Sashe 8
Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan fitar Sakeenah ta dade kafin ta fara ci.
Kasancewar da yunwa ta kwana, sai naman ya yi mata dadi ta bude ciki ta ci sosai, ta hada mata kasusuwan kamar yadda ta umarce ta.
Ta kuma hadiye magungunan da ba ta san na mene ne ba.
Karfe biyar na yamma
yan daukar amarya suka zo, Dr.
Sakeenah ta zabo mata wani sabon lace din ta don Kulsumu ba ta zo da kaya ba, sannan ba wasu kayan aure da aka kawo mata, Baffa ya sa an maida sauran ya ce, sadaki kawai zai karba kamar wancan karon.
Wadanda suka zo daukan amaryar dattijai ne su uku, cikin wata kosasshiyar mota ta Maimartaba.
Daya kanwarsa ce Goggo Hanna, daya yayar Umma ce da ta zo daga Gombe, dayar kuwa matar Galadiman Gaya ce Hajiya Rabi.
A karo na biyu yau ma sai da Lami ta goya Kulsumu sannan suka iya tafiya da ita.
Ko nasiha Goggo ba ta samu ta yi mata ba sabida tsananin tausayin da Kulsumun ta ba ta, ga ta cikin matsanancin kuka kamar na fitar rai.
Abubuwa da yawa ne suka damu Kulsumu, zuwa yanzu ba ta damu da sai ta san ko wane ne mijin da iyayen ta suka zaba mata ba, domin ta sa a ranta wannan auren za ta je bautar Allah ne kawai albarkacin ba za ta iya tozarta Baffa ba.
Ba ruwan ta da ko waye mijin.
Tausayin Nasara da
yanta shi ne babban abin da ya fi damun ta.
Ta yi nadamar kin Taufeeq da ta yi, domin an ce ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, amma ba ta duba hakan ba ta yi abin da zuciyar ta ta fi kwanciya da shi, ga shi sakamakon hakan ya jawo mata auren wanda ba ta sani ba, ba ta san shi kuma mene ne nashi nakasun ba.
Kugin da motar ta yi na karshe a kofar gidan Dr.
Turaki ne, kyakkyawan gidan da duk garin Gaya babu mai kyau da tsarin sa.
Asali Maimartaba ya gina gidan ne don hutawar sa ba da sunan Turaki ba, amma da ya ji kowa Turaki zai aura, ya tabbatar Turaki da gaske yake ya karbi zabin da suka yi masa da hannu bibbiyu, kuma ya yi damarar zaman aure ne yanzu da Kulsum, sannan kaunar sa ga yarinya UmmuKulsum wadda ba ya wa Turaki sha
awar kowacce mace sai ita, sabida sun zauna da ita, sun san halayen ta.
Sannan sun amince da dattakon iyayen ta, da soyayyar da ta ke yi wa Turaki.
Da wannan zazzafan darasin da iyayenta suka koyar da shi, su suka hadu suka faranta ransa har ya yi wa Turaki kyautar wannan dankareren gida.
Abin da ya janyo kishi karara daga sauran matan sa, amma ba su da ta cewa tunda ba su da Da namijin da zai kara da Turaki, duk
yan su mata ne a gidan aure.
Su Batulu ai tun safe ana gidan amarya, da ita aka yi jere/kafi da komai.
Ba ta damu da ta ga Kulsumu ba tana cikin sabga sosai.
Yaya Hadiza ce ta taro su lokacin da suka iso, ta yi musu jagora zuwa dakin Kulsumun, wadda ke rufe ruf cikin yalwataccen mayafin da Dr.
Sakeenah ta lullube ta da shi.
Hajiya Nasara ce rike da ita, a kofar dakin ta gaya mata ta shiga da kafar dama, sannan da addu
ar da za ta karanta.
Batulu ba ta gidan, Umma ta kira ta don ta je su hada kayan sallamar masu kafi da kawo amarya.
Daga Yaya Hadiza sai Aunty Ramla da sauran sisters din Turaki da suke uba daya.
Ko da wasa Kulsumu ba ta bude lullubin ta ba wai don ta ga inda aka kawo ta.
Kukanta ta ke bilhakki duk ta jika mayafin ta da hawaye.
Lokacin da ta ji su Hajiya Nasara na haramar tafiya sai ta rirrike ta, cikin kuka ta ce.
Mum ki yafe mini, kin yi min komai a rayuwa, amma ni na ki Yaya Taufeeq a kan ajizancin da babu wanda ya wuce shi.
Mum daga baya na so in gyara kuskurena baffa bai ba ni dama ba, wallahi Mum da wannan damuwar zan rayu har karshen rayuwa ta
.
Ta fada jikin ta tana kuka mai nuna nadamarta.
Hajiya Nasara ta riko ta sosai a jikin ta, ta ce,
Kulsum kada in kara jin wannan maganar a bakin ki, ke
yata ce kamar yadda Taufeeq yake dana.
Ba Taufeeq ne ya hada mu ba zumuncin Allah ne wanda Ubangiji ya yi mana umarni dole mu yi shi.
Da kin auri da na da ba ki aure shi ba, matsayin ki na
ya a gare ni ba zai taba canzawa ba.
Ba ki da wadda ta fi ni ke da Goggo, kamar yadda ba ni wadanda suka fi ku.
Ki sa a ranki Allah ne bai kaddara aure tsakaninki da Yayanki Taufeeq ba, ki taya ni addu
a Allah ya yaye masa halin da ya jefa kansa ya samu mata nutsattsiya kamar ki ya aura
Kulsum ta kara rungume Hajiya Nasara tana sakin wani sabon kukan, ta ce,
Na gode, na gode Mum
Ta ce,
Ba kin gode ba, be happy with your marriage, ki yi wa mijin ki biyayyah, shi din mai son ki ne.
Ina da tabbacin wannan karon sai kin fi kowa farin ciki da zaman aure.
Daina kukan nan in mun tafi ki dauro alwalla ki yi nafila raka
a hudu ki roki Ubangiji Ya dorar da farin ciki a rayuwar auren ki
Tana ji tana gani duk suka shige motoci suka tafi babu wanda ya rage a gidan.
Hatta masu aiki Umma ta ce sai bayan kwana bakwai za a kai mata.
Ta yi kukanta ma
ishi, a karshe ta yanke bin shawarar Hajiya Nasara, wato ta yi sallahr nafila.
Mikewa ta yi ta warware mayafin da ke jikinta ta ajiye, idanun ta suka hango mata kyakkyawan dakin nata, wanda ya ji rantsattsun furnitures tafiyayyu tun daga China.
Ta san wannan aikin Hajiya Nasara ne, ta yi mata tanadin rayuwa da danta, amma a karshe gidan wani suka shigo.
Ta girgiza kai a hankali, ta doshi kofar da ta tabbatar toilet ne.
Tana murda kofar toilet don fitowa, Turaki na turo kofar dakin don shigowa.
Sanye yake da wani irin tattausan yadin filtex fari sol, dinkin tazarce.
Kansa babu hula, sumar nan baka wuluk da ya tara a U.K ta kwanta luf a kansa, sai sheki ta ke yi, hade da lallausar sajen fuskar sa wanda a lokacin samartakar sa bashi da shi.
A hankali ta daga idanu ta dube shi.
It was a sudden shock irin wanda zai iya haifar da bugun zuciya a l
okaci guda.
Fuskar ta kuma ba ta boye halin shock na ba-zata da ta shiga ba, sai ta tsaya standstill rike da hannun kofa.
Ta rasa mafarki ta ke yi ko idonta biyu?
Ya fi kama da mafarki, wanda kusan kullum ba ta rabo da yin irin sa,.
Seeing Turaki a matsayin mijin ta!!!
Wani tattausan murmushi ya yi, wanda ya nuna fahimtar sa ga halin firgicin da ta samu kan ta, ya kuma gane ba ta san kan shi Baffa ya maida auren ba.
Wannan abu ya kara yi masa dadi ba kadan ba.
Takowa ya yi a hankali zuwa gaban ta.
Ya mika hannu da nufin ya kamo hannunta.
Da wani mugun zafin nama ta ja da baya, sannan ta daddage ta fasa wani firgitaccen kuka tare da durkushewa a kasa tana ta gunza shi kamar za ta fasa dakin.
Wannan abu ya matukar bai wa Turaki dariya, waje ya samu gefen gadon ta ya zauna, ya zuba mata ido, daga baya sai ya kishingide ya dauko wayar shi ya shiga danne-danne, ba da sanin ta ba vedio yake yi mata.
Cikin gunjin kuka ta ke fadin,
Na shiga uku na lalace ni Kulsum, abin da Baffa ya yi min ke nan???
Wannan karon dariyar Turaki ta kasa boyuwa.
Ya ce,
Ummukulsumun Turaki, this is the best decision ever, ki gode wa Baffa saboda ya taimake ki.
Ya dawo da ke inda kike so ake son ki.
Ina amfanin badi ba rai?
Ina amfanin ki je gidan Taufeeq alhalin kina da mijin ki a gefe?
To ki je ki kai masa me?
Bayan Turaki ya kwashe komai tun Kulsum na kwailar ta?
Ai da muguwar rawa gwanda kin tashi
.
Ya karasa da wani mischievous smile (murmushin keta) a siririyar fatar bakin sa.
Kulsum ta yi sak!
Daga kukan fitar ran da ta ke yi tana nazarin kalaman sa, kafin wani dan lokaci ta gane me yake nufi.
Wata zuciyar na cewa ta rufe shi da duka ko ta ji dadi, wata na cewa ta fice ta bar masa dakin.
Ta je ta yi jinyar abin da ya same ta ita kadai.
Kamar Turaki ya san tunanin da ta ke yi, ya mike kamar zai fita, kawai sai ya murza wa dakin key, ya tako ya iso har gaban ta ya durkusa.
For the first time a rayuwar sa da ya samu kansa durkushe gaban mace, sannan da niyyar lallashin ta.
Kulsumu ta yi wuf za ta mike, ya riko ta da kyakkyawan rikon da ba za ta iya kubucewa ba.
Sannan a hankali ya mike shi ma suka fuskanci juna, kirjin ta na heaving faster and faster tamkar mai ciwon asthma, yayin da zuciyar Turaki ke wani irin circulating tana haifar masa da abubuwan da bai taba ji a rayuwar sa ba akan diya mace.
Kulsum ba ta gama tantance halin da ta ke ciki ba ta ji Turaki ya rungume ta da wata irin kyakkyawar runguma (tight hug) yadda jikin sa ya ratsa ko'ina na jikin ta.
Bugun zuciyar ta ya karu, kamar yadda nasa ke yi, suka koma bugawa a tare, kamar zuciyar su za ta ballo allon kirazan su ta fito.
Kokari yake ya lalubo bakin ta, amma Kulsum ta ki ba shi damar hakan.
Sai faman cusa kai yake a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta yana kissing iya abinda zai iya samu.
Zamewa ta yi ta kasan hannayen sa ta koma toilet da gudu ta banko kofa ta murza key.
Ta koma ta jingina da kofar bandakin tana sauke ajiyar zuciya.