Sashe 20
Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kulsum ta zauna ta yi tunanin ya kamata ta fito duniya ta yi 'creating awareness' ga mata 'yan uwan ta masu fama da lalurar fitsarin kwance, domin da yawan wadannan mata, wadanda mostly suna gidajen aure, ko gaban iyayen su sabida zaman aure ya gagare su, a kan su fito su nemi 'medical help' a kan lalurar 'ENURESIS'.
Yanzu zamani ya zo da sauyi na ci gaba da babu irin lalurar da ba a magancewa a asibiti, maimakon su zauna cikin bakin cikin rayuwa.
Ta kuma yi kira ga maza kan su taimaka su kuma tausaya wa matan su masu lalurar fitsarin kwance.
Nuna kyama da wulakanci a gare su ko rabuwa da su babban kalubale ne ga rayuwar su.
Hakan zai jefa rayuwarsu cikin 'risk' na kamuwa da depression, self-hatred da inferiority complex, wani lokacin har ya jawo tunanin kashe kai, wato (suicidal thought) ga masu raunin imani.
Ta tattauna da mijin ta uban 'ya'yan ta Dr.
Abubakar Turaki kan kudirin ta.
Shi kuma ya ba ta goyon baya dari bisa dari.
Ta soma gabatar da makalar a media (talabijin da radiyo) a manyan tasoshi da taimakon Turaki.
Lakcoci ne ta ke gabatarwa masu taken 'Enuresis in Adults; A way out in the medical profession'(fitsarin kwance ga manya; mafitar sa a fannin kiwon lafiya).
A wata makalar kuma ta ce 'Psychological Trauma of Noctural Enuresis; ta kawo bayanin yadda mata da yawa ke fama da shi a gidan aure.
Yadda maza ke 'treating' dinsu da kyama, hantara, wulakanci da raini, ta yi kira ga masu fama da wannan lalura kan cewa lokaci ya yi da ya kamata su san cewa fitsarin kwance ba shi ne karshen rayuwar su ba.
Su mike su nemi magani, don tsira da martabar su a gidan aure.
Tun daga lokacin da aka fara sakin lakcocin Kulsum a 'social media' ta fara karbar kira daga mata daban-daban inda suke tabbatar mata halin da suke ciki kenan, da yanayin zaman su da mazajen su.
Kulsum in ta ji wani abun, ta tuno Turaki da nasa kalar 'treatment' din a gare ta, sai kuka ya kwace mata.
Ta kara godewa Ubangijin ta,
ta amince Turaki daya ne cikin dubu, kuma Ubangiji ya so ta da rahma ne da ya nufe ta da dawowa hannun sa.
*****
Baffa ne ba ya jin dadi, ta yi masa girki na musamman ta zuba yaran a mota suka tafi don su duba shi.
Goggo da Baffa wadanda tsufa ya dada kama su, amma shar suke cike da koshin lafiya sabida kulawar da suke samu daga Kulsumu da Turaki, suka shiga ina suka saka-ina-suka-aje da tattaba kunnensu masu kiriniya.
Iftihal ta yi tsalle ta haye wuyan Baffa tana fadin, "Baffan Goggo ka yi min doki irin wanda Baba na yake mana".
Kulsum ta mako ta a fusace tana fadin, "Sai kin karya min Baffa na?
Ki je Baban naki ya yi miki amma wannan Kakana ne".
Iftihal ta bare bakin shagwabar ta tana kuka, Baffa ya jawo ta jikin sa yana rarrashin ta.
"Kyale Mama, ni ma ba Baban ta ba ne, Baban ta yana 'Yalleman".
Goggo kuwa ta hau yi wa Kulsumu fadan saurin duka irin nata, fada ta ke,
"Ke wa ya doke ki?
Akwai wanda ya kai ki hawa jikin mutane?"
Kulsum murmushi ta ke tana zubo wa Baffa dafuwar hanta da ganyen alayyahu da ta kawo masa a faranti ta mika masa, ta zuba wa Goggo tana fadin, "Ku ci sosai ku murmure, umarah za ku koma sati mai zuwa, a can za ku yi azumi gabadaya".
Baffa sai ya kasa cin abincin don farin ciki, a rayuwar sa ba abinda ya ke so irin zuwa Makkah, ya dinga sanyawa Kulsum albarka, ba ya taba gajiya da ganin sa gaban dakin Ka'abah mai alfarma.
Washegari kuma 'Yalleman suka tafi, boot din motar su shake da buhunhunan kayan abinci da kayan masarufi.
Direban Turaki ne ke jan su kasancewar Turaki ba ya gari, ya je wani aiki a AKTH.
Malam Hadi ya tarbi 'yan jikokin sa cike da farin cikin ganin su, Lami sai hidima ta ke da su don yanzu tsakanin ta da Kulsum biyayya ce irin ta ubangida da yaron sa, ta yarda Allah ya gama daukakata a kan 'ya'yan ta, kuma ita ce marufar asirin su.
Ta gaya wa Malam Hadi sakon Turaki cewa, su samu wani gidan aro su koma sati mai zuwa za a zo a rushe gidan a yi musu ginin zamani.
Malam Hadi ya ce, "Kulsumu kina dora wa mijin ki hidimar mu, wadda na tabbatar ta fi karfin aljihun sa, a kan me?
Gini fa Kulsumu!
Ni ai gidan nan ya ishe ni a hakan da yake in ganganda in karashe
yar ragowar rayuwa ta, hidimar da ku ke mana kuwa Allah ne zai saka muku.
Addu'o'in mu gare ku ba za su taba yankewa ba".
Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Baba, duk abin da ka ji ya ce zai yi, to zai iya ne.
Burin mu shi ne ku kasance cikin farin ciki ku yi ta sanya mana albarka".
Lokacin da suka dawo Gaya yamma ta yi sosai.
Tun a harabar gidan ta ga motar Turaki a ma'adanar adana motocin sa, tabbacin ya dawo kenan daga Kano.
Wani sanyi ya ratsa zuciyar ta.
Kwanaki biyun da ba su sanya juna a idanun su ba, tamkar shekaru biyu suke ganin su.
Batulu da Iftihal suka bude motar suka fice da gudu suna fadin.
"Our Daddy is back..." (Baban mu ya dawo).
A falon suka tadda shi, yana tsaye yana waya sanye cikin kaftan na danyar farar shadda ga sajen nan nasa ya kwanta luf a saman fuskar sa ma'abociyar zati da kamala.
"Kullum girma ya ke, shekarun sa turawa suke, amma kamar kullum kara masa kuruciya ake!"
Kulsum ta fada a zuciyar ta.
Ya suri yaran su duka biyu a hannayen sa hagu da dama yana fadin, "Ina Mummy ta kwashe min ku ta kai ku na dawo babu kowa a gidan?"
Batulu sarkin magana ta ce, "Ai 'Yalleman muka je, Grandpa yana gaishe ka".
Dariya ya yi ya ce, "To in ce kun kawo min tsarabar 'Yalleman?"
Iftihal ta mika masa katuwar gorubar da ke dunkule a hannun ta.
Ya sumbaci goshin yarinyar ya ce, "Dadi na da Ifty babu rowa, Batulu ke ina taki?"
Ta shagwabe fuska ta ce, "Daddy na cinye, na yada kwallon".
Ita ma ya sumbace ta a kumatu ya ce yana kokarin sauke su kasa, "Maza ku je Baba Laraba ta yi muku wanka ku huta, a bar ni in gaisa da Mummy sosai".
"I missed you Prince...".
Ta fada tana sakalo hannayen ta ta saman wuyan sa.
Kallon ta yake kamar yau ya soma ganin ta.
Kullum Kulsum (sweet 16) ta ke kara komawa a idanun sa.
Kulsumun da ta dusar da hasken sauran mata daga idanun sa, ta cike masa gurbin da mata hudu da kwarkwarori goma, ba za su iya cike masa ba.
Kulsumun da ta dauke kuruciyar sa ta ci gaba da gwagwarmaya da shi a shekarun girman sa.
Kulsumun da ba zai iya hadawa da kowacce mace ya yi adalci ba...
Kulsumun da yake fata har a aljanna Allah ya tashe su tare, matsayin shugabar duka hurul-eenin'sa!.
Daukanta ya yi gabadaya yana tafiya da ita a hannunsa zuwa katafaren dakin barcin su.
A lokaci guda yana gaya mata kalaman da suka fi karfin biro na ya rubuta.
Wannan shi ne labarin KULSUM,....UMMUKULSUM ABDULHADI 'YALLEMAN.
Karshensa kenan ba shi da littafi na hudu.
Masha Allah laquwwata illa billah!!!
Kuskuren da ke ciki, ku taya ni rokon Allah ya yafe min.
Alkhairin da ke ciki, Allah ya raba mana ladan ni da ku bakidaya.
Sai mun hadu a sabon littafina.
YI WA KAI HISABI!!!
Tuna sunan;
YI WA KAI HISABI!!!
YI WA KAI HISABI!!!
Shima zai zo muku complete insha Allah nan ba da jimawa ba.
And I promised you a thrilled reading !
SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI ke cewa.
"Da fatan watarana Allah ya hada mu cikin ALHERInSa, amin".
Ga masu bukatar tsofaffin littatafaina softcopies ko hardcopies ku tuntubeni a 07030137870 (whtsp only).
SHAPE \* MERGEFORMAT
KULSUM-3 TAKORI
SHAPE \* MERGEFORMAT
PAGE \* MERGEFORMAT
Calibri
Calibri
SimSun
Times New Roman
Time
New Roman
Berlin Sans FB
Berlin Sans FB
Cambria
Cambria
Roboto Light
Times New Roman
Cutive Mono
Times New Roman
Noto Sans Bengali
Times New Roman
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
_GoBack
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
nass
Normal.dotm
TECNO LD7
WPS Office
16.000
6ec37066058b43d4a800ec9ff269ffbf