Sashe 2
Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saboda ita ne yake jin zai iya kare rayuwar sa single idan har bai same ta ba.
Ashe ita tuni ta manta shi, she have move on tare da wanin sa.
A zahiri bai kamata ya ga laifin ta ba, amma sai ya ji gabadaya duniyar na juya masa.
Idan har da gaske matar auren ce, ya san hatta wannan kebewar da ya yi da ita a cikin motar sa haramun ne, sai dai ji yake in wannan shi ne haramun din da zai halaka shi
ba zai bari ta sake kubuce masa ba.
Look Ummukulsum, duka cikin mu nan ba yaro karami, ki yi ta pretending din ki ba zan hana ki ba, amma in kin ga na barki kin bar gidan nan, to kin fito mun shiga ciki ne, mun zauna mun yi magana, na fahimce ki kin fahimce ni".
Kulsumu cikin shesshekar kuka, ta ce,
Ta ya ya zan yarda in bi ka ba ni da masaniyar ko za ka cutar da ni?
Ta ya ya ka ke tunanin zan yarda in shiga inda daga ni sai kai babu muharrami a tsakanin mu, alhalin na kasance matar aure?
Turaki ya lumshe idon sa na sakan biyu ba tare da ya bude ba, kalmar auren nan tata da take ambata ta kasa yi masa dadi, ta kasa zauna masa a rai, haka ta kasa daina gasa zuciyar sa, sannan ya kasa yarda da ita, ya ce,
ki sa a ranki cewa, kina cikin amana ta, ke da auren naki.
Amanar da idan na ci ta sai Allah ya saka miki.
Ki yarda komai lalacewar duniya har gobe akwai sauran masu amana da kokarin cika alkawari
Kulsumu ta ce,
babu ruwana da amanar ka, ko me za ka gaya min ka gaya min yanzu ka sallame ni in tafi, ni dai na san ban san ka ba, ban taba ganin ka ba ko a hanya.
Kawai ka ga matar mutane a titi ka sako ta a mota ta karfi ka dauko ta, wannan ai cin mutuncin aure da keta haddin dan Adam ne
Ba ta rufe baki ba Turaki ya bude motar ya fito, cikin zafin nama ya zagayo ya bude tata kofar, kama duka hannayen ta yayi ya dunkule a cikin nasa.
Sannan ya janyo ta ta karfi daga motar.
Ni ma ban ce ki ce kin san ni ba, mu je a ba ki san nin ba, ni ma ai ban sanki ba Kulsum, amma dole mu yi magana ni da ke
A haka suka shiga falon gidan, falo ne tsararre english parlour, bata ankara ba ta ga ya sa mukulli ya rufe kofar ya jefa mukullin cikin aljihun trouser din sa.
A tsaye Kulsumu ta tsaya ta ki zama, Turaki ya tako har gaban ta ya tsaya hannayen sa duka biyu zube cikin aljihu kamar yadda yake a al'adar sa.
Ya yi kokarin kallon tsakiyar idanun ta ya sakar mata signal.
Ta dauke kai, amma hatta hantar cikin ta kadawa ta ke yi.
Yana da wani irin effect (tasiri) a kan ta tun zamanin kuruciyar ta.
Ta yadda idan ya kasance a gaban ta, ko ya gifta ta gaban ta hatta hantar cikin ta rawa take yi.
Yau da ya kasance a gaban ta cikin wani sabon yanayi da bata taba tsammata daga gare shi ba, babu inda ba ya rawrawa a jikin ta, including tsokar zuciyar ta.
"Ummukulsum yaya rayuwa?
Yaya bayan saduwa?
What is special a bayan rabuwar mu?"
Bata bashi amsa ba, illa sunkuyar da kan ta da ta yi.
Kamshin one man show ya cika hancin ta.
Turaki ya kara takowa zuwa gaban ta, space din dake tsakanin su bai fi taku biyu ba.
Ya ce.
"Aka ce ba kya kasar?
Aka yi ta wahalar da ni?
Ashe kina cikin kasar nan Kulsumu?
Kin samu rayuwa yadda kike son ta kin manta da ni ko, ni ina can ina ta wahalar neman ki lungu da sako, , Kulsum tell me about you ko dan yaya ne.
I'm extremely intrigued!
Me ya kawo ki Lagos?"
Wannan karon ne ta dago kai ta dube shi cikin ido.
Kai tsaye ta gatsine fuska ta ce "AURE!
Aure ne ya kawo ni, ba zan gaji da gaya maka cewa ni matar aure ba ce.
Ka mayar da ni inda ka dauko ni, tun kafin miji na yayi karar ka".
Zuba mata ido ya yi kamar ya hadiye ta.
Hannayen ta duka biyu Turaki ya kama kafin ayi haka ya rungume ta da wata irin azama, wata irin kyakkyawar runguma wadda ta hade bugun zuciyar su wuri guda, yana sauke numfashi da sauri, yana barin dukkan excitement din zuciyar sa ya na fita ta cikin numfashin sa.
"Ko waye ya aure ki yayi aure kan aure UmmuKulsumu, ni da baki na ban taba sakin ki ba..... kuma har abada bazan yi ba!
Kuma na rantse sai kin dawo gidan ki da yardar Ubangijin sammai da kassai.
I don't mind your pretendings.... ki cigaba da yi, shekaru takwas da nayi ina dakon wahalar soyayya baza su tashi a banza ba..... this is a promise (wannan alkawari ne)".
Kokari take ta zame daga jikin Turaki amma ya ki bata damar hakan.
Kawai sai ta saka masa wani gigitaccen kuka da yasa dolensa ya sake ta, amma bai saki hannun ta ba, sunkuyawa yayi ya sumbaci goshin ta, karan hancin ta da saman bakin ta, abinda ya kara gigita Kulsumu, ta fizge daga rikon sa da karfi ta ja da baya tana hararar sa, tamkar idanun sa fado, murmushi ya yi, ya bude kofar falon suka fita.
Bai sake ce mata komai ba.
Shi da kan sa ya bude mata kofar motar ta shiga, shima ya zaga mazaunin sa ya zauna, sai da ya kara bata lokaci yana kallon ta da murmushin da bata taba ganin sa da shi ba.
Gabadaya ta canza masa, ta koma masa sabuwar Kulsumu, ba 'yar ficikar yarinyar da ya aura a kauye ya gudu ya bar ta ba, tana ta sharar hawayen dake gudu a fuskar ta da gefen mayafin ta.
Alamu ne dake nuna zuciyar ta na tono old memeories masu daci a kan sa da ta dade da binnewa lokaci mai tsaho.
Ya kunna motar ya taka totur din ta, reverse ya yi ya fita daga ma
adanar motocin ya doshi get cike da kuzari.
Maigadi ya bude musu kofa ya hau bisa kwalta yana jan motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, sabida rashin gudun ta.
Wace unguwa zan kai ki Ma
Ka kai ni bus stop zan samu taxi zuwa gida
Wannan ne kuma ba ki isa ba, sai na damka ki hannun solobiyon mijin ki, kamar yadda na yi masa alkawari
Wayar sa ya dauko ya kira lamba ya sa a kunnen sa, tare da saka wayar a handsfree, tarrr ta ji muryar Taufeeq yana fadin,
Doctor kun gan ta?
Ga mu nan duk hankali a tashe
Turaki ya ce,
security sun ganta, muna kan hanya yanzu haka.
Fada min address din naku
Tana ji Taufeeq na fadin lambar gidan Aunty Sakeenah da sunan unguwar Victoria Island.
A ranta ta ce,
Shi ke nan tawa ta kare!".
Amma a fili ban da kukan bakin cikin Turaki, ba abin da ta ke da rinannun idanun ta.
Suna sanyo motar cikin get din gidan Aunty Sakeenah gabadaya jama'ar gidan suka nufo su har Engnr.
Farouq.
Shi ya bude side din da Kulsumu ke zaune, yayin da Taufeeq ya bude wa Turaki.
Tana fitowa Nasmah da Aunty Sakeenah suka yi kanta suna kiran sunanta don tabbatar da lafiyar ta.
Ba ta tsaya ba, wuce su ta yi dukkan su ta yi cikin gida da gudu, Aunty Sakeenah ta bi bayanta hankali a tashe.
Taufeeq na bude masa kofar ya fito, inda Taufeeq din ya ba shi hannu, sannan suka yi musabaha, Taufeeq na ta yi masa godiya, ya ce,
Amma anya Doctor do you think she is okey?
Murmushi Turaki ya yi, wanda ya fi kama da na rainin hankali, ya ce,
Lafiyar ta kalau, na fi kyautata zaton akwai abinda ta gani ne wanda ya hargitsa ta.
Amma tunda kai mijin ta ne ai za ta gaya maka
Da haka suka yi sallama, Engnr.
Farouq ma na ta yi masa godiya.
Gabadaya suka rufu zuwa cikin gidan, Mujaheed ya ja Nasmah gefe suna magana.
Tsayawa suka yi bakidaya a kanta, kowa da tambayar da yake jefo mata.
Kulsumu lafiyar ki kalau?
Sakeenah ta fada.
Ya ya za ki yi min haka Kulsumu?
In kai ki asibiti mu shiga ofishin likita, kawai sai in juyo in neme ki in rasa?
Kin daga min hankali yadda ba kya zato, kadan ya rage jini na ya hau, to ina ki ka shiga cikin asibitin da muka neme ki muka rasa?
In ji Taufeeq.
Ku yi mata a hankali, ba kwa ganin kuka ta ke ne?
Duk mu kyale ta zuwa ta samu nutsuwa, please, na tabbata ko mene ne za ta gaya muku
.
Cewar Engnr.
Farouq.
Da wannan duk suka watse suka bar ta da Taufeeq, ya zauna kusa da ita, ya kira sunan ta a tausashe,
Kulsum
Ba ta amsa ba, kamar yadda ba ta dago ta kalle shi ba.
Ya dora hannun sa bisa nata, ai da mugun sauri ta janye hannun ta.
Abubuwan sun mata yawa, har suna son fin karfin kwakwalwar ta.
Wai me ke damunki ne?
Are you okey?
Maimakon ta ba shi amsa, sai ta mike ta nufi toilet, ta shige tare da rufe kofar da mukulli, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Ya dade a zaune inda ta bar shi cikin matsananciyar damuwar da ya kasa gano ta inda zai bullo mata.
Ko dai Kulsum ta yi gamo da aljannu ne?
Wani bangare na zuciyar sa ya tambaya, a karshe ya ga shawarar Engnr. ita ce abar bi, wato su ba ta lokaci ko zuwa gobe ne.
Yana so ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, amma bai san me zai ce mata ba, tunda bai san abin da ke damun Kulsum din ba.