← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gara ta kwana a toilet da ta kwana tana ganin Turaki a gaban ta, kuma wai a matsayin mijin ta na sunna a karo na biyu.

Tana jin shi yana mata magana a daidai kofar bandakin,
s okey, ni ba bakon zafi ba ne.

Na bar miki dakin ki, ki kwana cikin aminci UmmuKulsumun Turaki.

And dreamt of our twin babies masu zuwa nan da watanni tara
Ya yi murmushin da har ta ji tashin sautin sa, ya sake cewa
Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba?

Ai sai daren mutuwar sa.

Mutumin da ya yi hakurin shekara takwas ai ba zai gaza yin na dare daya ba
Ita dai ba ta ce komai ba.

Ya sake cewa,
Na barki lafiya Princess
Tana jin fitar sa da rufo kofar sa, amma ba ta fito ba sai da ta tabbatar ya fita din.

Tana fitowa ta murza wa dakin makulli.

Kasa tada sallar ta yi, sai ta zauna a bakin gado tana tunanin rayuwar ta mai abun mamaki.

Turaki as her husband for the second time, tare da wasu mabambanta halaye da suka barranta da nasa.

Ba ta da zuciyar da za ta kara yarda da Turaki, kamar yadda ba ta taba shirya wa ranta sake rayuwa da shi ba.

Zai sha mamaki kuwa, idan har yana zaton wannan karon ma zai ci galaba a kan ta, kamar yadda ya ci a baya, idan zaton sa karamar yarinya Kulsumun da, ita ce a cikin gidan sa yanzu.

Sai yanzu ta gane maganganun da Baban ta Malam Hadi ke yi a kan gidan Sarkin Gaya, ashe-ashe nufin sa can za ta sake komawa.

To me ya sa Baffa ya boye mata?

Ba shakka don ya san ba za ta amince ba ne.

Hawaye suka zubo mata, how could she forget his wickedness (ta ya ya za ta manta muguntar sa?) Shi ne yanzu ya zo yana
yar murya don ta tashi daga Kulsumu
yar kauye, mai fitsarin kwance?

Ta koma yadda yake son ganin mace?

Ko ta rasa miji me za ta dawo ta dauka a gidan Turaki?

Gara masa ya maida ita inda ya dauko ta ko ya shirya zama cikin bakin ciki da tashin hankali, ba za ta taba zaman lafiya da shi ba har karshen rayuwar ta.

A wannan daren, duk iya sata irin na barci da kyar ya iya sace UmmuKulsumu, tana kitsawa tana warwarewa, amma ta kasa gano hanyar da za ta bi ta tserar da kanta daga auren Turaki.

Bakin alkalami ya riga ya bushe.

Ta yi kuka, ta yi kuka har ta gode Allah.

A rayuwa Baffa bai taba bakanta mata irin wannan lokacin ba, shin ko sun manta wane ne Turaki ne?

Turakin da ya bula musu kasa a ido, ta koma sunan karamar Bazawara a dalilin sa, har ta yi zaman gidan sa ta kare ba ta taba ganin murmushin sa ba, kalma ta arziki bata taba hada su ba, bai taba daga ido ya kalle ta ba, sabida a baya bai dauke ta mutum ba, yanzu ne ta ke mutum, sabida ba ta fitsarin kwance, kuma ta yi ilmi ta goge?

Zai sha mamaki kuwa, don ba don shi ta dage ta canza rayuwar ta ba.

Ta canza ne don amfanin kan ta.

Tabbas za ta aro rigar rashin mutunci wanda ba halin ta ba ne ta saka a zama da Turaki, sai ya maida ita inda ya dauko ta yana so ko ba ya so.

Da wannan tunanin barci ya samu nasarar sace ta goshin asubahi.

Turaki a nasa dakin bayan ya rage kayan jikin sa zuwa na barci, komawa ya yi falo ya yi waya da Abdul
Ahad, yana bukatar raba farin cikin da yake ciki tare da aminin nasa.

Ya ce,
Aboki, ga ni ga Kulsum a cikin gida na, matsayin matata for the second time, wace irin godiya ya kamata na yi wa Ubangiji?

Abdul
Ahad ya ce,
ka yi sadaka ga mabukata, ka ziyarci marassa lafiya a asibiti, ka yi musu ihsani.

Sannan ka yi damarar rike matar ka tsakani da Allah, don ba dabararmu ce ta sa Ubangiji ya dube mu Ya yaye mana damuwar mu ba.

Rahamarsa ce da Gafarar sa gare mu
Turaki ya gamsu da maganganun Abdul
Ahad, ya yi niyyar bin duk abin da ya ce da zuciya daya.

Nan ya ce,
Amma wani hanzari ba gudu ba, Kulsum matukar fushi ta ke da ni Aboki, don ba ta ma san da ni aka daura mata aure ba.

Fushin da ban san yadda zan yi in rarrashe ta ba
Murmushi Abdul
Ahad ya yi, ya ce,
Turaki kada ka bada maza mana, ai kawai rikidewa za ka yi daga likitan ido ka koma Romeo, ka yi hakuri da duk abin da za ta yi, za ta gaji ta bari ne tunda bakin alkalami ya bushe
Turaki ya kyabe baki, ya ce,
ni fa ba zan yi abin da zai jawo min raini ba Malam, idan ta kawo ni bango dauke ta zan yi mu bar garin, mu tafi inda ba mu da kowa, in yaso ta tsire ni ta huta
Dariya Abdul
Ahad ya yi, ya ce,
Sanda za ka zama Romeo din ai ba gaya min za ka yi ba.

Ina nan isowa jibi insha Allahu, da ni za a yi kilisa
A yau ya san ya yi barci irin wanda tsawon shekaru takwas da doriya rabon sa da yin irin sa.

Duk wani tension ya kau.

Duk wani migraine ya tabbata daga yau babu shi; Kulsum cikin gidan sa, matsayin matar sa ta sunnah!

Babu wani kwanciyar hankali da contentment din da ya fi wannan a gare shi.

Da asubahi ya so ya je ya buga mata kofa, sai kuma ya yi tunanin ya kyale ta, a sanin da ya yi mata sallar asubah ba ta wuce ta ba tare da wani ya tashe ta ba.

Domin lokacin ne ta ke aikin wankin kayan fitsarin ta.

Ta dade da tashi kuwa kamar yadda ya yi hasashe, ta yi wanka, amma babu kayan da za ta canza.

Tana cikin gyaran gado ta ga wata jakar bacco a gefe, da ta bude sai ta tarar da kayan sawa ne na Dr.

Sakeenah, ta santa da kayan a jikin ta, ta gane ajiye mata ta yi don ta yi amfani da su kafin a tattaro kayan ta daga Abuja a kawo mata.

Kaunar Sakeenah da ganin girman ta suka kara cika ranta.

Ta zabi wata shudiyar super holland riga da zani da dankwalin su ta sanya, ta lullube jikin ta da mayafin kayan kamar mai shirin fita unguwa, lotion kawai ta shafa, ko hoda ta ki shafawa kada Turaki ya dauka kwalliya ta yi masa.

Tunanin sa kawai ya janyo mata wani irin bacin rai.

Daidai lokacin da ta ji ana buga kofar ta.

Dole ta je ta bude don rana har ta soma fitowa.

Wa za ta gani?

Batulu!

Wani irin rungume juna suka yi, Batulu na fadin,
Kulsumu na, ashe zan sake ganin ki?

Ta ce,
Batulu kudurar Allah ai ta fi gaban haka
Tare suka wuce zuwa tangamemen falon wanda ya sha tsari da tsadaddun kaya kamar a Turai.

Batulu ta ce,
In na ce wa Yaya Turaki ya kwantar da hankalin sa, idan Kulsumu matar sa ce babu makawa sai ya same ta, sai ya ga kamar na fada masa karya, yau Allah cikin hikimar sa ga Kulsumun mu ta dawo mana cikin yardar Ubangiji
Nan suka fara labarin bayan rabo, Kulsum ta ce, ina yaran ta?

Ta ce suna wajen Ummah.

Suna zaune kamar sa hadiye juna don kauna da aminci, kowacce na labarta wa
yar uwarta yadda rayuwa ta kasance mata bayan rabuwar su, Batulu na ba ta labarin irin bilinbituwar da suka sha ita da Turaki wajen neman komen auren ta.

A cikin ran ta ta yi mamaki sosai, mamaki ba dan kadan ba, in ta ce mamaki tana nufin mamaki, sai dai wannan bai ishe ta ta yarda yanzu Turaki na matukar son ta ba ne, yana dai da hujjar sa, watakila don ya samu cikar wani burin nasa ne.

Sai dai ba ta ce da Batulu komai ba, ganin yadda ta ke jaddada mata kaunar Yayan ta gare ta.

To da ma ita soyayyar kan shiga farat daya ne bayan kiyayyah?

Don dai ita a gabadaya sanin da ta yi wa Turaki kiyayya yake mata ba soyayya ba, don haka ba za ta yarda da wannan campaign din na Batulu ba, a dai yi sha
ani kawai wai kaza ta so tsegumi.

Gyaran muryar Turaki ya sa Batulu ta nutsu, ya shigo dakin cikin shirin fita, kamshin sassanyan turaren sa one man show ya mamaye su.

Ya dubi Batulu ya ce,
Ke kuma haka ake zuwa gidan mutane da sassafe?

Mutanen ma amare sabon aure?

Dariya ta yi, ta ce,
wadannan ai tsofaffin amare ne.

Yaya Turaki na kasa hakurin yamma ta yi ban ga Kulsumu ba.

Ka san tun tafiyar ta ba mu sake haduwa ba
I can relate
.

In ji Turaki.

Ya maida duban sa ga Kulsum,
Ummukulsum zan fita, ko kina da sako wajen su Baffa?

Dauke kanta ta yi gefe ba ta amsa ba.

Sai da Turaki ya yi da na sanin kula ta, ga shi ta dizga shi a gaban kanwar sa da ke matukar ganin girman sa.

Yana fita Batulu ta ce,
Wai fushi ki ke da Yaya Turaki Kulsumu?

Ki yi wa Allah ki yi wa Yaya Turaki adalci mana, ya sha wahala a kan ki, ya sha matukar wuya kafin ya same ki.

Ya yi nadama!

Murmushi kawai ta yi, ai Yayan ta ne da ta ke so, uwar su daya uban su daya, ba abin da ba za ta ce ba don kafa gwamnatin sa.

Ita kuma ta sha wahalar soyayya idan shi wahalar neman ta ya sha, shekara da shekaru tana dawainiya da soyayyar sa, wadda ba ta ga ranar da ta yi mata ba.

Batulu ta bar zancen don ta san ba hurumin ta ba ne.

Ta ce su je su zagaya ta ga gidan nata sosai.
Chapter 9 · 0% Book details