Sashe 1
Kwana Sittin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
KWANA SITTIN!
1
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
SADAUKARWA
Ga dukkan schizophrenics dake raye a duniya, wadanda ke fama da cutar schizophrenia. Suke rayuwa a cikinta da dukkan kalubalenta. Allah yasa ta zamo kaffara a garesu.
KWANA SITTIN-1
Za’a iya kimanta lokacin da misalinkarfe shidda na safe, cikin unguwar ‘Auckland Road’ yankin Smethwick (West Midland) cikin birnin Birmingham dinkasar England. Lokaci ne na azabar sanyi (winter), dusar kankara sai zuba ta ke a kan rufunan gidaje,kan titi da ko’ina. A kan tsaunuka kuma ta yi tsiri irin yadda ma’abota yawon bude ido ke son daukarta a hoto, ko masu daukar finafinai daga nahiyar kasar Hindu.
Gidan karami ne mai hawan bene daya, kwatankwacin sauran gidajen da ke layin. Duka gidajen da ke layin ‘Auckland Road’ iri daya ne, kuma girmansu daya. Akwai dan zagayayyen fili wanda ya dauke motar mamallakin gidan (parking space), sai kofar shiga. Kana bude ta za ka tadda matattakala (upstairs) wadda ta yi sama, in ka bi ta za ta kai ka dakunan bacci ne guda biyu, in ka sauko karkashinta za ka tadda matsakaicin falo ne, wanda ya qawatu da kujerun fata masu taushi da santsi, saitin kayan kallo da na’urar dumama daki (room heater), sai daki ciki daya da karamin bayan gida a cikinsa.
Kofar madafi (kitchen) tana gabas maso kudu na dakin. A cikin kicin dinkofa ce wadda za ta fidda kai lambu (garden) mai shimfide da korran ciyayi masu kawanya (grass carpet). Idan kana tsaye cikin kicin din ta fankaceciyar/wawakekiyar tagarsa kana iya hango illahirin lambun ciki da bai dinsa.
Cikin wannan madafi komai tsaf yake, babu tarkace, komai da ke cikinsa mai amfani ne na yau da kullum. Akwai firinji dogo (fridge) da gajere (freezer), sai (cooker gass) ta girki wadda (cabinets) suka sanya a tsakiya, (microwave) ta dumama abincin bature, (blander) wato injin markadesai ‘washing machine’(injin wanki). A gefe na’urar tace ruwa ce mai bada ruwan zafi da na sanyi.
Sai ‘yar kanta mai dauke da kayan girki, su gishiri; maggi, cooking oil (man girki), kayan kamshin girki (spices) na bature da na gargajiyarmu duk su ne a jere a cikin kantar. Sai famfon wanke-wanke (sink) mai kan famfo guda biyu mai ba da ruwan zafi ko na sanyi, ya danganta da wanda ka ke bukata.
Kai ba za ka ce tsohuwa ce ke amfani da madafin nan ba, sabida cikar tsaftarsa. A can gefe cikin kicin din teburin cin abinci ne mai cin kujeru hudu (dining table) duk a cikin wadataccen kuma tsaftaccen madafin.
A matattakalar da ta kai ka zuwa sama za ka isa dakunan bacci ne guda biyu, sai bayan gida daga gefe kusa da dankaramin ‘terrace’ da mamallakin gidan kan tsaya yana hango unguwar da motoci a bakin titi, kai kawon jama’a tsilli tsilli da yake akwai taga mai girma a wajen da ke rufe cikin farin kyakkyawan labule ‘terrace’ din na dauke da doguwar kujerar hutawa (sofa) ta zaman shan iska, da karamin tebirin gilashi a gabanta, wanda koyaushe za ka same shi cike da kayan marmari cikin dankaramin kwando (basket), saboda mamallakin gidan ma’abocin shansu ne, babu dare babu rana. Shi ya sa kullum yake cikin kuzari da koshin lafiya, da (body structure) mai kyan tsari, wanda babu Teba, kuma babu rama a cikinsa.
Dakidaya na baccinsa ne, dayan kuma a da na matarsa ne. A rashinta sai ya maida shi dakin karatu da motsa jikinsa. Ya cika shi da na’urorin motsa jiki, ya maida shi (gymnasium), a lokaci guda kuma dakin bincike cikin na’ura mai kwakwalwa da karatunsa (computer room).
Idar da sallar asubahinsa kenan, tun misalin karfe uku na dare, da yake lokacin asubarsu ke nan, ya yi addu’o’insa da ya saba da azkar masu tsayi da nafilfili ya shafa, wanda babu ranar Allah da zata fito ta fadi da baya yinsu ya nema wa mahaifinsa da matarsa, kuma masoyiyarsa uwar tilondansa rahma da gafara wurin Ubangiji ba.
Daga nan ya miqe ya hau (internet) ya ci gaba da rubutun ‘project’ din sa da yake hadawa, wanda zai ba shi damar karbar kwalin (FWACP) wato ‘Fellow West African Collage Of Physians’ a bangaren sa na (Psychiatry). Wanda wannan shi ne babban burin rayuwarsa. Bayan shi ba shi da sauran buri sai na ya amfani al’umma da wannan kokari da jajircewa na shekaru masu yawa, da kuma rokon Allah ya karawa mahaifiyarsa (Nanna) tsawon rai da lafiyar da za ta ci gaba da kula da su shi da gudan zuciyarsa, rabin rayuwarsa, hasken idanunsa wato dansa (Suhail), ya kuma sa ya cika da kyau da imani kamar matarsa SUHAILA.
Domin dai duk wani burin dan Adam a rayuwa, na shi kam Allah ya cika masa gwargwado, sai dai in bawan ya kasance mai zarmewa ne cikin son duniya (hadamamme ga kyale-kyalen duniya da dogon buri). Aure ba ya cikin lissafin rayuwarsa ta yanzu, Ubangiji ya yi masa baiwa da lafiya, muhalli wadatacce, yana da ilmi mai tsada da wuyar samu, wanda sai daidaiku Allah ke zaba cikin bayinSa Ya yi musu baiwarsa.
A birnin Birmingham gabadaya yana daga cikin likitocin kwakwalwar da ake ji da su. Sannan tabbataccen ma’aikacin asibitin kasa ne (NHS) da ke aiki da ‘Tavistock and Portman’, kuma ‘part time Doctor’ da fitaccen asibitin kudin nan na garin wato ‘Spire-Little Aston Hospital’ da ke Birmingham.
Babban farin cikinsa da Allah ya yo shi musulmi, cikakken Hausa-Fulani. Ya yi masa baiwa da wata irin UWA mai yawan jin qai da kyautatawa, tausasawa,karfafawa da tausayawa a gare shi. Mai yi masa addu’a a kan dukkan al’amuransa, Ya yi masa baiwa da rayuwa da masoyiyar da yake da yaqinin har abada ba zai samu makwafinta ba. Masoyiya ta haqiqa, wato marigayiya SUHAILA. Wadda har abada ta ke koriya sharrr cikin tsokar zuciyarsa, sannan abar tunawa da kewa mai yawa. Ta yadda ya alqawarta wa zuciyarsa ya gama aure a duniya, a dalilin ya rasa suhaila.
Yana jiran ajalinsa ne shi ma ya koma ga Ubangijinsa cikin imani da karbar jarrabawar da ya saukar a gare shi. Ya tadda Suhaila su ci gaba da rayuwar da suka faro, a inda babu mai yanke rayuwa,(mutuwa) balle ta sake raba su.
Sai dai ya amince Allah bai barshi haka nan ba bayan wannan babbar jarrabawar da Ya yi masa (ta dauke Suhaila), bai barshi haka ba sai da Ya ba shi sanyin idaniya daga Suhailar, wato dansu Suhail, da a kullum ya daga ido ya duba wata nutsuwa da kwanciyar hankali ke sauka a zuciyarsa, domin fuskar Suhaila da (dimple) dinta ne a fuskarsa. Idan kuma ya bangale baki yana masa dariya (cleft) din Suhaila ke lotsawa a habarsa. Tsakanin hakoransa hudu biyu na sama, biyu a kasa, wushiryar Suhaila da totsiyar karenta ke bayyana, wannan shi ne abin da ya fi so a rayuwarsa wato dan nan nasa ‘Suhail’ in ka cire mahaifiyarsa Nanna (Aisha).