← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da magriba ne ya je ya yi sallah ya dawo, ya ce ta shirya su je ta gaida Umma da sauran mutanen gida.

Sosai ta yi shiga ta alfarma sai kamshi suke daga ita har shi.

Tsakanin gidan su da masarautar Gaya ba tafiya ce mai yawa ba, a kafa ma za a iya zuwa.

Amma mota suka hau, lokacin da suka isa Umma fada ta hau yi kan don me zai fiddo Kulsum ko wata guda ba ta rufa ba, in gaisuwa ce ai tana aiko mata kullum.

Shi dai hakuri yake ba ta, bai gaya mata ba ya so ya fito ya baro Kulsum cikin damuwa ba ne.

Umma ta tambaye ta,
In ce ko babu matsala Kulsum?

Kanta a kasa ta ce,
Babu Umma, muna godiya da dukkan dawainiyar ku.

Allah ya kara girma, Allah ya kara yawan rai
Umma ta ce,
Ko kina bukatar karin ma
aikata?

An ce gidan naku da girma sosai
Kulsum ta ce,
Umma har sun yi yawa, Baba Laraba akwai zafin nama kamar ba tsohuwa ba".

Umma ta yi murmushi, ta ce,
Ga iya girki kuma.

Sannan tana son ki sosai
Kulsum ta ce,
Yaya labarin mutanen kaduna?

Tun bayan biki babu labarin su
To ke din ce ai babu waya, Turaki ya ya batun wayar Kulsum ne?

Shi dai yana gefe kan shi a kan wayarsa ba sauraron su yake ba, sai da Umma ta kira sunan shi ya dago, ta sake maimaitawa, ya ce,
Ina sane, ban samu shiga Kano ba ne sai wajen jibi
Duka dakin matan gidan sai da Kulsum ta je ta gaishe su, inda ta tarar Fulani wato kakar su Turaki tana kwance babu lafiya, likita ne ma a kanta ya daura mata ruwa.

Tsohuwar tana jin jikin ta, amma albarka ta ke sa wa Kulsumu, tana rokon ta ta rike Turaki da amana, domin shi dan albarka ne, wanda duk gidan ba wanda ta ke so irin sa.

Ba su koma gida ba sai wajen sha dayan dare.

Kulsum ta sa a ranta sai dai Turaki ya yi fushi da ita, amma ba za ta sake kwana daki daya da shi ba, hakan cutarwa ne a gare shi, duk son da yake ikirarin yana yi mata in aka ci gaba da tafiya a haka tana sharkaba masa fitsari a gado, watarana na zuwa da za ya tsane ta, in ma bai hada da duka ba.

Don haka ta lallaba ta shige dakin ta ta murza key, ta jingina da kofar tana sakin ajiyar zuciyar tausayin kan ta.

Bugun duniya Turaki ya yi, kiran duniya da lallashin duniya amma Kulsum ta ki budewa, don bacin rai kasa kwana a daki ya yi shikadai ya dawo falo ya sa filo a kasa ya kwanta.

Washegari sabida farin cikin ba ta yi fitsari ba don ta bi system din nan na non-pharmacological treatment, da kanta ta hada wa Turaki abin karin kumallo.

Ta koma dakin ta ta yi wanka ta zuba kwalliya mai sanyaya zuciyar maigida.

Ta feshe jikin ta da turaren fahrenheit ta doshi dakin Turaki.

Da sallama ta shiga, yana kwance daga shi sai kayan barcin jikin sa yayi filo da hannayen sa yana fuskantar ceiling.

Bai amsa sallamar ta a fili ba, amma ya amsa a zuciyar sa.

Bai kalle ta ba, balle kwalliyar da aka yi domin shi.

Tana iya karanto kwantaccen bacin rai a kan kyakkyawar fuskar sa.

Ta karasa a hankali ta zauna a daidai saitin kansa.

Barka da safiya Prince
Shiru ya yi mata, ta rasa abin da yake mata dadi.

Na shirya abinci, don Allah ka fito ka ci
A lokacin ne ya juyo gaba daya ya fuskance ta.

Kulsum, yaushe raini ya gifta a tsakanin mu, da har za ki kulle min kofa?

Ina miki magana ki ka yi banza da ni kamar ba ki san ina yi ba?"
Hawaye suka zubo daga idon Kulsum, ta ce, "Ban yi don raini ba Prince, na yi ne don gudun cutar da kai.

Yau da gobe duk hakurin ka da kaunar ka gare ni, wallahi sai ka tsane ni Prince
Abin da ki ka yi min shi ne babbar cutarwa a gare ni.

Kin sani ba ni da wata matar bayan ke.

Ni idan zan same ki a kullum ba ni da matsala da fitsarin ki.

Don dai barin garin za mu yi ne, amma tuni na yi mana odar water mattress har guda biyu daga Amazon za su kai min gida na na Reading.

In wadannan sun mutu babu damuwa
Kulsum couldn
t help it ban da ta fada jikin sa ta fashe da kuka, wani irin kuka mai kara soyayyar da ta ke yi wa Turaki.

Ta ce,
Na gode Prince, don Allah ka yafe min bacin ran da na sa ka jiya
Ya ce yana mai tuje daurin da aka bata lokaci ana kalmasawa.

Ai hakuri daya ne, ki biya ni bashina na jiyan".

Daga haka ya canza akalar hirar zuwa irin wadda ya fi so su yi.

Tun daga ranar Kulsum ba ta kara rufe wa Turaki kofa ba, ta yarda shi din mai son ta ne, mai yawan kaunar ta da tausayin ta ne.

Sai dai kuma ta daina barci, kullum cikin non-pharmacological exercise, wato ta daina shan abu mai ruwa-ruwa da shi ruwan kansa daga karfe shidda na yamma, sannan kafin ta kwanta sai ta tabbatar ta yi fitsari, bayan saduwarta da mijin ta abu na farko da ta ke yi shi ne fitsari, sannan ta saita alarm ta aje a saitin kanta tana tashi sau biyu cikin dare at interval ta je ta yi, daga lokacin da suka yi sallar asubah sai ta koma dakin ta, a can ta ke ramuwar barcin ta ta yi fitsarin ta son ranta, sai dai ta yi wata dabara, spreedsheet na kan dining table wanda leda ce ta dauke ta shimfida a saman katifar ta, ta lulluba zanin gado mara kauri a kai.

Turaki ya kara sayo su da yawa ya jibge mata, tana tashi za ta yaye su har ledar ta wanke ta shanya a bandakinta, ba ta taba fitowa waje ta yi shanya ba.

Turaki ba karamin tausaya mata yake ba, sabida irin yadda ta ke wahala wajen tsaftace kan ta da muhallin ta.

Aikin da da hali da ba zai barta ta yi shi da kanta ba, tunda suna da wadatar masu aiki, shi ya sa sau tari yake zuwa ya wanke zannuwan gadon da kansa, idan ta jika su a omo ta shiga wata sabgar.

Ta yi ta yi ya bari ya ki, cewa yake.

We are together in this difficulty (muna tare a cikin wannan wahalar)
A gefe kuma yana ta shirye-shiryen tafiyar su U.K.

Ya cika alkawari ya kawo mata dalleliyar waya, sai damuwar ta ta ragu.

Kullum in ba ya nan tana tare da
yan uwan ta a waya, sannan duk inda ya je Allah-Allah yake ya dawo da wuri don kada kadaici ya jefa ta a damuwa.

Ba ya son abin da ta ke yawan fadi na cewa, ta tsani kanta.

Ji yake me ya sa ma tun farko bai zama kidney and bladder specialist ko Nephrologist ba?

Da tuni ya bai wa Kulsum duk treatment din da ya kamata ba wanda ya ji ba wanda ya gani..

Ganin kwanakin da Dr.

Ibrahim ya deba musu yake kamar shekaru uku.

Ya je Gombe ya kwana biyu don gudanar da wani private aiki na Sarkin Gombe, wanda cikin ikon Allah aka yi nasara idanun Sarkin suka washe.

A lokacin da ya samu lafiya ne ya kira Turaki, wai ya zo ga
yar shi Siyama ya ba shi kyautar ta ko a mata ta hudu ne, bayan iyayen kudin da ya tura masa wadanda sun ninninka kudin da suka yi za'a biya shi.

Turaki ya yi dariya, ya ce da Maimartaba Sarkin Gombe, ya gode, amma ba zai karba ba, sabida ko wata bai yi da yin aure ba.

Wannan labari Turaki ya zo yana bai wa Kulsum, bayan dawowar sa daga Gombe.

Kulsum ta lumshe idanun ta ta ce,
Ai da ka karba Prince, ka ga ni babu tabbas din zan warke gabadaya, ko ba zan warke ba.

A baya ne nake tsoron ka yi aure, amma yanzu na yarda da kai dari bisa dari, na amince babu macen da za ta sa ka juya min baya.

Roko na gare ka shi ne, kada ka taba bari matar ka ta san ina da lalurar urinary incontinence (bed -wetting)
Turaki ya harare ta son ran sa, ya ce,
Wato Kulsum ba kya kishi na ko?

Ta ce,
Kishi ba zai sa in kware ka ba, soyayyar da nake maka ita ce ta sanya nake son ka samu cikakken farin ciki kamar kowanne namiji.

Ina farin ciki da jin dadi ga auren mai jika gado?

Ai sai dai maneji, manejin ma sai irin miji na (Turaki) masu babbar zuciya ta tausayi da jin kai
Fushi sosai Turaki ya yi, wai ta gasa magana kuma ba ta kishin sa.

Wuni guda ya ki dawowa gidan, da ya dawo din kuma ya ki yi mata magana.

Ya zauna a falo yana kallon football.

Kulsum ta fito cikin kasaitacciyar kwalliya, ta zagaya ta bayan kujerar da yake zaune ta zagaya hannayen ta a wuyan sa suka sauka a kirjin sa.

Ta sanya fuskar ta a masangalin wuyansa ta sumbace shi son ranta, sumba sosai, mai tsayi da zurfi.

Ina bada hakuri my Prince, ka je ka karata da mai fitsarin kwancen ka, ba zan kara cewa ka yi aure ba
Duk halin fushin da yake ciki sai da ta ba shi dariya.

Ya mika hannu ya zagayo da ita gaban shi ya zaunar ta bisa laps din shi.

Bakin ta da ya sha wet-lips ya hau tsotsewa sannan ya dalle mata shi da karfi, sai da ta yi
yar kara.

Matar tawa ki ke cewa mai fitsarin kwance?

Don zafi sai da hawaye ya tsattsafo mata.

Ka yi hakuri, na bi Allah na bi ka
Ya rungume ta sosai yana jin bugun zuciyar ta a kirjin sa.

Sun dade a haka yana gaya mata babban abin da ba ya so shi ne ta ce ya yi aure, sabida lalurar ta.
Chapter 15 · 0% Book details