hausawa ne?”
Ya ce, “Sosai ma, ‘yan Bauchi ne daga masarautar Alkaleri.....,,…”
Ji ka ke tush-tush! Nana ta saki kwanon tangaram din da ke hannunta ya kwankwatse a kasa, ya kuma yanke ta a kafafunta biyu.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. In ji Abdussamad.
Da gudu ya shigo madafin ya kama mahaifiyarsa ba tare da ya damu da kwalaben ba ko kada shi ma ya yanke. Ba don akwai ‘bed-shoe’ a kafarsa ba da shi ma ya yanke. Ya fito da ita falo jikinsa yana ta rawa kamar ba likita ba, ya rasa takamaiman taimakon da zai ba ta, sai jera mata sannu yake. Ban da gumi da Nanna-Aisha ke yankawa ta kowacce kafa ta jikinta ba ta komai.
Sai dai Abdussamad bai lura ba don ya tafi sama dauko ‘first aid box’ ne. ya dawo kuma ya maida hankali a ba ta ‘treatment’ ba a duban yanayinta ba. Ya cire wadda ta shiga cikin tsokar kafarta ya sa magani. Allah ya so bai yi zurfi sosai ba, ya rufe gurin da ‘plasta’.
Da ya kammala ya ce, “Sannu Nanna, laifina ne, da na dame ki da magana kina aiki”.
Ta ce, “Babu komai, je ka ka kwanta ka huta zuwa la’asar, ban ce ka kunna kowacce na’ura ko ka bude kowanne littafi ba, ko ka kunna waya. Ka yi bacci kawai, na amince karfe biyar ka sauko ka dauki abincin ka kai wa mara lafiyar”.
A ladabce ya amsa, ya kuma aikata yadda ta ce.
Bayan hawansa sama, Nanna ta ci gaba da safa da marwa tsakanin falo da madafi, hankali tashe. Ba ta son duk wata alaka da za ta sake hada su da Bauchi balle masarautar Alkaleri. Ga shi kuma dungurugum MASARAUTARTA kusa da gudan jininta.
Ba ta son duk wani abu da zai raba ta da danta ABDUSSAMAD ko na sakan guda ne. Kuma ba ta son duk wani abu da zai danganta Abdussamad da dangin ubansa. Mugaye, azzalumai, annamimai… ta fi son su kare sauran rayuwarsu a haka, a ba su da kowa, sai junansu. Me ake da masarautar ALKALERI ma’abociyar rashin adalci, rashin mutunci da tozarta dan adam?
To amma za ta hana shi aikin da shi ne madogararsu, marufar asirinsu a nan din? Bari kawai ta yi shiru ya yi aikinsa ya gama ba tare da ta daga masa hankali ba. Don ta san ba abin da yake bukata a duniya fiye da nutsuwa. In ta ce ya maida ‘case’ din hannun wani likitan in ya tambaye ta dalili me za ta ce masa?
Nanna Aisha, ta girgiza kai, ta mike cikin dafa bango don juwa da ke dibarta sakamakon jinin da ta zubar. Ta shiga madafi ta soma hada alkubus din. Bai dauke ta mintuna talatin ba ta kammala.
Karfe biyar daidai ya sauko cikin shirinsa tsaf, a ‘very smart guy’. Bai yi shigar ‘coat’ ko nektayil ba, sassaukar shiga ya yi ta rigar (shirt long sleeve) ruwan madara an rubuta ‘calvin klien’ da shudin wando ‘DKNY’. Ya fesa ‘Boss Intense’ dinsa. Ya sanya farin ‘lenses’ dinsa mai kara fiddo zahirin kyansa da kwarjininsa.
Da Nanna ta dago ido ta dube shi a wannan lokacin sai da gabanta ya fadi, domin gabadaya ya juya, ya rikide mata zuwa mahaifinsa, jinin Alkalerin ya fito sosai kamar na dukkanin zuri’ar Sarki Hamza mai Alkaleri.
Ta dauke idonta daga kansa da sauri sakamakon tahowar tawagar hawayen da ba ta san da zubowarsu ba. Ta dauko ‘basket’ din da ta adana abincin ta ba shi tana fadin.
“Sai ka dawo”.
Ba tare da ta yarda sun hada ido ba.
Ya yi dan jim, yana nazarin ta, sannan ya ce.
“Ina Suhail?”
“Yana bacci”. Yanzun ma ba ta dube shi ba.
Bai kawo komai a ransa ba don ya san hali. Watakila fillancin ya motsa ne, sai ya sunkuya ya dauki kwandon abincin (food basket) ya juya ya fita yana fadin.
“Sai na dawo”.
Sanda ya iso asibitin ana ta hada-hada a cikinsa kamar koyaushe daga wannan ‘department’ zuwa wancan kamar yadda ake yi kullum babu dare babu rana. Asibitin na kudi ne (private) da ke hayo kwararrun likitoci daga fanni daban-daban suna musu aiki suna biyansu. Don haka Abdussamad ma likitan haya ne, amma tabbataccen aikinsa (permanent job) dinsa a ‘Tavistock’ ne da ke cikin babban birni (London) wanda cibiya ce ta asibitin kasa (NHS). Shi da nurse on duty suka zuba duk sinadaran magungunan da suke son zubawa cikin abincin, ‘nurse’ din ta mika wa Safeenah ta taga. Daga inda yake tsaye yana iya ganin yadda ta ke cin alkubus din hannu-baka-hannu-kwarya alamar cewa lallai ta hora kanta da yunwa. Yana tsaye har ta gama, ta je ‘toilet’ ta wanke hannunta, ta dawo gadonta ta ja filo ta kwanta idanunta na kallon rufin dakin.
A hankali ya bar bakin tagar ya nufi motarsa ya kama hanyar gida.
Washegari da safe ya shirya ya yi wa Nanna sallama ya nufi asibitin. Ta taga ya hango ta tana karya kumallo, wannan karon cikin nutsuwa. Ya yi duk rubuce-rubucen da zai yi cikin ‘file’ dinta ya bar asibitin, ya nufo cikin gari.
Ya dankarowa Nanna cefane kasancewar karshen wata ne. suhail ma ya sha sayayya har da sabbin sittiru da rigunan sanyi, sannan ya dawo gida.
Wayewar garin ta kama litinin, rana ce da zai shiga ‘East London’ don yi wa gwamnati aiki(NHS). Ba ya aiki da ‘private hospital’ a ranakun litinin, talata da laraba. Yana aiki ne a ‘Tavistock and Portman’. (Foundation Trust ne wani bangare daga NHS dake kula da fiye da duk asibitocin NHS na Mental Health Services), yana duba yara kanana masu fama da ‘psychological maladjustments’ kala-kala. Abdussamad Haruna Dangi matashi ne dan baiwa, jajirtaccen mutum ne akan aikinsa mai yinamfani da baiwar ilmin likitancin kwakwalwar bil’adama ciki da bai dinta da Allah ya ba shi. Yana amfani da baiwar ta duk hanyar da zai ci amfaninta komai kankantarta ko girman ‘pay’ din ba ya rainawa, domin ba shi da dogon buri. In dai Suhail da Nanna za su ci duk abin da suke so su koshi, su sanya suttura mai kyau, ya cika motarsa da petir shi ke nan. Ya yi fice a lakantar aikinsa a cikin East London da Birmingham,masumatsalar kwakwalwa da yawa burinsusu ga Dr. Dangi. Haka asibitoci masu zaman kansu na son ya zamo daya daga cikin likitocin asibitocinsu.
Hatta turawan likitoci sun sara masa in dai a kan kwarewar aikinsa ne. duk da haka abin da yake samu din har ya fi karfinsa tunda a gidan kansa yake zaune ba na haya ba, babbar matsalar zaman kasar Ingila ke nan, shi Allah ya yaye masa ita, gidansa nasa ne na kansa. Don haka yana cikin wadata ta Ubangiji da rufin asirin rayuwa daidai gwargwado, ya fi karfin komai a rayuwarsa. Hazakarsa da himmarsa suka sanya ya zamo daya daga cikin ‘yan gaba-gaban goshin likitocin ‘National Hospital Services’ na kasar Ingila, duk da kasancewarshi ba dan kasa ba.
In zai iya tunawa, mafarin abin da ya kawo shi kasar Ingila har ta zame masa ‘refuge’ (mafaka) uwa ba da mama, kuma barin farin cikin rayuwa ba wani abu ba ne illa yanayin rayuwa mai daci da suka samu kansu a ciki shi da mahaifiyarsa shekaru ashirin a baya.
Ga shi a yau komai ya zama tarihi kamar ba a yi ba. Don haka Birmingham da UK bakidayanta yana kiransu ‘refuge from a rotten life’, ma’ana; mafaka daga rubabbiyar rayuwa. Mafarin al’amarin bai sanshi ba, don Nanna har gobe ba ta gaya masa ba. Shi dai ya san ya zo karatu ne yana saurayi dan shekaru ashirin. Lokacin da ya budi ido ya ganshi gaban mace daya tamkar maza dubu (Nanna), ita kadai ya sani a matsayin komai nasa. Ta kuma yi masa rantsuwa da Ubangijinta da cewa, shi din BA SHEGE BA NE, AMMA BA SHI DA DANGI. Mafarin ke nan da ya sanyawa kansa suna ABDUSSAMAD HARUNA DANGI, wato shi ne ‘dangin kansa’. Nanna ta roke shi alfarmar kada ya taba tambayarta ‘danginsa’ in har ba ya raina kulawarta a gare shi ba ne.
Ba zai ce abin ba ya damunsa ba, don haka kullum yake maida kansa ‘busy’ a bincike da karatu da aiki. Sannan da ya shigo rayuwa ta masu jajayen kunne inda ba a dauki dangin da muhimmanci ba sai ya taimaka damuwar ta bi ruwa. Musamman shigowar Suhaila rayuwarsa da nata dangin wadanda suka kama shi suka rungume, suka zame masa dangin.
Har bayan ranta kuma ba su cire shi a dangin nasu ba, kamar yadda mahaifinta Sanata Kabeer Barkindo ke gaya masa a kullum.
Yana tukinsa ne sannu a hankali yana wuce kananan garuruwa irin su Coventry, Wolvermphton, Molton Keynes, Oxford da sauransu,yana tunanin makasudin shigowarsa wannan kasa mai tarin albarkatun kasa da zaman lafiya daga surkukin kauyen Dambam, ta kasar BAUCHIN Najeriya.
******
Chapter 11 · 0% Book details