← Book details Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ya koma gida a matukar gajiye. Ya zauna cikin ‘three-seater’ yana tunani. Nanna ta ganshi cikin damuwa matuka, ko Suhail ya kasa dauka. Ya kira Khalil ya ce da shi su hadu gobe a London a ofishinsa da ke cikin ‘Tavistock ’.
Ya ja kumatun Suhail ya wuce samansa. Ya sakar ma kanshi shaya mai dumi ya sanyo jallabiya ya bada farali, sannan ya sauko kasa, ya tadda Suhail da Nanna. Tare suka yi ‘lunch’ na tuwon ‘semo’ da miyar danyar kubewa da kifi ragin ruwa. Ya shiga kicin ya wanko hannu da baki ya dawo ya kunna T.V, tashar saudiyya ya kamo suna sallar magriba, ya dubi Nanna ya ce.
“Nanna, ina tare da wani aiki babba mai ban tausayi a gabana, ina bukatar addu’arki”.
Nanna ta ce, “Addu’ata kullum tana tare da kai, ba abin da za ka fuskanta ba ka yi nasararsa ba da yardar Allah har karshen rayuwarka. Amma wane aiki ne haka?”
Ya nisa, “Nanna, yarinyar nan ‘yar sarkin Alkaleri da na baki labari, matsalarta babba ce, fiye ma da zaton iyaye da ‘yan uwanta. Tana da duk wasualamomin‘schizophrenia’ mai tsanani.(delusion da hallucination). Ita wannan matsala za ka tsinci kanka cikin wata rayuwa ne kai kadai, daban da ta sauran al’ummar da ka ke tare da su, ka dinga ganin abubuwa na gudana cikin rayuwarka alhalin sauran mutane ba sa ganin komai sai kai kadai”.
A zuciyar Nanna ta ce, “Allah ya ninninka mata, Ya kara mata ninkin ba ninkinta. Yo da ma jinin Mahmuda ya za a yi ya zauna lafiya a duniya alhalin ya tozarta zumuncin Allah? Kwallaya ciko idonta.
“Allah ya kara musu wahala a rayuwarsu ita da ubanta da duk wani zuri’ar sarautar Alkaleri”.
A fili kuma ta dubi dan nata cikin fushi ta ce.
“To dole ne sai ka yi abin da zai wahalshe ka? Ka mika ta ga wasu likitocin mana ka huta? Ko kai ne kadai likitan kwakwalwa a duniya?”
Ya yi murmushi, “Nanna ke nan, ashe ba kya so in zamo ‘specialist’ na can sama? Ai sai da irin wannan ake samun karin kwarewa da karin girma. Kuma ba na jin zan kasa yadda na fara da nasara insha Allah da ita zan kare daga bakinki mai albarka”.
A gundire ta ce, “Allah Ya sa”.
Washegarin ranar an tashi da ‘snow’ dusar kankara ba a magana, sai zuba ta ke a ko’ina. Hakan bai hana shi yin wanka ba da ruwa mai tiriri, ya shirya cikin bakaken (jacket) ya sanya bakar hular sanyi sakar inji ta ulu, takalmin kafarshi musamman na irin wannan yanayin ne, wato ‘snow-resistant’. Ya isa London da misalin karfe goma sha daya na rana.
A ka’idarsa tun lahadi yake tahowa daga Birmingham duk sati ya wayi gari a East London ya shiga ofis akan lokaci. Amma wannan satin da duniyar Safeenah ta sanya shi gaba, ta gigita shi bai san ya aka yi ya kasa tahowa a jiya ba, kodayake bai baro wajenta da wuri ba.
Inda Allah ya taimake shi yau ba shi da ‘appointment’ da kowa bayan Khalil Alkaleri. Shi da Khalil suka kulle kansu a ofis. Da kanshi ya hada musu ‘coffee’ mai zafi, ya bawa Khalil nashi, ya rike daya a hannun shi ya ce.
“Jika makoshinka Ibrahim Khalil”.
Suka fara kurba suna ajewa. Dr. Abdussamad ya ce.
“Khalil bayan rabuwar Safeenah da tsohon mijinta Kabeer ta sake yin aure ne?”
Khalil ya zaro ido, ya ce.
“Duka-duka yaushe suka rabun? Ba ta fi sati da gama idda ba”.
Abdussamad ya ce, “Ka san Habibu Sodangi? The designer of solar poweredlaptops?”(Wanda ya kirkiro kwamfuta mai aiki da solar?)
Ya ce, “Haka-haka na kan ji shi a kafafen yada labarai, kuma ina son fikirarsa, yanzu haka da ‘laptops’ dinsa muke amfani a ‘minting company’ kwanan nan aka zuba su”.
Abdussamad ya ce, “To a ‘hallucination’ da ‘delusion’ din Safeenah, shi ta ke ikirarin tana aure, wai har waya suke, ko jiya sun yi waya. Na nemi ta ba ni wayar ta bani (television remote) kuma fa ita a kwanyarta duk abin da ta fada daidai yake. Raba ta da wannan ‘illusion and perception’ din nata ba karamin abu ba ne, sai mun hada da nuna mata ‘reality’. Wato nemo wannan mutumin ya tabbatar mata bai santa ba, babu wata alaka a tsakaninsu. Wannan duk yana cikin ‘therapy’ din da za mu dora ta a kai, wato (counselling), a samu a raba ta da wannan tunani, ta dawo cikin tunaninta ta karbi rayuwarta ta gaske, ta watsar da ‘imaginary life’ dinta”.
Khalil ya ce, “Yo ma rabon Safeenah da waya an doshi shekara uku. Tun sanda ta fara shiga cikin wannan halin, sannan mu Kabeer kadai muka san ya auri Safeenah, Ya Sattaru, wane irin ciwo ne wannan? Dole wanda bai yarda da likitancin kwakwalwa ba ya ce aljannu ke ga Safeenah”.
Doctor ya ce, “Delusion’ ne kawai da ‘hallucination’ duka alamomi ne na ‘schizophrenia’, kuma insha-Allah zai wuce. Safeenah za ta dawo ‘normal’ kamar ba a yi ba.
Kafin haka dole zan nemo wannan mutumin ya tabbatar mata bai santa ba, bai da alaka da ita, bai taba alaka da ko mai kama da ita ba, shi kadai ne zai tabbatar mata da hakan ta yarda. Ina tabbatar maka har ‘sexuality’ ana gani cikin ‘schizophrenia’, za ta iya ganin har auratayya suna yi a cikin kwakwalwarta kafin ta yarda ta karbi gaskiya abu ne mai wuya, bayan magani da allurai sai an hada da ‘counselling’’.
“Ya za a yi mu samu magana da shi toh?”
Khalil ya tambaya.
“Zan shiga ‘website’ dinsa ba za a rasa ‘email’ dinsa ba. Zan nemi tattaunawa da shi a kan aikina (likitanci) a kan wata baiwar Allah da muke son ya taimaka mana. Zan je in same shi har inda yake I’m sure zai yarda mu zanta”.
Idanun Khalil suka ciko da kwalla, ya ce.
“Doctor, ina tausayin Safeenah fa, ko na ce bana yi to bacin rai ne. Ka taimake mu ka yi iya duk kokarin da za ka iya a kanta ta koma ‘previous’ Safeenah... Allah kadai ya san irin kyautar da za ka samu daga mahaifinmu idan haka ta faru, mu ga Safeenah yadda ta ke a da. Ni ma kuma na yi rantsuwa zan yi maka kyauta mai yawa, insha Allahu”.
Murmushi Abdussamad ya yi. Ya mike yana tattare takardun gabansa, ya ce da Khalil.
“Ni ma kuma na yi tawa rantsuwar da alkawarin ba zan karbi ko sisinku a kan Safeenah ba. Haka kawai nake jinta a raina. Wani irin ji mai yawa kamar na jima da saninta, ko na taba rayuwa da ita. Ba zan boye maka ba har kai. Ina jinka kamar kanina da muka fito ciki daya. Tun ranar da na fara ganinku na ji hakan a kanku. Don haka ka daina tunanin wannan babu shi a tsakaninmu da ku, ka sanya a ranka cewa, ni da ku mun zama daya. Sai ko kason asibiti, tunda ba asibiti na bane.
Sai abu na biyu, ina son ganawa da tsohon mijin Safeenah, wato shi Kabeer, don haka ka samo min lambarsa”.
Da haka suka yi sallama.

Ta waya Khalil ya turawa Dr. Dangi lambar Kabeer Dambatta. Yana kwance cikin ‘sofa’ a ‘terrace’ din ‘apartment’ dinsa da yammacin ranar ya kira Kabeer Dambatta.
Chapter 16 · 0% Book details