← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu dare ya yi
zuciyarsa kuwa ya fadi hakan ne gudun rigimar Kulsumu kada ta ruguje wannan maganar, amma kwarai zai so ya sake ganin ta.

Bayan ganin da ya yi mata a Lagos, wanda ya hana shi ko da runtsawa tsayin kwanaki biyun nan gabadaya.

A hankali yake tukin motar hawaye na sauka a kan kundukukin sa.

Hawayen farin ciki irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.

Kai tsaye cikin gida ya wuce da sassarfa, bangaren Umma ya nufa.

Har dakin barcin ta ya duba ba ta nan, sai ga Laraba za ta gifta ya tambaye ta Umma, ta ce tana turakar Maimartaba, ita ce mai girki.

Bai tsaya ya gama jin me ta ke cewa ba ya wuce bangaren mahaifin nasa.

Sallama ya yi cikin kokarin daidaita nutsuwar sa, duk suka amsa mishi, Umma na serving Maimartaba abinci.

Murmushi ya yi lokacin da Turaki ya gurfana a gaban sa yana gaisuwa.

Ya amsa, sannan ya ce,
Yanzu da ma na ce Umman ka ta kira min kai a waya, kwana biyu idanun nan nawa sun matsa min da kaikayi, ga wani hawaye da ke yawan fitowa
Turaki ya yi kasa da kansa, ya ce,
Allah ya kara ma yawan rai, zan kawo maganin da za a dinga digawa
.

Sannan ba tare da ya jira amsar Maimartaba ba ya dora abin da ke cin sa a zucci.

Baffan Kulsumu ne ya aiko ni Allah ya kara maka lafiya, ya ce, in har yanzu ina son komen Kulsumu in aika sadaki gobe a mayar da auren ta da zaa daura a kaina
Umma ta saki cokalin da ke hannun ta, ta ce,
Kai Turaki bana son hauka, ko dai soyayya ta sa ka fara kuncewa ne?

Ya ya za su daura wa
yar su aure da dan uwanta ka ce wai wani an ce da kai za a daura?

Murmushi ya yi, ya ce,
Wallahi Umma babu shirme cikin magana ta, na je ne in gaishe su kamar yadda na saba, sai yake cewa an samu matsala da wancan an fasa, in zo a daura da ni
Maimartaba ya ce,
to ban da abinki rabon kwado yana hawa sama ne?

Umma ta yi hamdala a fili, ta ce,
Ina ruwan Allah, abinda nake gaya maka kullum ke nan Turaki, cewa ka fauwala wa Allah komai, idan da rabon sauran zama a tsakanin ku Allah zai ba ka wannan damar
.

Sai ga hawaye a idon ta.

Ta kai hannu ta goge ta sake cewa,
Allah na gode maKa da Ka nufi Kulsumu da dawowa gare mu
Maimartaba kuwa cewa ya yi, ya kirawo masa Galadima a waya.

Nan da nan ya kira ya hada su.

Yana ji Maimartaba na bada umarnin a hada dukiyar aure da sadaki na alfarma su je shi da Chiroma su karba wa Turaki auren matar sa ta baya.

Tuni Umma ta fice zuwa dakin ta.

Batulu ta fara kira, sannan Yaya Hadiza da Ramla ta ce, su yi kokari dukkan su su zo gobe, amma ba ta gaya musu makasudin kiran nasu ba.

Nan kuma ta hada barorin ta da masu girkin bangaren ta ta soma bada umarnin girke-girken da za a yi gobe, da abubuwan da ta ke so a tanada, Laraba kawai ta gaya wa ko me ke nan, sai ga tsohuwar tana rawa tana juyawa.

A waya Baffa ya kira Daddyn Taufeeq wanda ke cikin Kano tare da Taufeeq din, ya gaya masa hukuncin da ya yanke na maida Kulsumu ga mijinta don ba zai iya kyale ta ta sake kwana a gabansa babu aure ba.

Duk da Daddy ya ji ba dadi, don shi ya yi hukuncin ne don in an kwana biyu Taufeeq ya sake nutsuwa a dawo da maganar auren.

Amma sai ya kasa fadin kudurin zuciyar tasa kada Baffa ya ga ya yi son kai, ya bi bayan nasa.

Ya sa albarka tare da cewa, insha Allahu da su za a daura auren Kulsumu gobe kafin su wuce.

Bai gaya wa Taufeeq ba, don a lokacin ma yana gaban sa yana masa magiya da hawaye, da zai amsa wayar Baffa sai ya kauce daga gaban sa don bai san me wayar karfe goma na dare ta kunsa ba.

Karfe goma sha dayan dare Galadiman Gaya kanin Maimartaba da Chiroma da limamin masallacin fadar Maimartaba Sarkin Gaya suka iso gidan Malam Jibo.

Babu wanda za su aika don haka Chiroma ne ya yi sallama da kansa.

Baffa da ke yi wa Goggo da Hajiya bayanin hukuncin da ya yanke a lokacin, ya fito don ganin masu sallama.

Nan ya ga manyan bakin dake tafe cikin dare daga fadar maimartaba Sarki.

Komawa ya yi ya sanar da su Goggo suka koma dakin Goggo ita da Hajiya Nasara, suna ta kakabin al
amarin a zukatan su.

Hajiya Nasara ba ta yi mamaki can-can ba, don ta san su Baffa har gobe suna son Turaki.

Baffa ya shigo da bakin sa har dakinsa, nan aka yi magana ta gemu-da-gemu.

Ya ce, sadakin da suka kawo ya yi yawa, don Kulsumu ba yau za ta fara zuwa gidan su ba, Galadima ya ce ai ba su da hurumin maida ko sisi ga maimartaba.

Nan aka sa lokacin daurin aure karfe goma sha daya na safe.

Kuma a daren ranar duk wanda ya kamata ya san zancen auren Turaki a masarautar Gaya sai da ya sani.

Mata ne kawai ba su da labari, su ma zuwa wayewar gari duk Laraba ta gama fesawa kowa labarin dawowar uwardakin ta UmmuKulsumu.

Nan aka fara hidimar girki wanda za a raba wa jama
a bayan daurin aure.

Daga nan kuma mata za su zarce da biki ne.

Kulsumu na kwance uwardakin Goggo a daren ranar, ba ta san wainar da ake toyawa ba.

Haka kawai ta ke fama da guilty conscience?

Ta ke tuhumar kanta, anya hukuncin da ta yanke a kan Taufeeq ta yi daidai?

Me ya sa ba ta yi hakuri ta aure shi haka ba?

Ko don albarkacin iyayensa da
yan uwan sa, ta san son da Taufeeq ke mata idan ta ce ya bar abu komai tsaurin sa za bari, in har za ta yi farin ciki.

Yanzu ga shi ta jefa iyayen sa cikin damuwa, ta hada su da dan su, anya hukuncin ta bai yi tsauri ba, kuma bai yi kama da butulci ba?

Da wannan guilty conscience din ta kwana, tana jin kamar ta je ta samu Baffa ta gaya masa ta janye hukuncinta.

Amma lokacin karfe biyu ne na dare, Hajiya na falon Goggo tana sallah, ta san shiriya ta ke roka wa Taufeeq a wurin Ubangiji.

Ta san halin Hajiya Nasara, duk wata matsala idan ta tunkaro ta, to ta daina barci ke nan har sai ta ga karshen ta da karfin addu
a.

Ta kara jin nadama ta lullube ta, ta sa a ranta gobe in Allah ya tashe su lafiya the first thing in the morning (abu na farko da zata yi da safe) shi ne gaya wa Baffa, Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, za ta auri dan uwanta Taufeeq cikin kowanne hali, ta taimaka masa ya yi yaki da kowanne irin sabon Allah.

Da safe bayan sun idar da sallar asubahi duk su ukun ba ta tashi a wajen ba sai da ta bude baki ta gaya wa Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, a ci gaba da shirin daurin aure.

Ba su ce mata komai ba sai ido da suka bi ta da shi suna tunanin ko dai ta samu depression ne?

Baffa na shigowa daga masallaci, shi ma ta je ta gaya masa.

Murmushi ya yi ya janyo wata jaka ya tura mata gaban ta.

Dauki wannan, sadakin ki ne.

Amma ba da Taufeeq ba, da wanda Allah ya tsaga da rabon sa
Kulsumu ta bi Baffa da kallo kamar za ta yi kuka.

Baffa, sadakata ka bayar?

Wani murmushin ya sake yi, ya ce,
Wace irin sadaka bayan ga sadaki irin wanda duk garin nan babu
yar wanda ta taba samun rabin sa?

Ni ba sadakar ki na bayar ba, aure ne na na-gani-ina-so.

Ba ki kara kwana daya gaba na sai da igiyar aure a kanki, domin kin gama zaman Abuja
Hankali tashe Kulsumu ta bar gaban Baffa ta koma daki ta soma rusa kuka.

Daga Goggo har Hajiya babu wanda ya rarrashe ta.

Gari na wayewa suka shiga hidimar da ke gaban su kada jama
ar da suka gayyata su fara isowa ba su shirya komai ba.

Karfe goma sha daya na safe, dumbin jama
ar garin Gaya da wajenta suka sake shaida daurin auren UMMUKULSUM ABDULHADI
YALLEMAN da YARIMA ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI a kan sadaki lakadan ba ajalan ba.

Yan
Yalleman sai ana gab da daurin aure suka iso.

Daga nan ne kowanne bangare (gidan su amarya da gidan su ango) ya zarce da wunin biki.

Turaki dai ko ganin sa ba a yi saboda yawan jama
a, kai ka ce an yi sati guda ana gayyatar su.

Kodayake su su Goggo sun yi gayyatar haka duk wadanda su Hajiya Nasara suka gayyato daga Abuja domin halartar auren dan su, sune suka halarci daurin auren Kulsumu da Turaki a karo na biyu.

Cikin mahalarta daurin auren har da TAUFEEQ MUHAMMAD BELLO (tears).

Boye kansa ya yi bayan daurin aure a cikin sassan shi da ke cikin gidan, ya gabatar da alwala ya sallaci walha (dhuha), sannan ya dora da sallar nafila raka
a biyu ya yi godiya ga Allah da Ya cika masa buri na karshe a rayuwar sa.

Duk wasu burikansa Ubangiji ya cika masa su daya bayan daya, wanda yake gani a matsayin mafi wahala (wato samun Kulsumu), yau ga shi Ubangiji ya cika mishi ba tare da kokari, dabara ko iyawar sa ba.

Lallai ne shi Allah fa
alun lima yuridu ne (wato mai aikata abin da ya so) a kuma lokacin da Ya ga dama.

Wayar sa ya lalubo daga cajin da ya sanyata tun jiya, mutum na farko da ya kira shi ne, Dr.

Abdul
Ahad Aminu Maikano, ya ce,
"Aboki, kana ina?

Ya ce,
Ina Manchester, amma gobe insha Allah zan koma Reading
Ya ce,
To kunnen ka nawa?
Chapter 6 · 0% Book details